Kalli Bidiyon:Sheikh Lawan Triumph yayi Allah ya isa ga abinda tawagar Sarki Sanusi II suka yi a kofar gidan Aminu Dogo Dantata
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Lawan Triumph yayi Allah ya isa kan abinda 'yan Bindiga na tawagar hawan Sallahn Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II suka yi a kofar gidan Aminu Dantata.
An zargi 'yan bindigar da buga Bindiga a kofar gidan Aminu Dogo Dantata inda aka ji suna cewa ku buga mai ya mutu.
Saidai wasu na ganin wannan ba wani Abu bane saboda al'adace wadda kuma ko lokacin tsohon sarki ana yinta.
https://www.tiktok.com/@arewaupdatesng/video/7515560323517041925?_t=ZM-8xCFtxmLMEH&_r=1
Sheikh Lawan yayi Allah ya Isa ga wadanda suka saka 'yan Bindigar suka yi wannan abu wanda ya kira da rashin da'a.








