ABIN MAMAKI: Ji yanda ake zargin ‘Yan Ķasar Indiýa Sùn Ķori ‘Ýan Nijeriya Daga Nìjeriya
ABIN MAMAKI: 'Yan Ķasar Indiýa Sùn Ķori 'Ýan Nijeriya Daga Nìjeriya.
Ɗan jarida Nasiru Zango ya rubuta yana mai cewa wannan hoto da kuke gani dake nuna wasu matasa biyu da 'yan sandan Nijeriya ke neman su ruwa a jallo ba kayan kowa suka sata ba kuma ba su yiwa kowa komai ba, babban laifin su bai wuce kasancewar su jajirtattun matasa masu neman abin kan su ba ta hanyar da dokar Nijeriya ta tanada, sai kuma watakila dan sun kasance masu karamin karfi da suka ki yadda wani babban kamfani ya zo har kasar su yana kokarin murkushe su ba.
Fiye da shekara kenan wani babban kamfani na 'yan asalin Indiya ya yi karar wadannan matasa wadanda sune suke da mallakin kamfanin ganyen shayin Y and Z kan cewar sun satar musu samfurin ganyen shayin su (kamar yadda Coca Cola suka taba yin karar Pop C...








