Allah Sarki: Karanta Jadawalin Manyan Sojojin da suka rhasa Rhayuwkansu a Fagen daga
A ranar Talata ne rahotonni suka fara ɓulla cewa mayaƙan ƙungiyar Islamic State of West Africa Province (Iswap) ta kashe Birgediya Janar Musa Uba a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kisan nasa ya tayar da muhawara game da yadda ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da Iswap ke kashe manyan jami'an sojin Najeriya, duk da cewa ba shi ne na farko da ya mutu a filin daga ba.
Bayanai sun nuna cewa Janar Uba ne babban jami'i na biyu mafi girman muƙami da 'yanbindigar suka kashe tun shekarar 2021.
Iswap ta bayar da sanarwar kisansa a shafinta na Telegram, inda ta ce mayaƙanta sun kama shi ranar 15 ga watan Nuwamba bayan harin kwanton-ɓauna da suka kai wa sojojin Najeriya a kusa da garin Wajiroko da ke jihar ta Borno.
Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da kai h...








