Ka Daina Boye-Boye Ka Fito Fili Ka Koma Jam’iyyar APC, Matawalle Ga Gwamnan Zamfara
Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, kuma tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Mohammed Matawalle, ya bukaci Gwamna mai ci, Dr. Dauda Lawal, da ya fito fili ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar APC ya daina wani boye-boye.
Da yake jawabi a gidansa da ke Maradun yayin wata ziyarar gaisuwar Sallah da dubban magoya baya suka kai masa, Matawalle ya ce lokaci ya yi da Gwamna Lawal zai daina “kumbiya-kumbiya" yana rufa-rufa” ya fito fili ya bayyana matsayarsa a jam'iyyance.
“Kofar jam’iyyarmu a bude take ga duk wanda ke neman ci gaban gaskiya ga jihar Zamfara da Nijeriya,” inji Matawalle, yana mai jaddada cewa bai dauki komai a ransa ba dangane da zabin siyasar Gwamna Lawal.
Ya ce APC jam’iyya ce da ke kan turbar tawali’u, gaskiya da shugabanci nagari.
“Muna kira gare shi ya ...








