Tuesday, December 16
Shadow
INNA LILAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Abokiñ Wasañ Kwallonsà Ya Càķa Màsà Aĺmàkàshì Ya Rasu A Kano

INNA LILAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Abokiñ Wasañ Kwallonsà Ya Càķa Màsà Aĺmàkàshì Ya Rasu A Kano

Duk Labarai
Wani mummùñan lamari ya faru a filin wasan kwallo na Shagari Quarters dake cikin garin Kano, inda wasu bata-gari suka kàśhe wani matashi mai suna Baba, ɗan asalin Jos, a cikin filin wasa. Yadda lamarin ya auku shine, wanda aka kaśhe, Baba, yana cikin wasa ne lokacin da ya ci kwallo, sai jikinsa ya bige wani yaro da ake kira Bello (Belloty). Alkalin wasa bai busa ketar ba, wanda hakan bai yi wa Belloty dadi ba. Bayan an kammala wasan, Belloty ya bi Baba da zargin me ya sa ya bige shi, hatsaniya ta barke tsakaninsu. Abokin Belloty, wanda ake kira Hafizu (wanda aka fi sani da “Mata”), ya miƙa masa almàķashi, inda Belloty ya caka wa Baba cìkin źùçiya, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa a nan take. Belloty (wanda ya caka almakashi) da Hafizu “Mata” (wanda ya mika almakashiñ) dukkan...
Majalisar Dinkin Duniya tace za’a yi yunwa me tsanani a Arewacin Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya tace za’a yi yunwa me tsanani a Arewacin Najeriya

Duk Labarai
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoto kan kasashen dake fuakantar ibtila'in yunwa su 13. Rahoton yace kasashen Gaza, Sudan, South Sudan, Haiti,da Mali na fuskantar yunwa nan take idan ba an kai musu dauki ba. Rahoton yace rashin tsaro, Rashin tabbas na tattalin arziki da canjij yanayi ne ya kawo lamarin yunwar. Rahotanni ya bayyana matsalar tsaro a Arewacin Najeriya wanda yace zai iya kara kazancewa. Rahoton yace matsalar tsaron Arewar zai kara jefa mutane cikin yunwa saboda za'a raba mutane da yawa da muhallinsu.
Baban mu ne kuma shugaba na gari>>Mansurah Isah ma tace tana tare da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Baban mu ne kuma shugaba na gari>>Mansurah Isah ma tace tana tare da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Duk Labarai
A yayin da dambarwa da rade-radi suka kunno kai cewa, za'a iya canja mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima kamin zaben 2027. 'Yan Fim sai fitowa suke suna nuna suna goyon bayan Kashim Shettima. Rahama Sadau ta fara fitowa ta nuna goyon baya ga kashim daganan kuma sai Shamsu Dan iya. A yanzu kuma Mansurah Isah itama ta fito ta nuna tana tare da Kashim Shettima. Mansurah Isah ta wallafa hoton kashim inda ta kirashi uba kuma shugaba na gari.
Kalli Bidiyo: Mustapha Salihu yayi bayanin dadalilin da yasa bai kira sunan Kashim Shettima ba

Kalli Bidiyo: Mustapha Salihu yayi bayanin dadalilin da yasa bai kira sunan Kashim Shettima ba

Duk Labarai
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC shiyyar Arewa maso gabas, Mustapha Salihu yayi karin haske kan rashin kiran sunan Shettima da yayi a wajan taron jam'iyyar APC na masu ruwa da tsaki daga yankin Arewa maso gabas. Lamarin dai ya jawo hatsaniya sosai. A hirarsa da Channels TV, Mustapha Salihu yace kamin ya bayyana Tinubu a matsayin zabinsu na dan takarar APC a 2027, dai da ya gama yabon Kashim Shettima. Yace Kuma a dokar jam'iyya Shugaban kasa kadai yake yin zaben fidda gwani ba tare da mataimaki ba, sai idan an kammala zabene sai ya dauko wanda yake so ya mai mataimaki. https://twitter.com/channelstv/status/1934690994139591081?t=XDjrbwb3Vn5SVTYWSwAhGg&s=19 Cikin wadanda basu ji dadin wannan abu ba, hadda Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum.
Da Duminsa:Aljanu sun je Asibiti Duba Adam A. Zango bayan da yayi Hadari

Da Duminsa:Aljanu sun je Asibiti Duba Adam A. Zango bayan da yayi Hadari

Duk Labarai
Sunce ta karewa Adam A Zango baya da kowa sai gashi har aljanu ke cika mana asibiti wajen dubiyar ganinsa saboda yawan jama'a ko aljanun sai sunyi kwana biyu suke samun damar ganinsa, komai zamanka celebrity a Kannywood sai kayi hakurin bata lokaci a waje kafin ka samu shiga dubiyar Adamu Zango a dakinsa, idan baka yi hakurin ba saidai ka fita Bantaba ganin celebrity a wannan yankin namu wanda yake da masoyan gaskiya ( Fan) ba irin Adamu Zango, masoyansa ba wanda ya siya da kudi ko karya ko da yarjejeniya sai don kauna da soyayyar gaskiya a tsakaninsa da masoyansa Adamu Zango bawan Allah, muna rokon Allah ya kara baka lafiya Boss. Daga Saifullahi Safzor
Kungiyar Direbobin Tanka ta koka da shirin Dangote na fara jigilar man fetur dinsa inda tace zai sa su rasa aiki

Kungiyar Direbobin Tanka ta koka da shirin Dangote na fara jigilar man fetur dinsa inda tace zai sa su rasa aiki

Duk Labarai
'Yan kasuwar man fetur da yawa na ganawa bisa yunkurin Matatar Dangote na fara rarraba man fetur dinsa a fadin Najeriya da tankokinsa. A ranar June 15 Matatar Dangote tace tana shirin kawo tankokin dakon man fetur 4000 da zasu fara jigilar man fetur din Dangoten zuwa sassa daban-daban na kasarnan daga ranar 15 ga watan Augusta me zuwa. 'Yan kasuwar sun ce suna tattaunawa kan lamarin dan daukar matakin da ya dace. Sun koka da cewa wannan yunkurin na Dangote zai saka 'yan kasuwa da yawa su karye
Kwanan nan mutane zasu daina yadda da kariyar gwamnati zasu fara tashi tsaye suna kare kansu>>David Mark

Kwanan nan mutane zasu daina yadda da kariyar gwamnati zasu fara tashi tsaye suna kare kansu>>David Mark

Duk Labarai
Tsohon Kakakin majalisar Dattijai, Sanata David Mark ya bayyana cewa, Kwanannan mutane zasu daina yadda da cewa gwamnati zata karesu inda zasu fara tashi tsaye suna kare kansu. Mark ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Paul Mumeh inda yace lamarin tsaro ya kazance. Ya jawo hankalin gwamnati data dauki mataki ko kuma nan gaba kadan mutane zasu fara tashi tsaye suna kare kansu. Ya bayyana hakane a yayin da aka kaiwa jiharsa ta Asali, Benue hari inda aka kashe mutane sama da 100.
Darajar Naira 100 a shekarar da aka baiwa Najeriya ‘yanci watau 1960 a yanzu Naira Miliyan 1.1 ne

Darajar Naira 100 a shekarar da aka baiwa Najeriya ‘yanci watau 1960 a yanzu Naira Miliyan 1.1 ne

Duk Labarai
Kudin Naira kusan za'a iya cewa ya rasa darajarsa baki daya a cikin shekaru 65 da suka gabata. Bincike ya nuna cewa Naira 100 a shekatar da aka baiwa Najeriya 'yanci watau 1960 daidai take da Naira Miliyan 1.1 a yanzu. An alakanta faduwar darajar Nairar da hauhawar farashin kayan masarufi da Karya darajar Nairar da kuma rashin iya gudanar da tattalin arziki. Hakan dai ba karamin ci baya bane ga Najeriya. An samo wadannan bayanai daga World Data ne.
Farashin kayan Masarufi ya sauka a Najeriya>>NBS

Farashin kayan Masarufi ya sauka a Najeriya>>NBS

Duk Labarai
Hukumar kididdi ta Najeriya, NBS tace farashin kayan masarufi ya sauka da kaso 22.97 a watan Mayu idan aka kwatanta da na watan Aprilu da yake kaso 23.71 cikin 100. NBS ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ranar Litinin. Idan aka kwatanta da shekarar data gabata, farashin kayan masarufin na yanzu yana kan kaso 10.98% ne cikin 100 wanda shima za'a iya cewa ya sauka idan aka kwatantashi dana shekarar 2024 wanda yake akan maki (33.95%). Yawanci ana tattara farashin kayan abinci ne dana Haya dana ababen hawa wajan fitar da wadannan alkaluma.