Monday, December 22
Shadow
Idan Ana son yin sulhu da mu sai an daina kiran mu da sunan ‘yan ta’adda>>Inji Aliero

Idan Ana son yin sulhu da mu sai an daina kiran mu da sunan ‘yan ta’adda>>Inji Aliero

Duk Labarai
Babban dan Bindiga, Ado Aliero yace shi da yaransa ba zasu daina kai hare-hare da yin garkuwa da mutane ba sai an daina kiransu da sunan 'yan ta'adda. Zagazola Makama ya ruwaito cewa, Aliero ya fadi hakane a Dan Musa jihar Katsina yayin da aka yi zaman Sulhu dasu. Sarakunan gargajiya, Jami'an tsaro da shuwagabannin kananan hukumomi da 'yan Bindigar ne suka halarci wannan zaman na sulhu. Yace da yawan matasa da suka shiga harkar garkuwa da mutane matsin rayuwa nw ya jefasu cikin harkar. Yace iyayensu basa farin ciki da irin wannan rayuwar da suke yace ko da su kansu a zuciyarsu ba son irin wannan rayuwar suke ba, sun fi so a koma girmama juna musamman tsakaninsu da manoma. Yace dan haka kamin ma a fara maganar sulhu sai kowane sashe ya girmama dayan sashen.
Ƴansanda sun kuɓutar da mutum 73 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Ƴansanda sun kuɓutar da mutum 73 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta ce ta ceto mutum 73 da aka yi garkuwa da su. Ta kuma ce ta kama mutum 75 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar. Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, Abubakar Sadiq ya fitar, ta ce ana zargin mutum 15 cikin mutanen da laifin fashi da makamai, yayin da wasu 20 kuma da laifin kisa. "An kama mutum guda da laifin mallakar bindiga, 30 da zargin aikata fyaɗe sannan 108 kuma an kama su ne da wasu laifukan," in ji sanarwar. Sadiq ya ce makaman da aka ƙwato daga wajen mutanen sun haɗa da bindigar AK-49, karamar bindiga ƙirar pistol, ɗaruruwan harsasai, babura biyu da kuma shanu 174 da ake zargin sun sace. Ya ce ana ci gaba da kula da waɗanda aka kuɓutar daga hannun masu garkuwan.
Gwamnati ta ƙara yin gargaɗi kan yiwuwar ambaliya a wasu jihohin Najeriya

Gwamnati ta ƙara yin gargaɗi kan yiwuwar ambaliya a wasu jihohin Najeriya

Duk Labarai
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta ce akwai yiwuwar wasu jihohin Najeriya su fuskanci ambaliya a daminar bana. Wata sanarwa da NiMet ta fitar a shafinta na X, ta ce jihar Akwa Ibom ce tafi barazanar fuskantar ambaliyar a yanzu. Sauran jihohin sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Plateau, Yobe, Bauchi da kuma Bayelsa. Sai Nasarawa da Benue da Ogun da Ekiti da Delta da kuma Ribas. Don haka ne hukumar ta gargaɗi jama'a, musamman waɗanda ke jihohin da lamarin zai iya shafa, da su riƙa yashe magudanan ruwa domin buɗe wa ruwa hanyar wucewa. Ta shawarce su da su riƙa yin nesa da wuraren da ke da haɗarin ambaliya, inda ta ce in ta kama su tashi daga waɗannan wurare. A kowace shekara dai, ambaliya na yin sanadiyyar rayukan mutane da dama da kuma lalata gidaje a Najeriya. Ko a ...
Barayin waya sun kashe ma’aikacin Jami’ar Northwest ta Kano

Barayin waya sun kashe ma’aikacin Jami’ar Northwest ta Kano

Duk Labarai
Masu kwacen waya sun kashe wani ma'aikacin Jami'ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daba masa wuta. Bayanai sun nuna cewa barayin sun ritsa shi ne a yankin unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso, inda suka sossoke shi da wuka a ciki kuma suka kwace wayarsa, a ranar Laraba. Marigayin ya rasu bayan da aka garzaya da shi asibitin koyarwa na Mallama Aminu Kano, a jiya Juma'a. Shugaban kungiyar ma'aikatan jami'ar (NASU), Kwamared Bashir Muhammad, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya yi kira ga gwamnatin jihar kano da sauran hukumomi da su dauki tsattsauran mataki a kan kisan.
Mutum 1,296 aka kashe a Najeriya a watan Mayu – Rahoto

Mutum 1,296 aka kashe a Najeriya a watan Mayu – Rahoto

Duk Labarai
Mutum 1,296 aka kashe a Najeriya a watan Mayu - Rahoto. Wasu sabbin alƙalumma kan matsalar tsaro a Najeriya sun nuna cewa mutum 1,296 aka kashe a watan Mayu a sassan ƙasar. Rahoton na kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a shiyyar Afirka ta yamma da yankin Sahel ya ce an samu ƙaruwar yawan waɗanda suka mutu a watan Mayu idan aka kwatanta da Afrilu inda aka kashe mutum 1,092. Rahoton ya kuma ce mutum 1,086 aka yi garkuwa da su a sassan Najeriya a watan Mayu inda aka samu ragi idan aka kwatanta da watan Afrilu da aka yi garkuwa da mutum 1,178. Rahoton Beacon Security and Intelligence Limited ya nuna cewa an samu ragi na kashi kusan shida cikin dari na matsalolin tsaro a Najeriya cikin watan Mayun da ya gabata, idan aka kwatanta da yadda lamarin ya kasance a watan wa...
Iyayen mu basu yadda ba muka yi aure, kuma abokai biyu ne kawai suka halarci wajan daurin auren mu>>Inji Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yayin da yake taya matarsa, Titi murnar cika shekaru 75 a Duniya

Iyayen mu basu yadda ba muka yi aure, kuma abokai biyu ne kawai suka halarci wajan daurin auren mu>>Inji Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yayin da yake taya matarsa, Titi murnar cika shekaru 75 a Duniya

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya taya matarsa, Titi Abubakar murnar cika shekaru 75 a Duniya. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace yana godiya da hakuri da ta yi da rauninsa. Inda ya jawo hankalin ma'aurata su rika hakuri da juna. Atiku yace duka iyayensu basu amince ba suka yi aure kuma abokai 2 ne kadai suka halarci wajan daurin aurensu. Yace amma gashi yau sun cika shekaru fiye da 50 da yin aure. https://twitter.com/atiku/status/1933988213430825259?t=yORVI652VYZhEkNi5JukUA&s=19 Atiku ya bayyana hakane a shafin sa na sada zumunta.
Hukumar kula da sararin samaniyar Najeriyar Najeriya tace za’a yi ruwa sosai daga ranar Lahadi zuwa Litinin inda ta bayyana jihohin da hakan zau faru

Hukumar kula da sararin samaniyar Najeriyar Najeriya tace za’a yi ruwa sosai daga ranar Lahadi zuwa Litinin inda ta bayyana jihohin da hakan zau faru

Duk Labarai
Hukumar kula da sararin samaniyar Najeriyar, The Nigerian Meteorological Agency ta bayyana cewa, za'a yi ruwan sama aosai a jihohi daban-daban na Najeriya daga ranar Lahadi zuwa Litinin. Tace ruwan zai sauka a jihohin Taraba, Kebbi, Zamfara, Kaduna, da Adamawa ranar Asarar. Da kuma jihohin Kebbi, Taraba, Zamfara, Borno, Kaduna, Sokoto, Gombe, Bauchi. Imo, Enugu, Abia, Ebonyi, Anambra, Ondo, Oyo, Ogun, Ekiti, Edo, Lagos, Cross River, Akwa Ibom, Delta, Bayelsa, da Rivers. Hukumar ta kuma yi hasashen za'a sake yin ruwan ranar Litinin a Arewa da kudu.