Saturday, December 13
Shadow
Bawai son Tinubu ne yasa ‘yan siyasa ke tururuwar shiga APC ba, Kudin da suka sata na al’umma ne suke neman a yafe musu>>Solomon Dalung

Bawai son Tinubu ne yasa ‘yan siyasa ke tururuwar shiga APC ba, Kudin da suka sata na al’umma ne suke neman a yafe musu>>Solomon Dalung

Duk Labarai
Tsohon Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Solomon Dalung, ya ce ‘yan siyasar da suka fice daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki suna yi ne kawai domin neman a share laifukansu ne na almundahana. Dalung wanda ya bayyana hakan ne a Abuja inda ya nuna rashin gamsuwarsa da cewa ’yan siyasa suna tururuwa zuwa jam’iyyar APC ne saboda ta yi aiki mai kyau, ko dan farin jininta da yi wa talaka aikin da ya dace. Dalung ya ce masu sauya shekar suna la'akari da kalaman tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole da ya ce komai girman zunubansu, za a gafarta musu da zarar sun koma APC, ko da yake Oshiomhole ya musanta wannan magana da aka danganta shi da ita.
Maganar gaskiya Tinubu na ƙoƙari wajen gyaran tattalin arzikin ƙasa kuma ya cancanci a ƙarfafi Gwiwarsa – Fayose

Maganar gaskiya Tinubu na ƙoƙari wajen gyaran tattalin arzikin ƙasa kuma ya cancanci a ƙarfafi Gwiwarsa – Fayose

Duk Labarai
Maganar gaskiya Tinubu na ƙoƙari wajen gyaran tattalin arzikin ƙasa kuma ya cancanci a ƙarfafi Gwiwarsa - Fayose. Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya ce ziyararsa ga Shugaba Bola Tinubu ta kasance ta kashin kai ne domin ƙarfafa masa gwiwa. “Ziyarata na kashin kai ce, domin ƙara ƙarfafa shi ya cigaba da abin da yake yi domin ‘yan Najeriya. Babu wanda ya ce abu ne mai sauƙi, amma babu wani mu’ujiza da zai iya sauya lamura cikin dare ɗaya,” in ji Fayose ga manema labarai a Legas ranar Litinin bayan ganawarsa da shugaban ƙasa. Ya ce Tinubu ya cancanci yabo bisa ƙoƙarinsa har zuwa yanzu. “Amma saboda abinda shugaban ƙasa ya riga ya yi, dole ne mu yaba masa,” in ji shi. Tsohon gwamnan ya ce tarihin sukar da ya yi wa gwamnatoci baya bai hana shi gane irin ƙoƙarin Tin...
In da na ci zaɓe nima sai na cire tallafin man fetur amma ba farar-ɗaya irin na Tinubu ba>>Obi

In da na ci zaɓe nima sai na cire tallafin man fetur amma ba farar-ɗaya irin na Tinubu ba>>Obi

Duk Labarai
In da na ci zaɓe nima sai na cire tallafin man fetur amma ba farar-ɗaya irin na Tinubu ba - Obi Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya ce da ya ci zaɓen da shi ma sai ya cire tallafin man fetur kuma ya kyale Naira ta neman wa kan ta daraja, kamar sai yadda shugaba Bola Tinubu ya yi. Da ya ke magana a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a jiya Litinin, Obi ya ce da zai aiwatar da manufofin a hankali a hankali ba farar-ɗaya ba gaba-gaɗi irin na Tinubu ba. Tsohon gwamnan na Anambra ya ce kowa ya san cewa dole ne a kawo karshen "baƙala da cin hanci da rashawa" da ke tattare da tsarin tallafin man fetur. Obi ya yi tambaya kan inda kudaden da ake tarawa cire daga tallafin man fetur suke tun lokacin da aka cire shi, ya kara d...
Masu zaben Tinubu su je su zabeshi mu dai ba zamu zabeshi ba saboda bai tsinana mana tsiyar komai ba>>Inji Inyamurai

Masu zaben Tinubu su je su zabeshi mu dai ba zamu zabeshi ba saboda bai tsinana mana tsiyar komai ba>>Inji Inyamurai

Duk Labarai
Inyamurai sun bayyana cewa, Ba zasu zabi shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa ba. Sun bayyana cewa saboda shugaban bai yiwa yankunsu na kudu maso Gabas wani abin a zo a gani ba. Dattawan Inyamuran sun ce idan aka tafi a haka Tinubu ko kaso 25 din da ake samu ba zai samu ba a yankin nasu. Jagoran dattawan, Prof. Charles Nwekeaku ne ya bayyana hakan inda yace Tinubu bai yi abinda zasu zabeshi ba. Yana mayar da martanine ga masu cewa, Tinubu yawa yankin nasu abin azo a gani.
Adam A. Zango ya saki Sautin Murya kan halin da yake ciki bayan hàdàrìn mota, Bidiyon ya bayyana inda aka ganshi kwance

Adam A. Zango ya saki Sautin Murya kan halin da yake ciki bayan hàdàrìn mota, Bidiyon ya bayyana inda aka ganshi kwance

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya saki sautin murya da ta yi ta yawo a kafafen sada zumunta inda aka jishi yana cewa jikinshi da sauki. Hakanan an ga Bidiyon Adam A. Zango Kwance a gadon Asibiti, kanshi daure da bandeji kafarsa ma haka. https://www.tiktok.com/@abduljarumi0/video/7514078573133630776?_t=ZM-8x5YKryIpaa&_r=1 Wani rahoto yace Ali Nuhu ne ya dauki nauyin yi masa magani. Da yawan 'yan Kannywood na ta saka sakon jaje a gareshi. https://www.faceb...
Kalli Bidiyo: Dubu dari hudu(400,000) aka sacewa, Adam A. Zango bayan da yayi hadari>>Inji G-Fresh

Kalli Bidiyo: Dubu dari hudu(400,000) aka sacewa, Adam A. Zango bayan da yayi hadari>>Inji G-Fresh

Duk Labarai
Tauraron dan Tiktok, GFresh ya mika sakon jaje ga Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango Wanda yayi hadarin mota. Adam A. Zango yayi hadarin motar ne a yayin da yake kan hanyarsa zuwa wajan wani wasa da aka gayyaceshi, kamar yanda Gfresh ya bayyana. Yace abin takaici shine, wanda suka je kan Adam A. Zango da sunan taimako, sun kwashe masa kudi kusan Naira dubu dari hudu(400,000). Ga jawabinsa kamar haka: https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7513990914524810502?_t=ZM-8x5WcxmyWtc&_r=1 Da yawa dai sun mika sakon Jaje ga Adam A. Zango.
Kalli Bidiyon: Hadarin da Adam A. Zango ya ta’azzara, duk wani me kaunarsa kawai ya sashi a addu’a>>Inji Murja Kunya

Kalli Bidiyon: Hadarin da Adam A. Zango ya ta’azzara, duk wani me kaunarsa kawai ya sashi a addu’a>>Inji Murja Kunya

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Murja Kunya ta bayyana cewa lamarin jikin Adam A. Zango ya ta'azzara. Tace bata san abin yayi muni haka ba. Tace dan haka tana kiran mutane dasu sakashi a addu'a. Ta bayyana hakane a shafinta na Tiktok. https://www.tiktok.com/@murjess1/video/7514043548795194642?_t=ZM-8x5WL9COjtI&_r=1 Rahotanni sun watsu sosai cewa, Adam A. Zango yayi hadari inda har wnda suka je da sunan taimako suka masa sata.
Kalli Bidiyo: Matashi ya yi fatan shi da mahaifiyara su dawwama a wutar Jahannama saboda ta haifoshi yana wahala

Kalli Bidiyo: Matashi ya yi fatan shi da mahaifiyara su dawwama a wutar Jahannama saboda ta haifoshi yana wahala

Duk Labarai
Wani matashi na shan Tofin Allah tsine bayan da yayi wani Bidiyo yana tsinewa mahaifiyarsa inda yace ta haifishi yana shan wahala abinci ma da kyar yake samu. Da yawa sun tsine masa inda suka rika tunawa mutane da su rika yin addu'ar Kwanciya da iyali dan ana tunanin hakan zai sa ba za'a rika haifo irinsa ba. https://www.tiktok.com/@danharuna44/video/7512774919676071173?_t=ZM-8x5VUudR9x0&_r=1 Saidai matashin ya bayyana cewa dan neman suna yayi kuma da talauci, inda yace iyayensa mutanen kirki ne kuma baya son a zagesu. https://www.tiktok.com/@danharuna44/video/7514262265588157702?_t=ZM-8x5Vf2vz8OW&_r=1 Wasu dai sun bayar da shawarar a kai yaron gidan mahaukata dan da alamar yana da tabin hankali.
Ba zamu baiwa Atiku takarar shugaban kasa a 2027 ba, dan kudu zamu tsayar takarar shugaban kasa a PDP>>Inji Wike

Ba zamu baiwa Atiku takarar shugaban kasa a 2027 ba, dan kudu zamu tsayar takarar shugaban kasa a PDP>>Inji Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya nanata cewa dole jam'iyyar PDP ta tsayar da dan takara daga kudancin Najeriya a shekarar 2027. Wike ya bayyana hakane a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da ya gudana ranar Litinin a Abuja. An gudanar da taronne dan warware matsalar dake tattare da jam'iyyar da kuma saitawa jam'iyyar Alkibla. Wike yayi gargadin cewa jam'iyyar PDP ta kama hanyar kashe kanta inda yace idan ba'a gyara ba aka ajiye jiji da kai da son rai ba, abinda ya faru a jam'iyyar a shekarar 2023 zai sake maimaita kansa. Yace kuma idan ana son Adalci da amfani da tsarin raba daidai da tsarin mulkin jam'iyyar PDP, dole a tsayar da dan takara daga kudancin Najeriya a jam'iyyar ta PDP.
Kalli Bidiyon me dokar bacci: An kama Dansanda na satar Wayar wutar Lantarki

Kalli Bidiyon me dokar bacci: An kama Dansanda na satar Wayar wutar Lantarki

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan wani dansanda ne da aka kama bisa zargin satar Wutar Lantarki. Rahoton yace an kamashi ne a Makurdi, babban birnin jihar Benue inda jamaa suka dakeshi. A Bidiyon an ganshi rigarshi da jini inda kuma ya amsa laifinsa da inda ya sato wayoyin wutar da aka ganshi dasu. Kalli Bidiyon anan Da yawa dai sun yi Allah wadai da halinsa.