Monday, December 22
Shadow
Jihar Ekiti ta Haramta Shan Tàbà

Jihar Ekiti ta Haramta Shan Tàbà

Duk Labarai
Jihar Ekiti, ta haramta shan Taba a babban birnin jihar, Ado Ekiti. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Felani Oyebanji ne ya bayyana hakan a wajan zagayowar ranar yaki da shan taba ta Duniya a birnin Ado Ekiti. Yace illar da taba kewa lafiyar dan adam ce tasa suka dauki wannan mataki. A wani labari me kama da wannan ma, kasar Faransa ma na shirin haramta shan taba sigari.
Da Duminsa: Mutane 9 sun mùtù bayan fashewar Bam a wata tashar mota dake jihar Borno

Da Duminsa: Mutane 9 sun mùtù bayan fashewar Bam a wata tashar mota dake jihar Borno

Duk Labarai
Rahotannin da hutudole ke samu na cewa a kalla mutane 9 ne suka mutu wasu suka jikkata bayan fashewar bam a tashar motar dake Maimalari a karamar hukumar Guzamala dake jihar Borno. Rahoton yace an dasa bam dinne a tashar motar wnda daga baya ya tashi. Lamarin ya farune da misalin karfe 11 a.m. na safiyar ranar Asabar. Jaridar Punchng ta ruwaito kakakin majalisar jihar Borno, Hon. Abdulkarim Lawan ya tabbatar mata da faruwar lamarin. Ya mika ta'aziyya ga iyalan mamatan inda yayi fatan samun sauki ga wadanda ke kwance a Asibiti. Ya koka da yawaitar hare-haren kungiyoyi masu ikirarin Jìhàdì.
Murnar cin kofin Championships League din PSG yasa mutane 2 sun mùtù dan sanda daya na can rai kwakwai mutu kwakwai a birnin Paris na kasar Faransa, an yi kòne-kòne da sace-sace

Murnar cin kofin Championships League din PSG yasa mutane 2 sun mùtù dan sanda daya na can rai kwakwai mutu kwakwai a birnin Paris na kasar Faransa, an yi kòne-kòne da sace-sace

Duk Labarai
Rahotanni daga birnin Paris na kasar Faransa na cewa an yi kone'kone da sace sace da lalata dukiya a yayin da ake murnar cin kofin Championships League da kungiyar PSG ta yi. Rahotannin sun kuma ce an kashe mutane 2 yayin murnar sannan an kama sama da 500 da suka aikata laifuka. https://twitter.com/Megatron_ron/status/1928945703352410317?t=2ftRc57m_y3NgxI415Ud6g&s=19 Hakanan rahoton yace dansanda daya na can rai kwakwai mutu kwakwai saboda lamarin. https://twitter.com/MegaGeopolitics/status/1929118696674361514?t=aMRoiiBdqoj7G4li9UZaXQ&s=19 'Yansanda sun fito da barkonon tsohuwa dan magance wannan matsala ta hatsaniya data kaure.
Gaba da gaba na faɗa wa Tinubu ba zan goya masa baya ba – Amaechi

Gaba da gaba na faɗa wa Tinubu ba zan goya masa baya ba – Amaechi

Duk Labarai
Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce tun farkon fara gangamin yaƙin neman zaɓen 2023 ne ya yanke shawarar ba zai zaɓi Shugaba Bola Tinubu ba, inda ya ce sun haɗu gaba da gaba, kuma ya faɗa a take cewa shi ba zai zaɓe shi ba. Amaechi ya ce hakan ya sa ya cika alƙawarin da ya ɗaukar wa kansa na ƙin taimakon yaƙin zaɓen Tinubu, saboda a cewarsa ya gano tun da wuri cewa aikin zai yi wa shugaban nauyi na mulkin Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Amaechi ya bayyana haka ne a wajen taron murnar cikarsa shekara 60 a duniya wanda aka yi jiya Asabar a Abuja. "A Yola muka haɗu da Tinubu, inda na faɗa masa cewa ni ba zan goya masa baya ba. Kuma ban yi ba, kuma ban zaɓe shi ba. Magana ce ta tunanin ba zai iya ba. "Wasu daga cikinmu da suke na...
Kusan mutane 400 ne suka ɓace a ambaliyar Mokwa – Gwamnatin Neja

Kusan mutane 400 ne suka ɓace a ambaliyar Mokwa – Gwamnatin Neja

Duk Labarai
A Najeriya, ana ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar ruwan da ta auku a garin Mokawa na jihar Neja, inda ya zuwa yanzu aka gano sama da gawa 150, kuma akwai sauran fiye da 400 da ake nema, yayin da gwamnatin jihar Neja da hukumomi da kungiyoyin agaji ke ci gaba da kai dauki ga daruruwan mutane da ambaliyar ruwan ta shafa. Kwamared Yakubu Garba, mataimakin gwamnan jihar Nejar, wanda ya kai ziyarar gani da ido da kuma jaje garin na Mokwa ne ya bayyana wa BBC hakan, inda ya ce lamarin akwai ɗaga hankali. Ya ce, "Aƙalla akwai mutum 40 ba suka ɓace har yanzu ba a gansu ba kuma ba a gano gawarsu ba. Ana dai cigaba da nemansu."
An bayyana abinda ke ta’azara matsalar tsàrò a Najeriya

An bayyana abinda ke ta’azara matsalar tsàrò a Najeriya

Duk Labarai
A Najeriya masana lamuran tsaro na ci gaba da bayyana albarkacin baki kan samun jami'an tsaro da suke safarar makamai ga ƴanbindiga. Masana suna cewa rashin ɗaukar matakan hukunta jami’an tsaron da aka samu da laifin safarar makamai ga ƴanbindiga, da kuma biyan jami’an tsaron ƙasar albashin da bai taka kara ya karya ba, na daga cikin abubuwan da ke taka rawa wajen ci gaba da samun karuwar wasu baragurbin jami’an tsaron da ke safarar makamai ga mayaƙan Boko Haram da ‘yan fashin daji. Barista Audu Bulama Bukarti, lauya kuma masani lamuran tsaro ne a nahiyar Afirka, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Najeriya na sakaci da lamuran da suka shafi tsaro da suka haɗa da rashin bibiyar yadda ake kashe kuɗaɗe a ɓangaren da ma yin biris da makomar sojoji da sauran masu aikin samar da tsaro a kasar...
An kama wasu dake amfani da lokacin aikin Hajji suna kai Miyagun Kwàyòyì kasar Saudiyya

An kama wasu dake amfani da lokacin aikin Hajji suna kai Miyagun Kwàyòyì kasar Saudiyya

Duk Labarai
Hukumar hana sha da fataucin Miyagun Kwàyòyì ta NDLEA ta sanar da kama wasu dake amfani da lokacin aikin Hajji suna safarar miyagun Kwàyòyì zuwa kasar Saudiyya. Hakanan, Rahoton yace kuma suna daukar nauyin mutane zuwa kasar Saudiyyar kawai dan su yi musu safarar kwaya. Kakakin NDLEA, Femi Babafemine ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi inda yace sun yi nasarar kama shugaban wannan muguwar harkar a Kano. Yace wadanda aka kama din sune Abubakar Muhammad, Abdulhakeem Muhammed Tijjani, da Muhammad Aji Shugaba. Yace an kamasu ne ranar 27 da 28 ga watan Mayu.
Tinubu ya miƙa ta’aziyya kan rasuwar ƴan wasan Kano da su ka yi haɗari

Tinubu ya miƙa ta’aziyya kan rasuwar ƴan wasan Kano da su ka yi haɗari

Duk Labarai
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhini da jimami da alhini bisa rashe-rashen da suka faru a jihohin Kano da Neja, yana mai bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya. A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya nuna matuƙar kaɗuwa kan hatsarin mota da ya rutsa da ‘yan wasan Jihar Kano a hanyarsu ta dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala a Jihar Ogun. Shugaban Ƙasa ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasa rayukansu a cikin hatsarin, ya kuma roƙi Allah ya bai wa iyalansu da daukacin al’ummar Kano haƙuri da juriya. Ya ce hanya mafi inganci ta girmama su ita ce ɗaukar matakan kariya domin rage aukuwar irin wannan ibtila’i a gaba. Baya ga haka, Tinubu ya bayyana alhini...