Monday, December 15
Shadow
“Babu ƙanshin gaskiya a cewar da ake yi ƴan ta’adda na da makaman da su ka fi na jami’an tsaron Nijeriya” Inji Ministan Tsaron Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar.

“Babu ƙanshin gaskiya a cewar da ake yi ƴan ta’adda na da makaman da su ka fi na jami’an tsaron Nijeriya” Inji Ministan Tsaron Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar.

Duk Labarai
“ Babu ƙanshin gaskiya a cewar da ake yi ƴan ta'adda na da makaman da su ka fi na jami'an tsaron Nijeriya” Inji Ministan Tsaron Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar. A Cikin Shekaru Biyu Na Gwamnatin Tinubu An Sami Cìkakken Tsaro Akan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna, Wanda A Baya Ya Taɓa Kasancewa Tungar Masu Ģarkuwa Da Mutane, Inji Ministan Tsaro, Badaru "Daga watan Mayun 2023 zuwa yanzu mun yi nasarar murƙushe ƴan ta'adda har 13,000, kazalika an kawar da shugabannin Boko Haram sama da 300 "A Maiduguri, a baya da an ce Gambaru, Bama, ka san an ambaci hanya mai hatsarin gaske, amma a yanzu hakan ya zama tarihi, duk wannan ya faru ne a cikin shekaru 2 na wannan gwamnatin". Sojojin Nijeriya Sun Cancanci Lambar Yabo Fiye Da Wanda Ake Yi Musu A Yanzu, Duba Da Yadda Suke Yin Nasara Àka...
Da Duminsa: Shugaban Sojojin Najeriya ya koma da zama jihar Borno dan magance matsalar tsaro

Da Duminsa: Shugaban Sojojin Najeriya ya koma da zama jihar Borno dan magance matsalar tsaro

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban sojojin Najeriya, General OO Oluyede ya koma jihar Borno da zama dan kula da yanda sojoji ke aikin magance matsalar tsaro. A 'yan Kwanakinnan dai Hare-haren kungiyar Bòkò Hàràm sun yawaita inda aka gansu da makamai na zamani. Majalisar tarayya ma ta bayyana cewa, 'Yan Bòkò Hàràm din sun fi sojojin Najeriya makamai masu kyau. Wasu na ganin komawar shugaban sojojin zuwa jihar Borno zai taimaka matuka wajan magance matsalar tsaron jihar da makwabciyarta Yobe.
A hukumance Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar mazaɓar Kano ta Kudu ya koma jam’iyyar APC daga NNPP bayan Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Godswill Akpabio ya karanta wasiƙar sauya sheƙarsa a yayin zaman majalisar na yau Laraba

DAGA ZAUREN MAJALISA : Sanata Kawu Sumaila (Kano ta Kudu) ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC a zaman majalisar dattawa na yau. Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar sauya shekar tasa. Inside Bauchi State07-05-2025
Ina gama Wa’adina na Mulki zan koma sana’ar da nake yi kamin in zama Gwamna watau Walda>>Inji Gwamnan jihar Nasarawa

Ina gama Wa’adina na Mulki zan koma sana’ar da nake yi kamin in zama Gwamna watau Walda>>Inji Gwamnan jihar Nasarawa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi karin haske kan sana’ar da zai fara bayan ya kammala wa’adin mulkinsa zango na biyu. Gwamna Sule yace zai koma sana’ar da ya fara yi tun kafin fara mulkin jihar Nasarawa wato sana,ar walda, da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2027. Yace akwai alkairi a cikin Sana’ar ta walda sosai ,Inda ya nemi matasa da su dage da Sana’a Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tattaunawa da hukumar samar da wutar lantarki ta karkara ta shirya tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Nasarawa. Ya kuma yi amfani da damar wajen tabbatarwa da masu sha’awar zuba jari cewa jihar Nasarawa na da ƙwararrun ma’aikata, inda ya nuna cewa jihar na da ɗimbin matasa masu horo da shaidar ƙwarewa da za su iya tallafawa mas...
‘Yan Najeriya na Daf da yi maka Bore irin wanda ba’a taba ganin irinsa ba muddin baka dauki mataki akan lokaci ba>>’Yan majalisar Wakilai suka shafawa fuskarsu toka suka gayawa shugaba Tinubu Gaskiya

'Yan majakisar Wakilai musamman wadanda suka fito daga jihohin da matsalar tsaro ta yi kamari sun gayawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauki mataki akan lokaci ko kuma mutane na Daf da giwa Gwamnatin sa Bore. 'Yan majalisar sun bayyana takaici kan kasa magance marsalar tsaro a kasar nan duk da kashe makudan kudaden da suka kai Naira Tiriliyan 19.7 akan tsaron a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019. An fara tattaunawar ne biyo bayan korafin harin da aka kai kan Giwa Barak a jihar ta Borno da kuma kashe-kashen da ake yi a Jihohin Borno da Yobe. Dan majalisa, Ahmed Satomi ya fara yin maganar a zaman majalisar inda sauran 'yan majalisar da yawa suka nuna damuwa sa alhini. Kakakin majalisar, Godswill Akpabio yace ya kamata a bar maganar siyasa a dakatar da wannan matsalar tsarom
Kwamishina ya mayar da Naira miliyan 301 ragowar kuɗin ciyarwar azumi a Jigawa

Kwamishina ya mayar da Naira miliyan 301 ragowar kuɗin ciyarwar azumi a Jigawa

Duk Labarai
Kwamishina ya mayar da Naira miliyan 301 ragowar kuɗin ciyarwar azumi a Jigawa. Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Auwalu Danladi Sankara, ya mayarwa baitul malin jihar Naira miliyan 301 da su ka yi ragowa bayan kammala shirin ciyarwa na watan Ramadan bana. Sankara ya sanar da mayar da kudaden ne a yayin taron majalisar zartarwa na jiha wanda gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranta. Kudin sun yi ragowa ne biyo bayan ware naira biliyan 4.8 da gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa ma’aikatar don shirin ciyar da abinci, wanda ya kunshi dukkanin kananan hukumomi 27 da kuma cibiyoyi kusan 700 na ciyarwa. An ba da rahoton cewa, shirin wanda wani kwamiti ya jagoranta, ya ciyar da mutane sama da 5,550 a kullum a tsawon kwanaki 29 na azumi. Majalisar zartaswar jihar ta yaba ...
Ji yanda Karamin yaro dan shekaru 18 ya dirkawa ‘yan mata 10 ciki a cikin watanni 5,  An kaiwa Kwamishiniyar mata ta jiharsa Korafin yaron tace lamarin yafi karfinta

Ji yanda Karamin yaro dan shekaru 18 ya dirkawa ‘yan mata 10 ciki a cikin watanni 5, An kaiwa Kwamishiniyar mata ta jiharsa Korafin yaron tace lamarin yafi karfinta

Duk Labarai
Wani matashi dan shekaru 18 ya dirkawa mata 10 ciki a cikin watanni 5. Yaron an kaishi wajan wani dan kasuwane dan ya koya masa kasuwanci daga kauyensu a jihar Anambra, saidai watanni 3 da kaishi wajan me gidan nasa ya dirkawa diyar me gidan ciki sannan ya dirkawa dayar yarinyar shagon me gidan ciki itama. Dalilin hakane me gidan ya tattara mai kayansa ya koreshi ya mayar dashi kauye. Saidai watanni biyu bayan komawarsa kauyen, a camma ya dirkawa 'yan mata 8 ciki. Mahaifiyarsa ce da kanta ta kaiwa kwamishiniyar mata da walwala ta jihar, Ify Obinabo korafi inda tace dan nata ya zamar mata annoba da ta ganshi da mace sai ta ji gabanta na faduwa. Kwamishiniyar matar tace ta sa yaron a gaba inda ta tambayeshi ko akwai wani magani da yake amfani dashi ne wajan yaudarar mata k...