Saturday, December 20
Shadow
Bidiyo: An yi kuskuren turawa Fasto Naira Miliyan 1 mimakon dubu dari a matsayin sadaka saidai da aka ce ya mayar da kudin, yace Kudin da aka baiwa Yesu sadaka ba’a mayar dasu, me kudin ya kira ‘yansanda

Bidiyo: An yi kuskuren turawa Fasto Naira Miliyan 1 mimakon dubu dari a matsayin sadaka saidai da aka ce ya mayar da kudin, yace Kudin da aka baiwa Yesu sadaka ba’a mayar dasu, me kudin ya kira ‘yansanda

Duk Labarai
Wani kirista da yayi kuskuren aikawa fastonsa Naira Miliyan daya maimakon Naira dubu dari a matsayin kudin sadaka, ya nemi faston ya mayar masa da kudinsa. Saidai Faston yace sam bai yadda da wannan maganar ba, dan kuwa kudin da aka aikawa Yesu ba'a mayar dasu. https://twitter.com/yabaleftonline/status/1929622499706191993?t=XrZ-vhZIvZDOJGk75tvSvA&s=19 Saidai me kudin ya je ya dauko 'yansanda.
Hutun Sallah da jihar Kano ta baiwa Makarantu yayi yawa, Inji ‘yan Kudancin Najeriya yayin da suke caccakar gwamnatin jihar suna cewa dama ‘yan Arewa basu san muhimmancin ilimi ba

Hutun Sallah da jihar Kano ta baiwa Makarantu yayi yawa, Inji ‘yan Kudancin Najeriya yayin da suke caccakar gwamnatin jihar suna cewa dama ‘yan Arewa basu san muhimmancin ilimi ba

Duk Labarai
''Yan kudancin Najeriya da yawa ne suke caccakar Gwamnatin jihar Kano bayan da ta ayyana kusan sati biyu a matsayin hutun sallah. Gwamnatin jihar Kano ta sanar kwanaki 12 a matsayin hutun Sallah Babbah ga makarantu. A arewa wannan ba sabon abu bane musamman lura da yanda ake dadewa a Kano ana bukukuwan sallah da ziyarar 'yan uwa. Saidai 'yan Kudun a kafafen sada zumunta sun ta caccakar gwamnatin jihar Kanon suna dariya akai.
A karshe dai Bidiyo tsìràicì na Muneerat Abdulsalam ya bayyana

A karshe dai Bidiyo tsìràicì na Muneerat Abdulsalam ya bayyana

Duk Labarai
Bidiyon tsiraici na tauraruwar kafafen sada zumunta Muneerat Abdulsalam ya bayyana. Muneerat Abdulsalam ta yi suna wajan sayar da kayan mata da kuma baiwa matan aure shawarar rike miji. Saidai a kwanan baya an ganta cikin wani yanayi mara kyau inda take cewa Rayuwace ta juya mata. Saidai a yanzu kuma Bidiyon tsiraicinta ne ya bayyana. Saidai kasancewar munin Bidiyon da tsiraicin da yayi yawa a cikinsa, ba zamu iya wallafa muku shi ba.
Sarki Sanusi ya umarci hakimai da su shigo cikin Kano domin hawan Babbar Sallah

Sarki Sanusi ya umarci hakimai da su shigo cikin Kano domin hawan Babbar Sallah

Duk Labarai
Sarki Sanusi ya umarci hakimai da su shigo cikin Kano domin hawan Babbar Sallah. Majalisar Masarautar Kano ta fitar da wata takarda mai dauke da umarni ga dukkan Hakimai da 'Yan Majalisa na masarautar da su hallara a Birnin Kano domin halartar bikin hawan Babbar Sallah da za a gudanar cikin makon gobe. A wata takardar sanarwa da Sakataren Majalisar Masarautar Kano, Alhaji Abba Yusuf Danmakwayon Kano ya rattabawa hannu, an bukaci Hakimai da sauran shugabannin gargajiya da su iso Kano tare da dawakan su da mahayan su a ranar Laraba, 8 ga Dhul Hijjah, 1446 Hijira, wanda ya yi daidai da 4 ga Yuni, 2025. Bayan haka, ana sa ran za su halarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Alhamis, 9 ga Dhul Hijjah, wato 5 ga Yuni, 2025 da misalin karfe 11:00 na safe, domin karbar umarni da ba...
Sauyin yanayi da rashin bin ƙa’idar gini ne suka haddasa ambaliyar Mokwa – Gwamnatin Najeriya

Sauyin yanayi da rashin bin ƙa’idar gini ne suka haddasa ambaliyar Mokwa – Gwamnatin Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ce sauyin yanayi da rashin bin ƙa'idar gine-gine da rashin gyara magunan ruwa ne suka haddasa mummunar ambaliyar da ta auku a garin Mokwa na jihar Neja. Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na ƙasar, Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana haka a Abuja babban birnin ƙasar, yayin da yake bayani kan ambaliyar da auka wa garin Mokwa na jihar Neja. Ministan ya ce ba ɓallewar madatwar ruwa ba ce ta haifar da ambaliyar, yana mai alaƙanta matsalar da ƙaruwar tasirin sauyin yanayi, da kuma ruwan sama da ya wuce kima. Ya ƙara da ce tawagar ƙwararru daga ma'aikatarsa da kuma sauran hukumomi na garin domin auna irin ɓarnar da lamarin ya haifar. Mista Utsev ya buƙaci gwamnatocin jihohi da masu ruwa da tsaki su riƙa la'akari da gargaɗin da hukumomi ke fitarwa tare da...
Ƴansandan sun hana hawan sallah a Kano

Ƴansandan sun hana hawan sallah a Kano

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan jihar Kano tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro a jihar sun ɗauki matakin haramta bukukuwan hawan salla a Kano. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya ce hukumomin tsaron sun ɗauki matakin ne sakamakon dalilai na tsaro. Matakin na zuwa ne bayan da wata takarda da aka yi amanna daga fadar Sarki Muhammadu Sanusi II ta fito, ta yi kira da hakimai da su shiga birnin Kano domin gudanar da bukukuwan hawan Sallah. Ko a lokacin bukukuwan ƙaramar sallah ma hukumomin tsaron jihar sun haramta hawan sallah, saboda bayanan sirrin da suka ce sun samu na wasu ''ɓata-gari'' da ke son amfani da bukukuwan hawan sallar wajen tayar da zauen tsaye a jihar. ''Kan haka ne hukumomin tsaron suka sake ɗaukar matakan haramta...
Gwamna Abba Kabir Ya Bada Gudummuwar Naira Miliyan Biyar Ga Farfesan Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Dake Sokoto Da Ake Nema Wa Taimako Rashin Lafiya

Gwamna Abba Kabir Ya Bada Gudummuwar Naira Miliyan Biyar Ga Farfesan Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Dake Sokoto Da Ake Nema Wa Taimako Rashin Lafiya

Duk Labarai
Gwamna Abba Kabir Ya Bada Gudummuwar Naira Miliyan Biyar Ga Farfesan Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Dake Sokoto Da Ake Nema Wa Taimako Rashin Lafiya Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf Ya Baiwa Farfesa Abubakar Roko Na Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Dake Sokoto Gudummuwar Naira Miliyan Biyar Dake Fama Da Jinya, Domin Zuwa Neman Lafiya A Kasashen Waje. Allah Ya Ba Shi Lafiya Ya Kuma Saka Wa Gwamna Abba Kabir Yusuf Da Alheri! Daga Jamilu Dabawa
Ya kamata Najeriya ta gina katanga a kan iyakokinta>>Inji Shugaban Sojojin Najeriya, Christopher Musa

Ya kamata Najeriya ta gina katanga a kan iyakokinta>>Inji Shugaban Sojojin Najeriya, Christopher Musa

Duk Labarai
Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya nuna buƙatar gina katanga a ilahirin iyakokin ƙasar da maƙwaftanta domin kare kwararar masu ɗauke da makami zuwa cikinta. Yanzu haka dakarun sojin Najeriya na fafutikar ganin sun yaƙi matsalar tsaro da ke addabar ƙasar, musamman rikicin Boko Haram da ƙasar ta kwashe shekara 16 tana fama da shi a arewa maso gabas. Mayaƙan ƙungiyar - wadda ta samo asali daga kungiyar IS reshen yammacin Afirka - sun kashe jami'an tsaro da dubban fararen hula, yayin da rikicin ya tagayyara miliyoyi. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato Janar Christopher Musa a wani taron tsaro da ke gudana a Abuja yau Talata a Abuja na cewa "kula da kan iyakoki abu ne mai muhimmanci," inda ya bayar da misali da iyakar ƙasar Pakistan mai katangar da ke ...
Da gangan wasu mugayen ‘yan Najeriya ke kara farashin kaya dan kawai su bata min suna>>Gwamnatin Tinubu

Da gangan wasu mugayen ‘yan Najeriya ke kara farashin kaya dan kawai su bata min suna>>Gwamnatin Tinubu

Duk Labarai
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa da gangan wasu 'yan Najeriyar ke karawa kayan da suke sayarwa farashi dan kawai su batawa gwamnatinsa suna. Hadimin shugaban kasar me bashi shawara akan tattalin arziki, Tope Fasua ne ya bayyana hakan. Yace banda alkaluma tattalin arziki, akwai sauran abubuwan da ke sanya farashin kayan masarufi su tashi a Najeriya, hadda muguntar wasu 'yan kasar. Ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook yayin da yake martani ga wani rahoto dake cewa wani gidan mai yana biyan ma'aikatansa Naira Dubu 10.