Saturday, April 25
Shadow
Tinubu ya amince da biliyan 16 don sake gina gadar Mokwa – Mohammed Idris

Tinubu ya amince da biliyan 16 don sake gina gadar Mokwa – Mohammed Idris

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da kashe naira biliyan 16.7 domin sake gina gadar Mokwa da ke jihar Neja a tsakiyar ƙasar, wadda ambaliya ta lalata. Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a yau Asabar, yayin da shi kuma Ministan Ayyuka David Umahi ya ce shugaban ya amince da yin irin wannan aiki a jihohi da dama. "Muna godiya ga shugaban ƙasa da minista [na ayyuka]. Tattaunawa kawai muka yi da shi kafin mu je wajen shugaban ƙasa, wanda shi kuma ya amince. Abu ne mai muhimmanci ga al'umma," a cewar Idris. Umahi ya ce sauran jihohin da za a yi aikin sun ƙunshi gadar Wukari a jihar Taraba, da gadar Lokoja a jihar Kogi, da gadar Afikpo a jihar Ebonyi, da gadar sama ta Keffi a jihar Nasarawa, da gadar Jebba a Kwara, da gadoji bakwai a jihar Edo, da kuma wata g...
A soke zaben cike gurbi na Kano, Bamu yadda dashi ba>>Inji Jam’iyyar APC

A soke zaben cike gurbi na Kano, Bamu yadda dashi ba>>Inji Jam’iyyar APC

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, bata yadda da zaben cike gurbi na Kano ba inda tace INEC ta sokeshi da gaggawa. Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Felix Morka ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Asabar inda yace suna kira ga INEC ta soke zaben da gaggawa. Yayi zargin cewa, 'yan Bangar siyasa a Shanono da Bagwai da Ghari sun tayar da hankula sosai ta hanyar amfani da muggan makamai. Yace masu zabe dole suka tsere inda suka sha karfin jami'an tsaron da aka kai wajan wanda hakan yasa zabe me inganci ba zai samu ba.
Zaɓen cike gurbi: Shugaban karamar hukumar Municipal a jihar Kano kenan, Salim Hashim, ya ke dafa taliyar indomie domin karin kumallo ga ƴan jam’iyyar NNPP da ke garin Shanono don gudanar da zaben cike gurbi

Zaɓen cike gurbi: Shugaban karamar hukumar Municipal a jihar Kano kenan, Salim Hashim, ya ke dafa taliyar indomie domin karin kumallo ga ƴan jam’iyyar NNPP da ke garin Shanono don gudanar da zaben cike gurbi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shugaban karamar hukumar Municipal a jihar Kano kenan, Salim Hashim, ya ke dafa taliyar indomie domin karin kumallo ga ƴan jam'iyyar NNPP da ke garin Shanono don gudanar da zaben cike gurbi
A karo na biyu, NNPCL sun sake rage farashin man Fetur a Abuja da Legas kadai

A karo na biyu, NNPCL sun sake rage farashin man Fetur a Abuja da Legas kadai

Duk Labarai
Rahotanni daga Abuja da Legas na cewa, Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya sake rage farashin man fetur a garuruwan biyu da Naira 10. Kafar The Cable ta ruwaito cewa ta lura a Abuja ana sayar da man fetur din akan naira N890 maimakon Naira 900, hakanan a Legas kuma ana sayar dashi akan Naira N865 maimakon Naira N875. Kafar tace ta gudanar da wannan bincike ne a ranar Juma'a data gabata. Hutudole ya lura Wannan ne karo na biyu da hakan ke faruwa.
Kalli Bidiyo: Na yi Mafarki Sheikh Ibrahim ya riko hannun Ibro zai kaishi gaban Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Alhaji Anisee

Kalli Bidiyo: Na yi Mafarki Sheikh Ibrahim ya riko hannun Ibro zai kaishi gaban Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Alhaji Anisee

Duk Labarai
Shahararren dan Darika, Alhaji Anisee ya bayyana cewa, yayi mafarkin Sheikh Ibrahim ya kamo hannun Marigayi shahararren me wasan Barkwanci, Ibro zai kaishi gaban Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). Ya bayyana cewa sun hadu amma bai bisu ba. https://www.tiktok.com/@alhajianisee1/video/7538931827612863751?_t=ZS-8yvKFrvIw08&_r=1
Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo

Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo

Duk Labarai
Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Hadejia, Auyo da Kafin Hausa dake jihar Jigawa, Honarabul Usman Ibrahim Auyo, wanda ake yi wa lakabi da Kamfani ya nesanta kansa da labarin karya da aka yada akansa, wanda aka ce ya ce ba a ba su damar gabatar da kudiri a majalisa har sai sun bada cin hancin naira milyan uku ko fiye da haka. Sannan kuma sai sun yi ta kamun kafa ga sauran 'yan majalisun. A cewarsa ba ya na nufin majalisa ake baiwa wannan kudin ba, a duk sanda mutum zai gabatar da kudiri, akwai wadanda daga waje aikin su shine ka ba su kwangilar rubuta maka kudiri ka biya su, kafin daga bisani ka nemi shawarwari daga wajen takwaro...
YANZU-YANZU: Jami’an DSS Sun Kama Wani Ejan Din PDP Da Kusan Naira Milyan 30 Domin Siyan Kuri’u A Yayin Zaben Cike Gurbi A Kaduna

YANZU-YANZU: Jami’an DSS Sun Kama Wani Ejan Din PDP Da Kusan Naira Milyan 30 Domin Siyan Kuri’u A Yayin Zaben Cike Gurbi A Kaduna

Duk Labarai
Mutumin mai suna Shehu Fantage, an kama shine a jiya Juma'a a wani otal dake cikin garin Kaduna, a yayin da yake kokarin kasafta kudin domin yin amfani da su wajen siyen kuri'u a zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya mai wakiltar Chikun/Kajuru. Ita na hukumar 'yan sandan jihar Kaduna ta bakin kakakinta, DSP Mansir Hassan ta tabbatar da kama mutumin da DSS suka yi, inda yake komar su kuma ana kan bincikensa.