Saturday, December 13
Shadow
Ku kara Hakuri, an kusa shan jar miya>>Shugaba Tinubu

Ku kara Hakuri, an kusa shan jar miya>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyanawa 'yan Najeriya cewa saukin rayuwa na nan kusa da bayyana. Ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Bayo Onanuga inda yace kowane sako da lungu na kasarnan zai shaida alfanin tsare-tsaren gwamnatinsa wanda nan gaba kadan za'a fara gani. Shugaba Tinubu yace a lokacin da ya hau mulki NNPCL baya iya kawo man fetur saboda bashi ya masa yawa yace amma a haka yayi kokari aka samu sauki. Yace kuma 'yan Najeriya da dama sun samu budin arziki a zamanin milkinsa.
A mulkin Tinubunnan nima yunwa ta kamani>>Inji Rotimi Amaechi

A mulkin Tinubunnan nima yunwa ta kamani>>Inji Rotimi Amaechi

Duk Labarai
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, Yunwa ta kamashi. Amaechi ya bayyana hakane a wajan taron zagayowar ranar haihuwarsa. Yace Dukkan mu nan muma cikin yunwa, idan baku ciki ni ina cikin yunwa. Amaechi yace duk da yana APC amma bai zabi Tinubu ba a matsayin shugaban kasa ba. Amaechi dai shine yazo na 2 a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a shekarar 2022 wanda Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya lashe zaben. Yace idan suka dage a matsayinsu na 'yan Adawa zasu iya kwace mulki daga hannun Tinubu.
Gwamnatin Nijeŕiya Ta Gargadi Sarkin Mota Kan Çiñ Mutùncin Ma’aikatan Gwamnati

Gwamnatin Nijeŕiya Ta Gargadi Sarkin Mota Kan Çiñ Mutùncin Ma’aikatan Gwamnati

Duk Labarai
Gwamnatin Nijeŕiya Ta Gargadi Sarkin Mota Kan Çiñ Mutùncin Ma’aikatan Gwamnati. Gwamnatin Nijeriya ta hannun Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) ta yi tsawatarwa ga wani dillalin mota da aka fi sani da “Sarkin Mota” kan wani bidiyo da ya yada inda ake ganin yana ba’a da raina ma’aikatan gwamnati. A cikin bidiyon, an ji Sarkin Mota yana tambayar na’urar AI na wata mota kirar **Mercedes. Ya kuke ganin wannan matakin da Gomnatin ta dauka? Daga Muhammad Kwairi Waziri
Kalli Bidiyon: Shahararren mawakin Najeriya, Portable ya nuna saniyar da zai yànkà da sallah

Kalli Bidiyon: Shahararren mawakin Najeriya, Portable ya nuna saniyar da zai yànkà da sallah

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shahararren mawakin Najeriya, Portable wanda yayi wakar Zazuzeh ya wallafa saniyar da zai yanka da Sallah. Ya bayyana cewa Naira Miliyan 1.5 ya sayota. https://www.youtube.com/watch?v=LIFZ3CSRcsY?si=Aq6fM0CjaWeVoZ-9 Da yawa sun masa fatan Alheri.
Gwamna Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31

Gwamna Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31

Duk Labarai
Gwamna Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31. Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, a ranar Lahadi ya aike da tawaga zuwa Jihar Kano domin yi wa gwamnatin jihar da al’ummar Kano ta’aziyya bisa rashin wasu 'yan wasa da jami'ai da suka rasu yayin dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala kwanan nan. Gwamna Abiodun ya kuma ba da gudummawar Naira miliyan daya (N1m) ga kowanne iyali daga cikin iyalan mamatan a matsayin taimako na farko, wanda jimillar kudin ta kai Naira miliyan 31. A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, mataimakiyar gwamna, Injiniya Noimot Salako-Oyedele ce ta jagoranci tawagar, da ta haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar Ogun, Mista Tokunbo Talabi; Kwamishinan Ci gaban Wasanni, Hon. Wasiu Isiaka; da Sakatar...
Rahoto: Gwamnati ta gano gurɓacewar iska a wasu unguwanni a jihar Kano

Rahoto: Gwamnati ta gano gurɓacewar iska a wasu unguwanni a jihar Kano

Duk Labarai
Wani rahoto na mako-mako kan yanayin lafiyar iska da gwamnatin Kano ke saki ya nuna cewa akwai gurɓatar iska a wasu unguwanni a cikin ƙwaryar Kano, inda hakan zai ƙara ta'azzara yaɗuwar cutuka a cikin al'umma. Rahoton, wanda Ma'aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta fitar bayan gwajin lafiyar iska da ta yi tsakanin 26 zuwa 30 ga watan Mayun da mu ka yi bankwana da shi, ya nuna cewa unguwanni kamar su Gaida, Ja'en, Sabon Titi da Sharada Kasuwa, basu da lafiyayyar iska, inda sakamakon ya nuna akwai gurɓatar iska a waɗannan unguwanni. Rahoton ya nuna cewa gwamnatin Kano na shirin kai ɗauki a wadannan unguwanni sakamakon gurɓacewar iska, inda ta nuna damuwa kan karin gurɓacewar yanayi da ake samu a jihar. Kwamishinan Ma'aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir M Hashim ne ya wallafa...
Saudiyya ta tanadi jami’an tsaro 40,000 domin Hajjin bana

Saudiyya ta tanadi jami’an tsaro 40,000 domin Hajjin bana

Duk Labarai
Saudiyya ta tura sama da jami’an tsaro 40,000 don tabbatar da tsaro yayin aikin hajjin 2025. Da yake jawabi a wani bikin gagarumin faretin soji da aka gudanar a birnin Makkah, Mohammad bin Abdullah Al-Bassami, darektan tsaron jama'a kuma shugaban kwamitin tsaron hajji, ya ce dukkan sassan tsaro an tura su domin aiwatar da shirin tsaro na bana, tare da karin bayani cewa jami’an tsaron suna cikin shirin ko-ta-kwana kuma a shirye suke su dauki matakin gaggawa idan ya taso. “An tanadi dukkan abinda ake bukata domin tabbatar da tsaron lafiyar mahajjata da jin dadinsu a lokacin aikin hajji,” in ji shi. “Jami’an tsaronmu suna cikin matakin shiri mafi girma don fuskantar kowanne hali da zai iya barazana ga tsarkin wannan ibada. “Muna da kwarin guiwar tabbatar da cewa mahajjata za su gu...
Mahaifiyar dalibi me rubuta jarabawar WAEC ta dauko hayar ‘yan Iska sun zane malamin danta saboda ya hana dan nata satar Jarabawa

Mahaifiyar dalibi me rubuta jarabawar WAEC ta dauko hayar ‘yan Iska sun zane malamin danta saboda ya hana dan nata satar Jarabawa

Duk Labarai
Wani malami a makarantar Complete Child Development College Aule dake Akure jihar Ondo ya sha duka bayan da ya hana daya daga cikin dalibansa satar jarabawa a yayin da ake rubuta jarabawar WAEC. Ana zargin mahaifiyar dalibinne ta dauki hayar 'yan Iska suka zane malamin Dama dai malamin da farko ya hana dalibin satar jarabawa saidai dalibin yaki dainawa inda ya gayawa mahaifiyarsa. Mahaifiyarsa ta je makarantar inda ta yi barazanar yin maganin duk wanda ya sake ya hana danta satar Jarabawa. Saidai malamin me suna Rotifa wanda shine mataimakin shugaban makarantar ya sha alwashin sai ya hana dalibin satar jarabawar duk da barazanar mahaifiyarsa. Hakan kuwa aka yi da dalibin ya koma makarantar sai ya je da waya ya fiddo zai yi satar Amsa amma malamin ya kwace wayar. Nan ne ma...
Shugaban kasar Nijar ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da kasarsa

Shugaban kasar Nijar ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da kasarsa

Duk Labarai
Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya da haɗa baki da Faransa da China da Amurka wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a ƙasarsa. A cikin wani jawabi na awa uku da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na Radio-Télévision du Niger (RTN) a ƙarshen mako, Tchiani ya yi magana da harshen Hausa, Zabarma da Faransanci, inda ya zargi Najeriya da Jamhuriyar Benin da Faransa da China da Aljeriya da Amurka da kokarin dagula ko cutar Nijar da sauran ƙasashen da ke cikin ƙawancen AES. Wannan shi ne karo na biyu da Tchiani ke zargin Najeriya a yayin wata hira da ya yi ta ranar Kirsimeti a bara, inda ya ce Faransa na haɗa baki da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin tafkin Chadi domin lalata tsaron Nijar, tare da sanin Najeriya. Tchiani ya ƙara da cewa an ...
Dakarun sojin ruwa na Najeriya sun yi kaɗan wajen tsaron ƙasa>>Inji Shugaban Sojojin

Dakarun sojin ruwa na Najeriya sun yi kaɗan wajen tsaron ƙasa>>Inji Shugaban Sojojin

Duk Labarai
Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya ya ce dakarunsa sun yi kaɗan wajen tabbatar da tsaron gaɓar ruwan ƙasar da kuma daƙile satar man fetur. Da yake magana ta kafar talabijin ta Channels TV a yau Litinin, Vice Admiral Emmanuel Ogalla ya ce jimillar dakarun rundunar tasa ba su 30,000 da ɗoriya ba. Sai dai ya ƙara da cewa mahukunta sun ƙara yawan adadin mutanen da suke ɗauka duk shekara domin cike giɓin. "Za ku sha mamaki idan kuka ji cewa dakarun rundunar sojin ruwa ba su wuce 30,000 da ɗoriya ba," in ji shi. "Amma kuma muna da gaɓar ruwa mai girman kashi ɗaya cikin uku na faɗin ƙasar Najeriya baki ɗaya. Muhimmin abu dai shi ne muna ƙoƙarin ƙara yawan dakarun."