Friday, December 19
Shadow
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a 6, da Litinin 9 ga watan Yuni, 2025 a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan babbar Sallah na bana

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a 6, da Litinin 9 ga watan Yuni, 2025 a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan babbar Sallah na bana

Duk Labarai
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya daukacin al’ummar musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar sallah. Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin koyi da sadaukarwa da imani da kuma amfani da wannan lokacin wajen yi wa Nijeriya addu’a ta zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gyare-gyare da tsare-tsare da suka shafi jama’a da aka yi, a ci gaban ajandar sabunta fata na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, shi ne dawo da Nijeriya kan turbar ci gaba. Yayin da yake yiwa al'ummar musulmi barka da Sallah, Ministan ya bukaci dukkan 'yan Najeriya da su hada kai da gwamnati mai ci a kokarinta na dawo da martabar Najeriya a matsayin kasa mai girma.
Sunan Muhammad ya shiga cikin sunaye mafiya shahara a kasashen Turai da ake sakawa Jarirai

Sunan Muhammad ya shiga cikin sunaye mafiya shahara a kasashen Turai da ake sakawa Jarirai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, sunan Muhammad ya shiga cikin jerin sunaye mafiya shahara a kasar Ingila inda aka sakawa jarirai 4,661 sunan. A Brussels kuwa sunan Mohamed shine yazo na daya. Hakanan a Jamus ma sunan Muhammad ya shahara sosai. A Netherlands kuwa sunan Muhammad shine ya zo na 2. A Norway kuwa sunan Mohammed na daya yazo. A Ireland ma sunan Muhammad ya taba zuwa na daya a shekarar 2022.
Bama sacewa ko yin Almubazzaranci da kudin da muka ciyo bashi, ayyukan gina kasa muke yi dasu>>Inji Shugaba Tinubu

Bama sacewa ko yin Almubazzaranci da kudin da muka ciyo bashi, ayyukan gina kasa muke yi dasu>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, basa sacewa ko yin Almubazzaranci da kudaden da aka ciwo bashi. Shugaban ya bayyana hakanne a ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga. Inda ya kara da cewa, kudaden da suke ciwo bashi ya zama dole saboda mafi yawanci ayyukan titi da sauran wasu basa cikin kasafin kudi, yace dan haka dole a ciwo bashi. Yace kuma ba Najeriya ce kadai kasar dake ciwo bashi ba, hatta kasashe manya irin su Amurka na ciwo bashi.
Kalli Bidiyon:Yanda Kishin Addinin Musulunci ya sa shahararren dan danbe, Khabib Nurmagomedov yaki gaisawa da mace ‘yar Jarida

Kalli Bidiyon:Yanda Kishin Addinin Musulunci ya sa shahararren dan danbe, Khabib Nurmagomedov yaki gaisawa da mace ‘yar Jarida

Duk Labarai
Shahararren dan Dambe daga kasar Rasha, Khabib Nurmagomedov yaki yadda ya gaisa da mace 'yar jarida bayan data bashi hannu. Lamarin ya farune bayan kammala wasan gasar cin kofin Championships League wanda kungiyar PSG ta lashe. https://twitter.com/AzatAlsalim/status/1929216302746378627?t=_R7lM6v3JBYTXlUgGt-FSA&s=19 Khabib Nurmagomedov ya gaisa da 'yan uwansa maza inda itama 'yar jaridar ta mika masa hannu su gaisa, amma yaki yadda ya bata hannu, daga baya dai ta bashi hakuri. Ya sha Yabo kan lamarin.
Kuma Dai: Jirgin Yakin Sojin Najeriya ya Kàshè ‘yan Bijilante bisa kuskure a jihar Zamfara

Kuma Dai: Jirgin Yakin Sojin Najeriya ya Kàshè ‘yan Bijilante bisa kuskure a jihar Zamfara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, jirgin yakin sojin Najeriya ya kashe 'yan Bijilante bisa kuskure a jihar Zamfara. Shafin Bakatsina ya ruwaito cewa, lamarin ya farune a kauyen Mani dake kamar Hukumar Maru dake jihar. Yace an kashe manoma 50 da yin garkuwa da mutane 20 a ranar da lamarin ya faru bayan harin 'yan Bindiga. Yace jirgin da aka kawo dan ya taimaka a yi maganin 'yan Bindigar sai ya kare da kashe 'yan Banga bisa kuskure. Zuwa yanzu dai Gwamnatin jihar Zamfara da Hukumomin tsaro basu ce uffan ba kan lamarin.
Ka rage yawan cin Bashi>>IMF ta gargadi shugaba Tinubu

Ka rage yawan cin Bashi>>IMF ta gargadi shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kungiyar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta gargadi Najeriya kan ci gaba da ciwo bashi duk da yanda tattalin arzikin kasar ya tabarbare. Hakan na zuwane yayin da Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ke shirin cin bashin da ya kai kusan Dala Biliyan $26. Kungiyar tace kusan kaso 60 na kasafin kudi da gwanatin Tinubu ke dashi da bashi take kokarin aiwatar dashi inda tace hakan ya sabawa Alkawarin Gwamnatin Tinubu din na kaucewa bashi da mayar da hankali wajan jawo masu zuba hannun jari a Najeriya. Kungiyar tace karuwar bashin Najeriya abu ne me hadarin gaske. Sannan tace tana bayar da shawarar a mayar da hankali wajan samun kudi ta cikin gida da fadada hanyoyin kudin shigar Gwamnati ya fi a mayar da hankali wajan yawaita ciwo bashi. Kungiyar tace duk da yawaitar bashin da Najeriya ke c...
A shekaru 2 da ka yi kana mulki, baka tsinana komai ba sai shegiyar karya kawai>>Kungiyar Kare muradun yarbawa ta Afenifere ta caccaki shugaba Tinubu

A shekaru 2 da ka yi kana mulki, baka tsinana komai ba sai shegiyar karya kawai>>Kungiyar Kare muradun yarbawa ta Afenifere ta caccaki shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kungiyar kare muradun Yarbawa ta Afenifere ta caccaki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da cewa a shekaru 2 da yayi yana mulki bai tsinana komai ba sai karyar nasarar da babu ita a zahiri. Kungiyar ta bayyana hakanne ta bakin sakatarenta, Oba Oladipo Olaitan inda tace Alkawuran kawo sauyi da yawa 'yan Najeriya sun juya sun zama bala'i. Kungiyar tace masana'antu sun durkushe, Sai yawan ciwo bashi ga kuma matsanancin Talauci da ake fama dashi a mulkin na Tinubu. Kungiyar ta kuma ce shugaba Tinubu baya bin tsarin doka inda ta zargeshi da son mayar da Najeriya a karkashin tsarin jam'iyya daya. Kungiyar tace sakamakon shekaru biyu da Tinubu yayi akan Mulki sun nuna cewa, dukkan wani bangare a ci gaban rayuwa ya samu ci baya a Najeriya tun bayan da Tinubu ya zama shugaban kasa. Kun...
An soki Tinubu saboda kaddamar da titin Legas zuw Calabar da ba’a kammala ba

An soki Tinubu saboda kaddamar da titin Legas zuw Calabar da ba’a kammala ba

Duk Labarai
Wata kungiyar dake saka ido kan yanda Gwamnati ke gudanar da ayyukanta, NEFGAD ta caccaki Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda kaddamar da wani karamin sashe na titin Legas zuwa Calabar. Kungiyar ta bakin wakilinta, Mr Akingunola Omoniyi tace yaudara ce kawai ace an kaddamar da kaso 4 cikin 100 na aikin wanda gaba dayansa ne ake bukata. Kungiyar tace kamata yayi a mayar da hankali wajan kammala aikin bawai wajan tallatashi ba.
Kuma Dai:Kalli Bidiyon sabuwar wakar Idris Abdulkarim inda ya caccaki APC da INEC

Kuma Dai:Kalli Bidiyon sabuwar wakar Idris Abdulkarim inda ya caccaki APC da INEC

Duk Labarai
Shahararren mawakin Gambara, Idris Abdulkarim wanda yayi wakar Najeriya Jaga-jaga ya sake sakin wata sabuwar Waka. Idris Abdulkarim ya saki wakar ne bayan a wadda ya saki ta farko ta jawo cece-kuce. A wannan sauwar wakar da ya saki, Idris Abdulkarim ya mayar da hankali kan APC da hukumar zabe me zaman kanta, INEC. Saurari sabuwar wakar a kasa: https://twitter.com/TENIBEGILOJU202/status/1929065906451169302?t=bZh9wlVcfMsxxMTgiujL2A&s=19 Idris ya saki wakar ne yayin da ake fuskantar zaben shekarar 2027
Mùtùwàr ‘yan Kwallon Kano, da Mùtùwàr mutane a Ambaliyar ruwan Jihar Naija, Kunki dakar mataki, kun bari mutane na ta mùtùwà>>Atiku Abubakar ya caccaki Gwamnatin Tinubu

Mùtùwàr ‘yan Kwallon Kano, da Mùtùwàr mutane a Ambaliyar ruwan Jihar Naija, Kunki dakar mataki, kun bari mutane na ta mùtùwà>>Atiku Abubakar ya caccaki Gwamnatin Tinubu

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya inda yace basu dauki matakan da ya kamata ba gashi mutane na ta mutuwa. Ya bayyana hakane a sakon ta'aziyya ga iyalan 'yan kwallon Kano 22 da suka rasu a hadarin Mota. Inda yace ba iyalansu kadaine suka yi asararsu ba, hadda ma Najeriya baki daya. Ya kuma bayyana Alhinin rasuwar mutane sama da 100 a ambaliyar ruwan garin Mokwa dake jihar Naira inda yace abin takaici ne. Atiku ya baiwa Gwamnatin tarayya shawarar ta dauki matakan kula da titinan Najeriya dan rage ko kawar da yawaitr hadurra. Sannan ya nemi da a dauki matakan hana ambaliyar ruwa musamman yanzu da ake fuskantar yawaitar ruwan sama.