Monday, December 15
Shadow
An Kama wani Ɗan Nijar a Dajin Yankari sanye da kayan sojoji.

An Kama wani Ɗan Nijar a Dajin Yankari sanye da kayan sojoji.

Duk Labarai
An Kama wani Ɗan Nijar a Dajin Yankari sanye da kayan sojoji. Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta kama wani mutum mai suna Jibrin Ali, ɗan shekara 28 daga Zandar, Jamhuriyar Nijar, a cikin dajin Yankari da ke ƙaramar hukumar Alkaleri. An kama shi ne yayin sintiri na hadin gwiwa, yana sanye da kayan sojoji, kuma ana zargin yana ciki waɗanda suke tada hankali a yankin wanda ya ke fama da ayyukan ‘yan bindiga, ya kasa bayar da sahihin bayani kan dalilin kasancewarsa a dajin.Kwamishinan ‘yan sanda ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa sojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa sojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar.

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa s5ojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar. Yayin da yake jawabi ga sojojin ƙasar ranar Juma'a a wata ziyara da ya kai jihar Katsina - ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ƴan fashin daji, shugaban ƙasar ya ce matsalar ƴanta'adda da masu garkuwa da mutane da ƴan fashin daji ta jima a ƙasar. "Ƴan Najeriya sun zuba muku ido, suna jiran ku kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da ƙwato kowane yanki na ƙasarmu, ku nuna wa maƙiyan Najeriya cewa ƙaryarsu ta ƙare'', in ji Shugaba Tinubu. ''Gwamnati na ɗaukar matakan samar muku isassun kayan aiki, da suka haɗ da sabbin fasahohin zamani da sabbin hanyoyin tattara bayanan sirri da dabarun yaƙi, ba wai don kare ƙasarmu kaɗai ba, sai don samun ƙar...
Facebook da Instagram na barazanar daina aiki a Najeriya saboda Harajin da Gwamnatin Tinubu ke saka mai yayi yawa

Facebook da Instagram na barazanar daina aiki a Najeriya saboda Harajin da Gwamnatin Tinubu ke saka mai yayi yawa

Duk Labarai
Kamfanin Meta iyayen Facebook da Instagram na barazanar ficewa daga Najeriya saboda yawan dokokin da gwamnatin tarayya ke gindaya musu. Hakanan dayan dalilin da yasa kamfanin ke son ficewa daga Najeriya hadda harajin da ake kaka ba musu wanda suka ce yayi yawa. Gwamnatin Najeriya ta maka kamfanin META a kotu akan zarge-zarge daban-daban inda take neman kamfanin ya biyata diyyar Dala Miliyan $290m, META sun shiga kotu amma basu yi nasara ba. Kamfanin na Meta dai shine kuma ke da manhajar WhatsApp amma bai bayyanata cikin wanda zai kulle ba. Kotun dai ta baiwa kamfanin nan da zuwa watan Yuni ya biya harajin da aka kakaba masa.
Bidiyo Kalli Miliyan 10 da kayan Abinci, Shinkafa, Kaza, da Talotalo, lemu da za’a kai a matsayin kudin fansa dan kubutar da wani da aka yi Gàrkùwà dashi

Bidiyo Kalli Miliyan 10 da kayan Abinci, Shinkafa, Kaza, da Talotalo, lemu da za’a kai a matsayin kudin fansa dan kubutar da wani da aka yi Gàrkùwà dashi

Duk Labarai
Bidiyon yanda aka tara Miliyan 10 a matsayin kudin fansa za'a kaiwa 'yan Bindiga ya dauki hankulan mutane sosai a kafafen sada zumunta. Rahoton Bidiyon yace an tara kudinne ta hanyar neman taimako. Sannan 'yan Bindigar sun nemi a kuma kai musu Lemu da kaza da sauran kayan abinci wanda suma sun kai Naira Miliyan 1. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1918310544060170580?t=Gi4pQc0qWeFOsOA26eFvzg&s=19 Mutane dai sun yi ta Allah wadai kan lamarin.
Ribar da bankunan Najeriya ke samu ta ragu

Ribar da bankunan Najeriya ke samu ta ragu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, ribar da bankunan Najeriya ke samu ta ragu matuka a yayin da suka bayyana yawa kudaden da suka samu a watanni 3 na farkon shekarar nan. A baya dai bankunan kan sau jimullar ribar Naira biliyan 150 a iin wannan lokaci amma da alama lamura sun canja. An alakanta hakan da hauhawar farashin kayan masarufi inda a yanzu bankunan ke kashe kudade da yawa wajan gudanar da ayyukansu fiye da da. Misali bankin GTCO ya samu raguwar riba da kaso 41 cikin 100, shi kuma bankin First Bank ya samu raguwar riba ne da kaso 20.2 cikin 100. Da dai sauransu.
Da Duminsa: Ji Abinda Dan shugaba kasa, Seyi Tinubu yace bayan da shugaban kungiyar daliban Najeriya yace yasa an masa dukan kawo wuka saoda yaki goyon bayan Tinubu

Da Duminsa: Ji Abinda Dan shugaba kasa, Seyi Tinubu yace bayan da shugaban kungiyar daliban Najeriya yace yasa an masa dukan kawo wuka saoda yaki goyon bayan Tinubu

Duk Labarai
A yaune aka tashi da labarin shugaban kungiyar Dalibai ta kasa, Comrade Atiku Abubakar Isah inda ya zargi dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da daukar nauyin 'yan daba suka dakeshi. Yace an masa wannan cin zarafine saboda yace ba zai goyi bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba. Saidai a martaninsa, Dan shugaban kasar, Seyi Tinubu yace wannan zargi ba gaskiya bane. A sakon da ya fitar ta shafinsa na Instagram, Seyi Tinubu yace shi baima taba haduwa da shugaban kungiyar dalibanba.
An Tura Shi Gaidan Yari Saboda Ya Yada Labarin Cewa Gwamnan Kebbi Zai Bar APC

An Tura Shi Gaidan Yari Saboda Ya Yada Labarin Cewa Gwamnan Kebbi Zai Bar APC

Duk Labarai
An Tura Shi Gaidan Yari Saboda Ya Yada Labarin Cewa Gwamnan Kebbi Zai Bar APC. Muna rokon gwamnatin jihar Kebbi da ta dubi girman Allah ta saki wannan bawan Allah Muktar da aka kama a yau aka tura gidan yari. Laifin Muktar daya ne, saboda ya yi 'sharing' wani 'posting' wanda wata gidan jarida ta ruwaito na cewa " Gwamnan jihar Kebbi zai bar jam'iyyar APC". Sanadiyyar wannan posting din da wannan bawan Allah ya yi sharing a page dinsa, yau an kama shi an gurfanar da shi kotu. Babu wani jayayya aka wuce da shi gidan yari. Muktar ya fito ya bada hankuri na wannan posting din da ya yi, amma kuma ba'a duba masa ba, saida aka kama shi aka gurfanar da shi a kotu. Mun san Gwamnan jihar Kebbi mai adalci ne, dan Allah ka dubawa wannan bawan Allah. Yana da iyali kuma yana da 'yan u...
Gwamnan Katsina ya ba da hutun aiki saboda ziyarar Tinubu

Gwamnan Katsina ya ba da hutun aiki saboda ziyarar Tinubu

Duk Labarai
Gwamnan jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ya ayyana yau Juma'a a matsayin ranar hutu ga ma'aikata domin "tarɓar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu" da ke ziyara a jihar tasu. Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin jawabin da ya gabatar a taron Ranar Ma'aikata. "Ina mai farin cikin shaida muku cewa Shugaba Tinubu zai kawo ziyara Katsina gobe [Juma'a] domin buɗe ayyuka da dama da muka kammala cikin shekara biyu da suka wuce," in ji gwamnan. "Saboda haka, na ayyana goben a matsayin ranar hutu saboda ma'aikata su samu damar haɗuwa da mu wajen tarɓar shugaban ƙasa." A jiya Alhamis ne fadar shugaban Najeriya ta sanar cewa Tinubu na jam'iyyar APC zai kai ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar da ke arewa maso yamma kuma ta tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.