Wednesday, December 24
Shadow
Kalli Bidiyon yanda manomi ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta a jihar Kebbi

Kalli Bidiyon yanda manomi ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta a jihar Kebbi

Duk Labarai
Wani manomi a jihar Kebbi me suna Kabiru Kamba ya ce ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta amma bata mutu ba a gona. An binne jaririyar a gonarsa dake Kamba karamar hukumar Dandi dake jihar. Ya bayyana hakane ga tawagar hukumar yaki da cin zarafi ta jihar da ta kai masa ziyara gida. Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito cewa, tsohuwar babbar sakatariya a jihar, Hajiya Rafa’atu Hammani.ce ta jagoranci tawagar zuwa gidan Kabiru. Yace a ranar da lamarin ya faru ya je gona sai yaga kunya wadda bai san da ita ba kuma ta yi sama sosai Yace anan ya kira mutane suka tayashi suna tonawa sai suka ga jaririya. Yace sun sanar da 'yansandan kusa da gurin inda yace kuma ya dauki yarinyar zai rike kuma an yi sa'a ma matarsa ta haihu dan haka ba za'a sam...
An Samu Mace Ta Farko Da Ta Kai Matakin Farfesa A Bangaren Haɗa Magunguna A Arewacin Nijeriya

An Samu Mace Ta Farko Da Ta Kai Matakin Farfesa A Bangaren Haɗa Magunguna A Arewacin Nijeriya

Duk Labarai
An Samu Mace Ta Farko Da Ta Kai Matakin Farfesa A Bangaren Haɗa Magunguna A Arewacin Nijeriya. Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria Ta Ɗaga Likkafar Hajia Hadiza Usman Ma'aji Zuwa Matsayin Farfesa Akan Haɗa Magunguna Na Clinical Pharmacy, Wadda Ita Ce Mace Ta Farko A Arewacin Najeriya Da Ta Kai Wannan Matakin. Wace Irin Fata Za Ku Yi Mata? Daga Jamilu Dabawa
WATA SABUWA: Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah

WATA SABUWA: Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah

Duk Labarai
Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah. Cikakken rahoto na nan tafeA Dimokuraɗiyya
Peter Obi: Sau daya kacal zan yi mulki idan aka zabeni shugaban kasa>>Peter Obi

Peter Obi: Sau daya kacal zan yi mulki idan aka zabeni shugaban kasa>>Peter Obi

Duk Labarai
Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ya shirya yin wa’adin shekara huɗu kacal idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027. Obi, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir el-Rufai, na shirya kafa kawance domin ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027. Da yake magana a wata tattaunawa ta “Twitter Space” da Parallel Facts suka shirya a ranar Lahadi, Obi ya ce duk wani ɗan takara daga kudancin Najeriya da aka zaɓa shugaban ƙasa a 2027 dole ya kasance cikin shiri ya sauka daga mulki ranar 28 ga Mayu, 2031, bisa abin da ya kira “yarjejeniya marar rubutu” da kuma tsarin rabon mulki. Ya ƙara da cewa tsarin rab...
Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka tarwatsa taron jam’iyyar PDP a Abuja duk da musanta rufe ofishin jam’iyyar da suka yi

Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka tarwatsa taron jam’iyyar PDP a Abuja duk da musanta rufe ofishin jam’iyyar da suka yi

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana wanda ya nuna 'yansanda a wajan taron jam'iyyar PDP inda rahotanni suka ce sun tursasawa 'yan jam'iyyar ficewa daga taron. https://twitter.com/thecableng/status/1939708148878884974?t=GCP_zgMmmcYiHVEPqmoTtA&s=19 A baya dai hukumar 'yansandan ta musanta cewa, ta kulle ofishin jam'iyyar PDP din.
Allah Sarki Kalli Bidiyon yanda aka cire hoton Ganduje daga ofishin APC ana maye da hoton sabon shugaban jam’iyyar

Allah Sarki Kalli Bidiyon yanda aka cire hoton Ganduje daga ofishin APC ana maye da hoton sabon shugaban jam’iyyar

Duk Labarai
A yayin da aka nada shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC bayan saukar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi. An ga Bidiyon yanda aka cire hoton Ganduje daga ofishin shugaban jam'iyyar aka mayeshi da na sabon shugaban jam'iyyar. https://twitter.com/INYAMURI/status/1939643637438267642?t=Pr0LkVz9nZOIaHCfud-I6A&s=19 Duniya kenan kowa da zamaninsa.
Kadaici na kai mutane 871,000 zuwa lahira duk shekara>>WHO

Kadaici na kai mutane 871,000 zuwa lahira duk shekara>>WHO

Duk Labarai
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO tace kadaici na kashe mutane 871,000 duk shekara. Rahoton yace a duk cikin mutane 6 na Duniya akwai mutum daya dake fama da kadaici wanda hakan ke haifar da cutuka kala-kala. Masanan sun ce, kadaici na kara hadarin kamuwa da shanyewar rabin jiki, da ciwon zuciya, da ciwon sugar da damuwa da kisan kai. Masana sun ce wayar hannu ta taimaka wajan saka mutane cikin kadaici inda ake samun karuwar masu kadaicewa da rashin son shiga mutane.
PDP na gudanar da manyan taruka biyu da nufin samo hanyar gudanar da taronta na NEC

PDP na gudanar da manyan taruka biyu da nufin samo hanyar gudanar da taronta na NEC

Duk Labarai
Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Najeriya na ci gaba da tattanawa wajen gani sun shawo kan ɓarakar da ta kunno kai a tsakaninsu da ya janyo tsaiko, wajen gudanar da taron majalisar zartawa na jam'iyyar da aka shirya gudanarwa a yau Litinin. Tun da safiyar yau ne dai aka ga jami'an 'yansanda da na tsaron fararen hula na Civil Defense suka yi wa ofishin jam'iyyar na Wadata Plaza, Abuja tsinke tare da hana dukkanin manyan jami'an jami'yyar shiga. Yanzu haka dai kwamitin amintanntu na jam'iyar na gudanar da wani taron sirri a babban ɗakin taro na Ƴar'adu Center da ke Abuja. Taron nasu na zuwa a daidai lokacin da gwamnonin jam'iyyar da ƴan majalisar dattawa da na wakilai da ke gudanar da wani taron a gidan gwamnatin jihar Bauchi da ke unguwar Asoko...