ADC ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman karɓuwa ba ji ba>>Shugaba Tinubu
Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da martani kan zargin da jam’iyyar haɗaka ta ADC ta yi na cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na amfani da rasuwar tsohon shugaba Muhammadu Buhari, don samun tagomashi na siyasa da neman karɓuwa a idon jama'a.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya bayyana zargin na ADC a matsayin “abin kunya,” inda ya ce jam’iyyar ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman suna.
ADC dai ta ce gwamnatin Tinubu ta yi amfani da yadda aka gudanar da jana’izar Buhari da kuma yadda aka shirya bikin bankwana da shi a Daura da ke jihar Katsina, domin ƙara samun ƙarbuwa a idon ƴan ƙasa.
Fadar shugaban ƙasar ta ce marigayi Muhammadu Buhari ya cancanci yi masa jana'izar ban-girma kuma sun yi haka ne don girmamawa saboda hakan ne ya dace da sh...








