Wani matashi a Bauchi ya hau kan karfen wayar Salula (Mast) ba zai sauko ba sai Dr. Bala Wunti ya yarda zai yi takaran gwamnan Bauchi a 2027.
Daga Humaid K Madaki
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa, Hukumar Ilimin bai daya UBE ta jihar ta dakate da albashin malaman makarantar Firamae 239 da aka samu da laifin rashin shiga aiki su koyar da dalibai ko rashin zuwa wajan aiki.
Shugaban hukumar, Prof. Haruna Musa ya bayyana cewa wannan kokari ne na tsaftace aikin gwamnati.
Sannan yayi kira ga al'umma da su rika lura su kai karar wadanda basa zuwa wajan aikin.
Daga cikin wadanda aka dakatar da albashin nasu akwai malamin da ya shekara 3 kanan bai je wajan aikin ba
Rahotanni sun ce Kamfanin Multichoice wanda su DSTV suke karkashin sa sun tafka mummunar asara saboda 'yan Najeriya da yawa sun daina saka kati suna kallon tashoshin.
Kudin shigar kamfanin a shekarar data gabata yayi kasa da kaso 44 cikin 100 inda a yanzu suka samu kudin shiga da ya kai dala Miliyan $197.74.
Saidai a shekarun baya suna samun kudin shiga da ya kai dala Miliyan $355.93.
Hakan na nufin sun tafka asarar dala Miliyan $158.19 idan aka kwatanta da shekarar data gabata.
Lamarin dai bai zowa mutane da mamaki ba musamman ganin yanda kasar ke cikin hali na matsin tattalin arziki.
Hakan kuma baya rasa nasaba da karin kudin subscription da DSTV din suka yi daga Naira N29,500 zuwa Naira 37,000 duk wata.
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya yace zai yi aiki tukuru dan goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce a shekarar 2027.
Gwamnan ya bayyana hakane a yayin kaddamar da wani shirin noma da kiwo a jiharsa.
Gwamnan yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya warew shirin Naira Biliyan 120 dan karfafa kiwo kuma ya amince a bayar da kaso 50 cikin 100 na kudin.
Yace babu shugaban Arewa da aka yi a baya da ya taba warewa bangaren kiwo irin wadannan makuda kudade duk da cewa yankin Arewa an sanshi da kiwo.
Yace bisa haka suna goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce.
Yace zasu goyi bayanshi ido Rufe dan ya sake zama shugaban kasa a 2027.
“I assure the President that for what he has done, is doing, and will do, Gombe people will follow him to the battlefield bl...
Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g
Tauraruwar Tiktok Murja Kunya ta bayyana cewa, bata yadda da matsayar jarumin Tiktok, Gfresh ba kan cewa mutanen dake zuwa duba Adam A. Zango sun yi yawa ba.
Gfresh ya yi Bidiyo inda yake kiran mutane su rage tururuwr da suke ta zuwa duba Adam A. Zango.
Saidai Murja tace Adam A. Zango na mutanene dan haka wannan shawara ta Gfresh bata karbu ba.
https://www.tiktok.com/@murjess1/video/7515950812531657991?_t=ZM-8xDePcFp5YG&_r=1
Adam A. Zango dai yayi hadari a hanyar Kaduna zuwa Kano a yayin da yake kan hanyar zuwa bikin Sallah.
Kuma mutane da yawa ne ke ta tururuwa suna zuwa dubashi.
Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g
Ma'aikatar noma ta Najeriya ta bayyana cewa manyan ma'aikatan hukumar ne ke ta mutuwa shiyasa ma'aikatar ta fito da tsarin yin Azumin dan neman taimakon Allah.
Hakan na zuwane bayan da aka samu rahotanni dake cewa, ma'aikatar ta nemi ma'aikatan ta da su dauki azumi dan neman nasarar wadatar Abinci a Najeriya.
Saidai a sanarwar da mataimakiyar me yada labarai ta hukumar, Ezeaja Ikemefuna ta fitar tace zancen ba haka yake ba.
Tace manyan ma'aikatan hukumar ne ke ta mutuwa akai-akai shiyasa suka fito da tsarin yin addu'a ta hanyar Azumi dan neman sauki da daukin Allah.
Saidai Tuni an dakatar da yin azumin wanda da za'a fara ranar Litinin bayan da cece-kuce yayi yawa akan Lamarin...
Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g
Bankin Duniya ya ware dala Miliyan $40 dan tallafi ga talakawa mafiya rauni a Najeriya.
Tun a watan Satumba na shekarar data gabata ne dai Bankin ya amince da bayar da wadannan kudade a matsayin bashi amma sai yanzu za'a bayar dasu.
Tallafin za'a bayar dashi ne da karfafa 'yan Najeriya da yawa kuma zai ci gaba har nan da zuwa shekara 2029
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, Tsohon Gwamnan Benue, Samuel Ortom, da tsohon Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu, da tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da sauransu sun kaiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ziyara.
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta tabbatar da kama wani ɗan kasar China bisa zargin taimaka wa ƴan ta’adda.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta tabbatar da kama wani ɗan ƙasar China yayin wani samamen yaƙi da ta’addanci da aka gudanar a Jihar Borno.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo- Markus Kangye, ne ya tabbatar da hakan a madaJanardin manyan hafsoshin soji a ranar Juma’a.
Sai dai Manjo-Janar Kangye bai bayyana sunan baƙon ba, amma ya ce mutumin da ya bayyana kansa a matsayin mai hakar ma’adanai yana hannun dakarun soji yanzu kuma ana ci gaba da bincikarsa.
Kama ɗan ƙasar China ɗin ya faru ne kasa da mako guda bayan rundunar soji ta bayyana kama wasu 'yan Pakistan huɗu da ake zargin suna koyar da 'yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.
Yayin da ake tambayarsa ...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump na shirin dakatar da karin kasashe 36 daga shiga kasar Amurkar kuma ana tsammanin Najeriya ka iya shiga ciki.
A cikin kasashen da Trump din ke shirin dakatarwa akwai kasashen Afrika guda 25 ciki hadda kasar Egypt da Djibouti sannan akwai kasashen Asia.
Kafar the Washington post ta kasar Amurkar tace ta yi kokarin jin ta bakin fadar White House amma abu ya ci tura.