Ni Musulmi ne kuma nasa Allah a raina sanda nake aiki, Na yiwa Najeriya aiki tukuru ta yanda ko hutu bana samu, kuma a shirye nake na amsa tambayoyin EFCC, amma dai yanzu basu kamani ba ina nan ina hutawa tukuna>>Tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari
Tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari ya fito ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa wai yana hannun hukumar EFCC inda ake bincikensa.
Kyari ya fitar da sanarwa ta shafinsa na X inda yace a yanzu yana hutawa ne bayan kammala yiwa Najeriya aiki na tsawon shekaru 34.
Yace a lokacin da yake aiki ko hutun sati biyu baya samu dan haka yanzu yana hutun da ya kamata ace yayi a baya.
Yace 'yan uwa da abokan arziki suna ta kiranshi suna sanar dashi game da wani labari dake cewa an kamashi yana hannun EFCC.
Yace wannan labari karyane, yace a sanda yake aiki ya sa Allah a ransa saboda yasan zai tsaya a gaban Allah ya amsa tambayoyi.
Dan haka yace a yanzu ma a shirye yake ya amsa tambayoyin EFCC ka yanda ya gudanar da ayyukansa.
Yace ya kamata a daina yada ir...







