Monday, December 22
Shadow
Bayan da suka ta yi yawa, Ministan Abuja, Nyesom Wike yace baya dana sanin Sakawa babban dakin Taron Najeriya sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Bayan da suka ta yi yawa, Ministan Abuja, Nyesom Wike yace baya dana sanin Sakawa babban dakin Taron Najeriya sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
'Yan Najeriya, Musamman kungiyoyin fafutuka, sun yi Allah wadai da sakawa babban dakin taron Najeriya dake Abuja sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ministan Abuja, Nyesom Wike ya canjawa babban dakin taron sunane bayan da ya gyarashi. An gano akalla gurare 7 da suka hada da barikin sojoji da filin jirgin sama da sauransu wadanda aka sakawa sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Lamarin yasa abin ya fara damun mutane musamman masu fafutukar kare hakkin al'umma suka fara suka. Saidai a martaninsa, Wike Ya bayyana cewa duk me suka ya je yayi ta yi, yace ya ji wasu na cewa, wai ba Tinubu ne ya gina dakin taron ba. Yace to gurare da yawa da aka sakawa sunayen manyan mutane, kamar su Filin jirgin sama na Murtala Muhammad da Nnamdi Azikwe ai duk ba su ne suka ginasu ba. ...
An ga fastocin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a kafafen sada zumunta, Ya mayar da martani

An ga fastocin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a kafafen sada zumunta, Ya mayar da martani

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana fastocin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a kafafen sada zumunta inda aka ga yana neman tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027. An ga fastocinne a kafar Instagram. Shafin da ya wallafa labarin na dauke da sunan tsohon shugaban kasar ne inda ya soki gwamnati me ci. Saidai da aka Tambayi kakakin Jonathan din me suna Ikechukwu Eze ya musanta cewa ba Jonathan ne ya ke yakin neman zabeba, bashi ma amfani da shafin Instagram. Ba wannan ne karin farko da ake amfani da sunan tsohon shugaban kasar ana nuna yana neman sake tsayawa takarar shugaban kasa ba, ko da a shekarar 2023 ma an samu wasu suka rika amfani da sunansa suna cewa ya fito takarar shugaban kasa.
Gwamnatin Tarayya da hadin kan kasar China zata tayar da kamfanin karafa na Ajakuta

Gwamnatin Tarayya da hadin kan kasar China zata tayar da kamfanin karafa na Ajakuta

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya a ranar Juma'a ta bayyana aniyarta ta son tayar da kamfanin Karafa na Ajakuta dan kirkiro ayyukan yi ga matasa. Gwamnatin tace Tuni ta fara hadaka da kamfanonin kasar China da kuma neman kudi dan tayar da kamfanin da ya dade a lalace. Hakan na cikin shirin ministan Karafa, Shuaibu Audu wanda a yanzu haka yake jagorantar wata tawaga daga Najeriya zuwa kasar China dan jawo hankalin masu zuba Jari zuwa Najeriya. Hadimin Ministan, Lizzy Okoji ya bayyana cewa, tuni tawagar ta fara ganawa da kamfanonin kasar China irin su Sino Steel, da Fangda Steel da Jingye Steel. Ministan yace dawo da kamfanin karafan na Ajakuta ya ci gaba da aiki na daya daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta sanya a gaba kuma zasu cimma nasara kamin karshen mulkins...
Kasar Pakistan ta bayyana goyon baya ga Ìràn

Kasar Pakistan ta bayyana goyon baya ga Ìràn

Duk Labarai
Kasar Pakistan ta bayyana cewa, tana goyon bayan kasar Iran a ci gaba da gumurzun da suke da kasar Israyla. Pakistan ta yi Allah wadai da hare-haren da kasar ta Israyla ta kaiwa Iran inda a wasu rahotannin ta bayyana cewa, a shirye take ta goyi bayan Iran a wannan rikici. A jiyane dai yaki ya barke tsakanin Israyla da Iran inda Israyla ta fara kaiwa Iran hari inda ta kashe manyan sojojinta da dayawa daga cikin masana kimiyyar ta. Kasar dai ta zargi Iran da yunkurin mallakar makamin Kare dangi wanda tace ba zata amince da hakan ba. Israyla ta kaiwa Iran hare-hare akan tashar inganta makamin kare danginta. Saidai daga baya itama iran ta yi ramuwar gayya.
An gano Majalisar tarayya ta cusa jimullar Naira Tiriliyan 10.96 a cikin kasafin kudin Najeriya cikin shekaru 4

An gano Majalisar tarayya ta cusa jimullar Naira Tiriliyan 10.96 a cikin kasafin kudin Najeriya cikin shekaru 4

Duk Labarai
Wasu kungiyoyin fafutuka sun yi Allah wadai da majalisar tarayya saboda cusa jimullar Naira Tiriliyan N10.96tn a cikin kasafin kudin Najeriya a tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025. Kungiyoyin sun bayyana hakan da cewa bai dace ba inda suka nemi hukumomin yaki da rashawa da cin hanci na Najeriya dasu yi bincike kan wannan zargin. Kungiyoyin da suka yi wannan zargin sune the Socio-Economic Rights and Accountability Project, da kuma the Centre for Anti-Corruption and Open Leadership. Kungiyar BudgIT ce ta fara yin wannan bincike inda tace jimullar ayyukan da aka cusa a cikin kasafin kudin sun kai 30,632.
Duk wanda baya son Gwamnatin Tinubu na iya zuwa ya kàshè kanshi dama mun yi yawa a Najeriya>>Wike

Duk wanda baya son Gwamnatin Tinubu na iya zuwa ya kàshè kanshi dama mun yi yawa a Najeriya>>Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, duk wanda baya tare da Gwamnatin Tinubu na iya zuwa ya mutu dama mun yi yawa a Najeriya. Yace shi zai bayar da filima a binne duk me son mutuwa. Wike ya bayyana hakane inda yace ya gani a wani gidan talabijin ana sukar sakawa babban dakin taro na Abuja sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Wike yace dalilin da suke bayarwa wai shine me yasa ba'a saka sunan wanda ya gina dakin taron ba. Wike yace wannan maganar banza ce. Yace akwai gurare da aka sakawa sunayen manyan mutane wadanda basu ne suka ginasu ba irin su FIlin Jirgin sama n Murtala dake Kano da

Da Duminsa: Ana sa Ran cikin darennan kasar Ìràn zata yi gwajin makamin Nòkìlìyà

Duk Labarai
Rahotanni daga kafafe da yawa sun ce ana tsammanin kasar Iran zata yi gwajin makamin Nokiliya a cikin darennan. Saidai Iran din bata bayyana hakan a hukumance ba. Idan Iran ta yi gwajin makamin Nokiliya din, to lallai ya tabbata ta mallakeshi kuma za'a kiyayeta. Watakila hakan ya kawo karshen yakin dan gudun kada ta jefawa kasar Israyla. Iran dai ta ki yadda Ayi sulhu dan ta daina shirin mallakar makamin kare dangi.

Labari Me Dadi: Makamin dake tare makamai da kakkabo jirage na kasar Iran ya dawo aiki bayan da Israyla ta musu kutse

Duk Labarai
Bayan da kasar Israyla tawa makaman tare hari da kakkabo jiragen sama na kasar Iran kutse, a yanzu ya dawo aiki tukuru. Harba ya harbo jirgin Israyla F-35 sannan sun kama mace matukiyar jirgin. https://twitter.com/Megatron_ron/status/1933634825602412759?s=19 Iran itace kasa ta Farko a Duniya data taba kakkabo wannan jirgin na Israyla. https://twitter.com/WarMonitors/status/1933630986220106229?t=pjwlPWagZztdqgdFe8h6qQ&s=19 Rahotanni sun ce makamin ya ci gaba da kakkabo jirage marasa matuka na kasar Israyla. https://twitter.com/Megatron_ron/status/1933637359435665787?s=19 Sannan 'yan kasar sun taru sai shewa suke.
Kasar Ìràn na mayar da martani me zafi

Kasar Ìràn na mayar da martani me zafi

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Israyla na cewa, kasar Iran ta cillawa Israylan manyan makamai sosai. Bidiyo ya nuna yanda makaman kasar Iran suka rika keta makaman tsaro na Israeyla suna mata barna. Rahotanni sun ce iran ta jefawa Israyla makamai akalla guda 800. Hare-hare Iran sun lalata gine-gine akalla 9, wasu 100 kuma an lalata su amma ba duka ba. https://twitter.com/I__military/status/1933619888314331601?t=fc-ipnlSknycH8rvKu_wow&s=19 https://twitter.com/I__military/status/1933609851818815936?t=YIOf8EzL4W-Qm3ec8PH-tg&s=19 Daga cikin gine-ginen da aka lalata hadda ginin ma'aikatar tsaro ta kasar Iran din. https://twitter.com/Megatron_ron/status/1933603426396483646?t=Wjkpy8u_t6d0-2I2i-PO1Q&s=19 Lamarin ya firgita mutanen kasar Israyla inda suka rik...
Israyla ta kaiwa tashar Nùkiliya din kasar Ìràn mafi tsaro hari

Israyla ta kaiwa tashar Nùkiliya din kasar Ìràn mafi tsaro hari

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotanni daga kasar Iran na cewa, jiragen yakin kasar Israyla na ci gaba da ludugen wuta a kasar. Rahotanni sun ce yanzu haka jiragen sun yiwa tashar Nùkiliya mafi tsaro a kasar Iran me suna FORDO luguden bamabamai inda rahotanni suka ce an ji karar fashewar abubuwa har sau biyu. Ita dai wannan tashar Nokiliya a karkashin kasa take kuma an ginata ne da cewa bam din Buñkèr Bustèr ba zai iya lalata ba watau bam me tono kasa. Rahotanni sin ce taba wannan gurin zai iya harzuka ka...