Saturday, December 13
Shadow
Mutum ko wani shugaba ba zai iya gyaran Najeriya ba, dan haka mu ci gaba da addu’a kawai>>Inji Fasto Wale Oke

Mutum ko wani shugaba ba zai iya gyaran Najeriya ba, dan haka mu ci gaba da addu’a kawai>>Inji Fasto Wale Oke

Duk Labarai
Fasto Wale Oke na cocin Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN ya bayyana cewa matsalolin Najeriya sun fi karfin mutum ya gyarasu. Yace dan hakane ma su ka yanke hukuncin ci gaba da yiwa Najeriya addu'a inda yace zasu ci gaba da azumi da addu'a kan Allah ya gyara Najeriya. Yace kuma ya gayawa mutanensu cewa su shiga siyasa kada su yi baya-baya, su shiga a dama dasu. Ba wai maganar karbar katin zabeba, su tsaya takara suma a zabesu.
Jihar Jigawa ta dakatar da Albashin malaman makarantar Firamare 239 da aka samu basa zuwa aiki, ciki hadda wanda ya shekara 3 bai je wajan aikin ba

Jihar Jigawa ta dakatar da Albashin malaman makarantar Firamare 239 da aka samu basa zuwa aiki, ciki hadda wanda ya shekara 3 bai je wajan aikin ba

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa, Hukumar Ilimin bai daya UBE ta jihar ta dakate da albashin malaman makarantar Firamae 239 da aka samu da laifin rashin shiga aiki su koyar da dalibai ko rashin zuwa wajan aiki. Shugaban hukumar, Prof. Haruna Musa ya bayyana cewa wannan kokari ne na tsaftace aikin gwamnati. Sannan yayi kira ga al'umma da su rika lura su kai karar wadanda basa zuwa wajan aikin. Daga cikin wadanda aka dakatar da albashin nasu akwai malamin da ya shekara 3 kanan bai je wajan aikin ba
Kamfanin DSTV da sauran tashoshi na Tauraron dan Adam sun tafka asarar Dala Miliyan $158.19 saboda ‘yan Najeriya da yawa yanzu sun daina saka kati saboda matsin tattalin arziki

Kamfanin DSTV da sauran tashoshi na Tauraron dan Adam sun tafka asarar Dala Miliyan $158.19 saboda ‘yan Najeriya da yawa yanzu sun daina saka kati saboda matsin tattalin arziki

Duk Labarai
Rahotanni sun ce Kamfanin Multichoice wanda su DSTV suke karkashin sa sun tafka mummunar asara saboda 'yan Najeriya da yawa sun daina saka kati suna kallon tashoshin. Kudin shigar kamfanin a shekarar data gabata yayi kasa da kaso 44 cikin 100 inda a yanzu suka samu kudin shiga da ya kai dala Miliyan $197.74. Saidai a shekarun baya suna samun kudin shiga da ya kai dala Miliyan $355.93. Hakan na nufin sun tafka asarar dala Miliyan $158.19 idan aka kwatanta da shekarar data gabata. Lamarin dai bai zowa mutane da mamaki ba musamman ganin yanda kasar ke cikin hali na matsin tattalin arziki. Hakan kuma baya rasa nasaba da karin kudin subscription da DSTV din suka yi daga Naira N29,500 zuwa Naira 37,000 duk wata.
Ina Goyon bayan Tinubu ya zarce a 2027 ido rufe, saboda babu shugaban da ya taba yin abinda yayi>>Inji Gwamnan Jihar Gobe, Inuwa Yahya

Ina Goyon bayan Tinubu ya zarce a 2027 ido rufe, saboda babu shugaban da ya taba yin abinda yayi>>Inji Gwamnan Jihar Gobe, Inuwa Yahya

Duk Labarai
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya yace zai yi aiki tukuru dan goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce a shekarar 2027. Gwamnan ya bayyana hakane a yayin kaddamar da wani shirin noma da kiwo a jiharsa. Gwamnan yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya warew shirin Naira Biliyan 120 dan karfafa kiwo kuma ya amince a bayar da kaso 50 cikin 100 na kudin. Yace babu shugaban Arewa da aka yi a baya da ya taba warewa bangaren kiwo irin wadannan makuda kudade duk da cewa yankin Arewa an sanshi da kiwo. Yace bisa haka suna goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce. Yace zasu goyi bayanshi ido Rufe dan ya sake zama shugaban kasa a 2027. “I assure the President that for what he has done, is doing, and will do, Gombe people will follow him to the battlefield bl...
Bidiyo: Wai Gfresh yaushe zaka yi hankali ne, wa ya ce maka Adam A. Zango baya son Ana zuwa Dubashi>>Murja Kunya

Bidiyo: Wai Gfresh yaushe zaka yi hankali ne, wa ya ce maka Adam A. Zango baya son Ana zuwa Dubashi>>Murja Kunya

G-Fresh Al'amin, Jaruman Tiktok
Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g Tauraruwar Tiktok Murja Kunya ta bayyana cewa, bata yadda da matsayar jarumin Tiktok, Gfresh ba kan cewa mutanen dake zuwa duba Adam A. Zango sun yi yawa ba. Gfresh ya yi Bidiyo inda yake kiran mutane su rage tururuwr da suke ta zuwa duba Adam A. Zango. Saidai Murja tace Adam A. Zango na mutanene dan haka wannan shawara ta Gfresh bata karbu ba. https://www.tiktok.com/@murjess1/video/7515950812531657991?_t=ZM-8xDePcFp5YG&_r=1 Adam A. Zango dai yayi hadari a hanyar Kaduna zuwa Kano a yayin da yake kan hanyar zuwa bikin Sallah. Kuma mutane da yawa ne ke ta tururuwa suna zuwa dubashi.
Manyan Ma’aikatan mu ne ke ta tafiya lahira akai-akai babu kakkautawa shiyasa muka ce a yi Azumi ko zamu samu sauki>>Ma’aikatar Noman Najeriya

Manyan Ma’aikatan mu ne ke ta tafiya lahira akai-akai babu kakkautawa shiyasa muka ce a yi Azumi ko zamu samu sauki>>Ma’aikatar Noman Najeriya

Duk Labarai
Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g Ma'aikatar noma ta Najeriya ta bayyana cewa manyan ma'aikatan hukumar ne ke ta mutuwa shiyasa ma'aikatar ta fito da tsarin yin Azumin dan neman taimakon Allah. Hakan na zuwane bayan da aka samu rahotanni dake cewa, ma'aikatar ta nemi ma'aikatan ta da su dauki azumi dan neman nasarar wadatar Abinci a Najeriya. Saidai a sanarwar da mataimakiyar me yada labarai ta hukumar, Ezeaja Ikemefuna ta fitar tace zancen ba haka yake ba. Tace manyan ma'aikatan hukumar ne ke ta mutuwa akai-akai shiyasa suka fito da tsarin yin addu'a ta hanyar Azumi dan neman sauki da daukin Allah. Saidai Tuni an dakatar da yin azumin wanda da za'a fara ranar Litinin bayan da cece-kuce yayi yawa akan Lamarin...
Bankin Duniya ya bayar da tallafin Dala Miliyan $40 a rabawa talakawan Najeriya

Bankin Duniya ya bayar da tallafin Dala Miliyan $40 a rabawa talakawan Najeriya

Duk Labarai
Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g Bankin Duniya ya ware dala Miliyan $40 dan tallafi ga talakawa mafiya rauni a Najeriya. Tun a watan Satumba na shekarar data gabata ne dai Bankin ya amince da bayar da wadannan kudade a matsayin bashi amma sai yanzu za'a bayar dasu. Tallafin za'a bayar dashi ne da karfafa 'yan Najeriya da yawa kuma zai ci gaba har nan da zuwa shekara 2029
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta tabbatar da kama wani ɗan kasar China bisa zargin taimaka wa ƴan ta’adda

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta tabbatar da kama wani ɗan kasar China bisa zargin taimaka wa ƴan ta’adda

Duk Labarai
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta tabbatar da kama wani ɗan kasar China bisa zargin taimaka wa ƴan ta’adda. Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta tabbatar da kama wani ɗan ƙasar China yayin wani samamen yaƙi da ta’addanci da aka gudanar a Jihar Borno. Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo- Markus Kangye, ne ya tabbatar da hakan a madaJanardin manyan hafsoshin soji a ranar Juma’a. Sai dai Manjo-Janar Kangye bai bayyana sunan baƙon ba, amma ya ce mutumin da ya bayyana kansa a matsayin mai hakar ma’adanai yana hannun dakarun soji yanzu kuma ana ci gaba da bincikarsa. Kama ɗan ƙasar China ɗin ya faru ne kasa da mako guda bayan rundunar soji ta bayyana kama wasu 'yan Pakistan huɗu da ake zargin suna koyar da 'yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas. Yayin da ake tambayarsa ...