Monday, December 22
Shadow
Masana a Amurka sun ce hare-haren kasar Israyla kadai ba zai iya hana kasar Ìràn mallakar makamin kare dangi ba saida taimakon Amurka

Masana a Amurka sun ce hare-haren kasar Israyla kadai ba zai iya hana kasar Ìràn mallakar makamin kare dangi ba saida taimakon Amurka

Duk Labarai
Wani Rahoto daga kafar Newsweek yace masana a Amurka sun ce hare-haren kasar Israyla kadai ba zai iya hana kasar Iran mallakar makamin kare dangi ba. Rahoton yace dole sai kasar Amurkar ta taimakawa Israyla. Rahoton yace ko da ma Amurkar ta taimakawa Israylan, idan dai ba kawar da gwamnati me ci suka yi daga kan mulki ba, za'a dakatar da shirin ne na dan wani lokaci amma za'a ci gaba. Dan haka rahotan yace ko da basu yi nasarar kawar da Gwamnatin kasar daga kan mulki ba, su gurguntata ta yanda mutanen kasar zasu tashi tsaye su nemi sauyin gwamnatin Dimokradiyya. Hakan na zuwane yayin da ake rade-radin kasar Amurka na shirin shiga fadan.
Yanzu-Yanzu: Kàsàr Amùrkà tà shìgà fàdàn Israyla da Ìràn tà aìkà dà manyan jiragen ruwa dauke da jiragen yaki gabas ta tsakiya

Yanzu-Yanzu: Kàsàr Amùrkà tà shìgà fàdàn Israyla da Ìràn tà aìkà dà manyan jiragen ruwa dauke da jiragen yaki gabas ta tsakiya

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, kasar ta aike da jiragen ruwa dauke da jiragen yaki zuwa gabas ta tsakiya. A baya dai Amurka ta nuna goyon bayan ta ga kasar Israyla a harin da ta afkawa kasar Ìràn. Kasar Israyla ta kashe manyan sojoji da masana Kimiyyar Nòkìlìyà na kasar Iran da dama. Zuwa yanzu bai babu wani rahoton babbar martani da Iran ta dauka akan kasar Israyla.
Da Duminsa: Zàngà-zàngà ta barke a kasar Ìràn inda ‘yan kasar ke neman ta mayarwa da Israyla martani me zafi kan kìsàn da tawa manyan mutanen kasar

Da Duminsa: Zàngà-zàngà ta barke a kasar Ìràn inda ‘yan kasar ke neman ta mayarwa da Israyla martani me zafi kan kìsàn da tawa manyan mutanen kasar

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Iran na cewa, Zanga-zanga ta barke inda mutanen kasar ke neman kasar tasu ta mayar da martani me zafi kan kasar Israyla. Bidiyo sun bayyana inda aka nuna Iraniyawa maza da mata na kuka suna dauke da hotunan mutanen da aka kashe a kasar. Masana kimiyyar Nòkìlìyà da manyan sojojin kasar da yawa ne aka kashe. Lamarin ya zo da ba zata inda kasar iran din bata tabuka wani kokari na kare harin da aka afka mata ba.
Kafar Yada labaran Amurka me suna Axios ta ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump karya yake da yace bai goyi bayan kaiwa Ìràn hari ba, Zambatar Ìràn din yayi dan kada wadanda suke son kàshèwà su boye

Kafar Axios ta kasar Amurka tace ta gano cewa shugaban kasat Amurka, Donald Trump karya yake da yace baya goyon bayan harin da aka kaiwa kasar Ìràn. Kafar tace ta yi magana da wata majiya 2 daga Israyla wadda ta tabbatar mata da cewa sai da kasar Amurkar ta amince sannan suka kaiwa kasar Ìràn hari. Kafar tace shugaban Amurka Donald Trump ya nuna cewa bai san da harin bane dan yaudarar wadanda suke son kashewa su tsaya kada su boye kamin a kashèsu. Shugaba Trump dai yayi ikirarin cewa, ya gargadi kasar Israyla kada ta kaiwa kasar Iràn hari, amma idan wannan rahoton na kafar Axios ya tabbata, to lallai ya munafurci mutane.
Jirgi ko daya marar matuki da kasar Iran ta jefawa Israyla bai kai kasar Israylan ba, Kasashen, Saudi Arabia, Jordan, Qatar, Turkiyya, UAE duk sun tare su

Jirgi ko daya marar matuki da kasar Iran ta jefawa Israyla bai kai kasar Israylan ba, Kasashen, Saudi Arabia, Jordan, Qatar, Turkiyya, UAE duk sun tare su

Duk Labarai
Rahotanni daga gabas ta tsakiya na cewa kasashen Larabawa na cikin wadanda suka tare jirage marasa matuka 100 da kasar Iran ta jefawa Israyla a matsayin martani. Kasashen Larabawan da suka tare wadannan makamai sun hada da Saudi Arabia, Jordan, Qatar, Turkiyya, UAE. Sannan kuma akwai kasar Azerbaijan, da Israyla, da Amurka, da Ingila. Rahotanni sun ce sai da Israyla ta kwace iko da dukkanin sararin samaniyar kasar Iran tana cin karanta babu babbaka da jiragen yakinta.
Mun ci gaba da kaiwa Kasar Ìràn hari>>Inji Sojojin kasar Israyla

Mun ci gaba da kaiwa Kasar Ìràn hari>>Inji Sojojin kasar Israyla

Duk Labarai
Sojojin kasar Israyla sun bayyana cewa, sun ci gaba da kaiwa kasar Iran hari. Hakan na zuwane bayan da a baya muka kawo muku rahoton cewa, an ga jiragen yakin kasar Israyla na ci gaba da shawagi a sararin samaniyar kasar Iran. Sun samu wannan nasarar ne bayan lalata makaman dake kakkabo jiragen sama na kasar ta Iran. Kasar ta Israela tace kamata yayi ta kammala kaiwa Iran hari a cikin kwanaki 2 amma sun ga alamu na nuni da cewa harin zai iya kai akalla sati biyu suna kaiwa.
Sai da na gargadi duka manyan sojojin Ìràn akan a yi Sulhu amma suka ki saurarona, gashinan duk an kàshèsù>>Shugaban Amurka Donald Trump

Sai da na gargadi duka manyan sojojin Ìràn akan a yi Sulhu amma suka ki saurarona, gashinan duk an kàshèsù>>Shugaban Amurka Donald Trump

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, sai da ya gargadi duka manyan sojojin Kasar Ìràn cewa a yi sulhu amma suka kiya. Yacw gashinan duk an kashesu. Yace Ya gargadesu Amurka ce ke kera makaman da babu irin su a Duk Duniya, kuma kasar Israyla na da wadannan makamai kuma ta iya aiki dasu. Yace amma duk suka ki saurarensa. Yace amma har yanzu akwai sauran lokaci be kure ba, kamin a gama lalata kasar Iran din baki daya, zasu iya zuwa a yi sulhu. A ranar Alhamis ne dai ake sa ran ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran kan shirinta na mallakar makamin kare dangi. Saidai Iran din tace ba zata halarci ci gaba da tattaunawar ba.
Cikakken rahoto kan irin mummunar barnar da kasar Israyla tawa kasar Ìràn a hàrè-hàrèn da ta kai mata, harin ya kàshè fararen hula da dama, an gano karin manyan sojoji da masana kimiyya da harin ya kàshè

Da Asubar yau Juma'a ne aka tashi da mummunan rahotan harin kasar Israyla akan kasar Iran. Israyla tace ta kaiwa gurare akalla 12 a cikin kasar Iran hare-haren. Wani abin mamaki shine yanda aka ga jiragen kasar Israyla na shawagi a sararin samaniyar kasar Iran suna ta kai hari inda suke so ba tare da makamai masu kakkabo jirgin sama na Iran sun yi kokarin harbo jiragen ba. Wasu rahotanni da ba'a tabbatar da su ba amma suna da alamar gaskiya sun ce Israyla ta yiwa makaman kakkabo jiragen sama na kasar Iran Kutse ta hanasu aiki kamin ta kai harin, shiyasa suka kasa harbo jiragenta. Ana zargin akwai sa hannun wasu munafukai 'yan kasar Iran da suka bayar da bayanai akan kasar kamin harin. Wannan Bidiyon na kasa ya nuna yanda Israyla ta jefa makamai masu lalata maboyar karkashin...
Kalli Bidiyon jiragen sama 100 marasa maruka da kasar Ìràn ta harbawa kasar Israyla

Kalli Bidiyon jiragen sama 100 marasa maruka da kasar Ìràn ta harbawa kasar Israyla

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Kasar Iran ta harbawa kasar Israyla jirage marasa matuka 100. Ga Bidiyon yanda lamarin ya faru kamar haka: https://twitter.com/ME_Observer_/status/1933406333203513430?t=YEbsDe3lfCwq9ShGoiM18g&s=19 https://twitter.com/DD_Geopolitics/status/1933405369000456316?t=TkuLir4rlCPoMgp45uzwyg&s=19 Zuwa yanzu dai babu rahoton irin barnar da harin Iran yayi a kasar Israyla saboda kasar ta haramtawa 'yan kasarta daukar hotunan sakamakon hare-haren.
YANZU-YANZU: Iran ta harbawa kasar Israyla jirage marasa matuka guda 100

YANZU-YANZU: Iran ta harbawa kasar Israyla jirage marasa matuka guda 100

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotanni daga kasar Iran na cewa shugaban juyin juya hali na kasar Ayatollah Khameini ya baiwa sojojin kasar Umarnin su mayarwa da kasar Israyla martani. Martanin farko shine kasar Iran ta jefawa kasar Israyla jirage marasa matuka guda 100. Rahoton yace sojojin Israyla sun ce suna kokarin tare wannan hari.