Ji Dalilai bakwai da ke ta’azzara talauci a yankunan karkarar Najeriya>>Inji Bankin Duniya
Wani sabon rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna yadda talauci ƙaruwa a yankunan karkara a Najeriya, inda alaƙluma ke nuna ya ƙaru zuwa kashi 75 cikin 100 a watan Afrilu.
Rahoton da bankin ya fitar na watan Afrlun 2025, ya nuna cewa talaucin dai ya ƙaru a ɓangren karkara idan aka kwatanta da yadda yake a biranen ƙasar.
Rahoton ya yi nazari kan girman talauci a ƙasashen duniya, yana mai bayyana kashi 30.9 cikin 100 na 'yan Najeriya na rayuwa ne kasa da dala biyu a kowacce rana a shekara ta 2018/2019 - kafin annobar korona.
Haka kuma, rahoton ya nuna cewar 'wasu alkaluma da aka fitar na 2018/2019 ya nuna cewar akwai karin mutum miliyan 42 da suka sake faɗawa cikin talauci a Najeriya, wanda hakan ke nuni da fiye da rabin al'ummar ƙasar wato kashi 54% da aka yi ƙiyasin na fama da t...







