Saturday, December 13
Shadow
Shugaba Tinubu ya bar Katsina bayan ziyarar Kwanaki biyu

Shugaba Tinubu ya bar Katsina bayan ziyarar Kwanaki biyu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Katsina bayan kammala ziyarar kwanki biyu da ya je jihar. D misalin karfe 3 na yammacin ranar Asabar ne jirgin shugaban kasar ya bar filin jirgin sama na Umar Musa 'Yaradua dake jihar. Shugaba Tinubu a yayjn ziyararsa a jihar Katsina ya ziyarci sojoji inda ya karfafa musu gwiwa sannan ya kaddamar da wasu ayyuka biyu na titi da wata cibiyar ayyukan noma da gwamnatin jihar ta gina. A yau Asabar kuma shugaba Tinubu ya halarci daurin auren diyar gwamnan jihar Dikko Radda kamin barin Katsina.
‘Yan Bìndìgà sun kai hari wani sansanin sojojin Najeriya dake jihar Zàmfara inda suka kori sojojin suka konashi, sojojin sun koka da rashin makamai

‘Yan Bìndìgà sun kai hari wani sansanin sojojin Najeriya dake jihar Zàmfara inda suka kori sojojin suka konashi, sojojin sun koka da rashin makamai

Duk Labarai
Rahoto daga jihar Zamfara na cewa, 'yan Bindiga sun kai wani mummunan hari akan wani sansanin sojojin Najeriya dake Jangebe inda suka koneshi. Sun kai harinne da misalin karfe 3 na daren ranar Asabar. A garin Jangebe ne dai 'yan Bindigar suka taba sace 'yan mata daliban makaranta dake da shekaru tsakanin 10 zuwa 17 a ranar 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2021. Harin ya farune a makarantar kwana ta mata me suna Government Girls Science Secondary School. Majiyar tace sojojin basu da kayan aiki kuma ta kara da cewa soja daya ya jikkata kuma an garzaya dashi Asibiti.
‘Yan Bindiga sun kàshè shahararren malamin Addinin Islama a jihar Katsina bayan sun yi garkuwa dashi

‘Yan Bindiga sun kàshè shahararren malamin Addinin Islama a jihar Katsina bayan sun yi garkuwa dashi

Duk Labarai
'Yan Bìndìgà a jihar Katsina sun kashe wani babban malamin Addinin Islama me suna Sheikh Mustapha Aliyu Unguwar Mai Kawo. 'Yan Bindigar dai sun yi garkuwa dashi inda suka ajiyeshi a wajensu na tsawon sati 3. Malamin shine shugaban kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam ta karamar hukumar Kankara. Kuma an yi garkuwa dashi ne a garinsu na Unguwar Mai Kawo wanda hakan ke kara bayyana matsalar tsaron da ake fama da ita. Bakatsinene ya bayyana rasuwar tasa da yammacin Ranar Juma'a.
Ke Uwace, Ki yi hakuri da rashin Kunyar da matan jihar mu suka miki, daukar nauyinsu aka yi>>Wike ya baiwa matar shugaban kasa, Remi Tinubu hakuri bayan matan jihar Rivers sun tashi sun fice daga dakin taro yayin da take jawabi

Ke Uwace, Ki yi hakuri da rashin Kunyar da matan jihar mu suka miki, daukar nauyinsu aka yi>>Wike ya baiwa matar shugaban kasa, Remi Tinubu hakuri bayan matan jihar Rivers sun tashi sun fice daga dakin taro yayin da take jawabi

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya baiwa matar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu watau Remi Tinubu hakuri kan abinda matan jihar Rivers suka mata. A jiya Juma'a ne dai hutudole ya kawo muku rahoton cewa, matan jihar ta Rivers ana tsaka da taro sun tashi sun tafi yayin da matar shugaban kasar ke tsaka da jawabi inda suka ce basa son saurarenta. Wike ta bakin kakakinsa, Lere Olayinka ya bayyana cewa wannan abin kunyane kuma daukar nauyin matan aka yi. Yace wanda ke cewa yana neman sulhu ne wai yake irin wannan abin inda yace ba da gaske yake ba. Wike yace a madadin al'ummar jihar Rivers kuma a matsayinsa na dattijo daga jihar Rivers yana baiwa matar shugaban kasar Hakuri.
Manyan Malaman Najeriya, Sheikh Daurawa, Bin Uthman, da Gidado Triumph sun roki Allah yasa kada gobarar kasar Israyla ta mutu

Manyan Malaman Najeriya, Sheikh Daurawa, Bin Uthman, da Gidado Triumph sun roki Allah yasa kada gobarar kasar Israyla ta mutu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} A yayin da annobar gobarar daji ta Dumfari kasar Israyla mutane nata bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. Manyan Malam Arewacin Najeriya ma ba'a barsu a baya ba. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1918519721491570788?t=2-0V3cJ7oi64ly1SW_1BFQ&s=19 Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Sheikh Muhammad Bin Uthman, da Sheikh Abdulmudalib Gidado Triumph duk sun yi fatan Allah yasa kada wutar ta mutu. https://twitter.com/el_uthmaan/status/1918520226720678252?t=qq6f5cmVzbYaH0q3Ow...
Katsinawa sun nishadantar dani sosai, ji na yi kamar a garin mu nake>>Shugaban kasa, Bola Ahmad

Katsinawa sun nishadantar dani sosai, ji na yi kamar a garin mu nake>>Shugaban kasa, Bola Ahmad

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Katsinawa sun Nishadantar dashi sosai a ziyarar da ya kai jihar. Tinubu ya bayyana hakane bayan da mawaka ciki hadda Rarara suka wakeshi da yaren Yarbanci. https://twitter.com/NTANewsNow/status/1918607611420660172?t=hq3bHIKxYRmmRMKg7N5mYw&s=19 Ya jinjinawa mawakan inda a wasu lokutan aka hangoshi yana rausayawa.