Saturday, December 13
Shadow
Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Miliyan 670 Don Siyan Motoci Ga Sunusi Lamido Sanusi, Duk Da Kalubalen Da Al’umma Ke Fuskanta

Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Miliyan 670 Don Siyan Motoci Ga Sunusi Lamido Sanusi, Duk Da Kalubalen Da Al’umma Ke Fuskanta

Duk Labarai
Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Miliyan 670 Don Siyan Motoci Ga Sunusi Lamido Sanusi, Duk Da Kalubalen Da Al’umma Ke Fuskanta. A wani lamari da ke kara daukar hankalin jama’a, gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware zunzurutun kudi har Naira ₦670,000,000 don sayen motoci na alfarma ga tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi. Bincike ya nuna cewa kudaden za su fito ne daga asusun jihar Kano da kananan hukumomi 44, inda kowace karamar hukuma za ta bayar da ₦15,227,272 domin cika adadin kudin. Wannan bayani yana kunshe ne a cikin wata takarda mai lamba MLG/SNSNTLGD/166T/6 da aka fitar ranar 25 ga Maris, 2025. Kamfanin da aka ba kwangilar siyan motocin shi ne Sottom. Wannan yunkuri na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar Kano ke fuskantar manyan ma...
Kalli Zafafan hotunan da baku gani ba na Ango Mawaki Dauda Kahutu Rarara tare da Amaryarsa A’isha Humaira

Kalli Zafafan hotunan da baku gani ba na Ango Mawaki Dauda Kahutu Rarara tare da Amaryarsa A’isha Humaira

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Zafafan hotunan da baku gani ba na Ango Mawaki Dauda Kahutu Rarara tare da Amaryarsa A'isha Humaira.
Kalli Bidiyon wani matashi daga jihar Katsina na fadin cewa, bai taba samun farin ciki irin na gwamnatin Tinubu ba, Yace da mata daya gareshi yanzu ya kara, hakanan kasuwarsa ta habaka kuma matsalar ‘yan Bìndìgà ta gushe a karamar hukumarsa ta Jibia

Kalli Bidiyon wani matashi daga jihar Katsina na fadin cewa, bai taba samun farin ciki irin na gwamnatin Tinubu ba, Yace da mata daya gareshi yanzu ya kara, hakanan kasuwarsa ta habaka kuma matsalar ‘yan Bìndìgà ta gushe a karamar hukumarsa ta Jibia

Duk Labarai
Wani matashi ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta bayan da yayi ikirarin cewa bai taba samun farin ciki kamar a zamanin mulkin Tinubu ba. Yace da mata daya gareshi, amma yanzu ya kara aure, hakanan sannan kuma kasuwarsa ta kara habaka. Yace a karamar hukumar Jibia yake zasu tafi gida aka ce su bari sai da magariba, alamar cewa tsaro ya samu. https://twitter.com/Realoilsheikh/status/1919463062735577586?t=91zXI0pWCdlgjk8cTFNrcQ&s=19
Najeriya ce kasa ta daya a Afrika sannan ta 2 a Duniya wajan yawan yaran da basu samun abinci me gina jiki>>Inji UNICEF

Najeriya ce kasa ta daya a Afrika sannan ta 2 a Duniya wajan yawan yaran da basu samun abinci me gina jiki>>Inji UNICEF

Duk Labarai
Najeriya ce kasa ta daya a Afrika sannan ta Biyu a Duniya wajan yawan yaran da basa samun Abinci me gina jiki kamar yanda hukumar kula da yara ta majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana. Wakiliyar UNICEF, Nemat Hajeebhoy ce ta bayyana hakan a wajan shirin magance matsalar rashin abinci me gina jiki da ake shiryawa yaran jihohin Adamawa, Borno, da Yobe. Tace akwai yara guda 600,000 dake fama da matsalar rashin abinci me gina jiki kuma kusan rabinsu na fuskantar kara tsanantar matsalar. Tace yaran dake fama da matsalar matsananciyar rashin abinci me gina jiki zasu iya mutuwa.
Shugaba Tinubu ya haramta sayo kayan da ake iyayi a cikin gida daga kasashen waje

Shugaba Tinubu ya haramta sayo kayan da ake iyayi a cikin gida daga kasashen waje

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a kokarin karfafa tattalin arzikin Najeriya ya hana sayo kayan da ake iya yinsu a cikin gida daga kasashen waje. Majalisar zartaswa tuni ta amince da wannan kudirin a zamanta na ranar Litinin inda aka bayyana cewa an yi hakanne dan karfafa masana'antun gida Najeriya. Da yake magana ga manema labarai bayan zaman, ministan yada labarai, Mohammed Idris yace an dauki wannan mataki ne dan karfafa amfani da kayan da aka kerasu a cikin gida. Yace sun kwaimwayi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ne a kokarin da yake na karfafa masana'antun kasarsa ta Amirka
Ana ta caccakar wani ɗansanda saboda ya ɗaura wa Ganduje takalmi

Ana ta caccakar wani ɗansanda saboda ya ɗaura wa Ganduje takalmi

Duk Labarai
Ana ta caccakar wani ɗansanda saboda ya ɗaura wa Ganduje takalmi. Wani ɗansanda na shan matsin lamba a kafafen sada zumunta bayan da aka gan shi ya na ɗaura wa Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC mai mulki, igiyar takalmi. A cikin wani bidiyo da ya karade intanet, an ga Ganduje tsaye yayin da dansandan da ba a bayyana sunansa ba ya durƙusa ya na ɗaura masa igiyar takalmi. Bidiyon da ya bayyana a yanar gizo ranar Litinin ya janyo ce-ce-ku-ce daga jama’a. Wasu sun yi mamakin yadda dan sanda da ke cikin kayan aiki zai aikata irin wannan abu, yayin da wasu kuma suka ce wata kila Ganduje ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar dan sandan.