Thursday, December 18
Shadow
Ka jawa Danka kunne yana wuce gona da iri>>Atiku ya gayawa Shugaba Tinubu bayan da aka zargi Seyi Tinubu da lakadawa shugaban Daliban Najeriya dukan kawo wuka

Ka jawa Danka kunne yana wuce gona da iri>>Atiku ya gayawa Shugaba Tinubu bayan da aka zargi Seyi Tinubu da lakadawa shugaban Daliban Najeriya dukan kawo wuka

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya jawo hankalin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya jawa iayalinsa musamman dansa, Seyi Kunne. Atiku yace Najeriya ba kayan Tinubu bane kasa ce ta al'umma dan haka bai kamata a bar dan shugaban kasar yana abinda yake ba na yawo yana nemawa mahaifinsa goyon baya ba. Atiku yace ya zama wajibi a binciki zargin da shugaban kungiyar daliban Najeriya ya yiwa Dan shugaban kasar dan gano gaskiya. Atiku yace kuma ko me ya faru da Shugaban daliban ba zasu amince ba zasu tsaya mai. Yace abin takaici ne ace irin wannan abin yana fitowa daga iyalin shugaban kasa. Atiku yace wannan abu ne da ba za'a amince dashi ba.
Ji yanda shugaba Tinubu ya kaiwa Sojojin dake Fagen yaki ziyarar ba zata ba tare da jami’an tsaronsa ba a jihar Katsina

Ji yanda shugaba Tinubu ya kaiwa Sojojin dake Fagen yaki ziyarar ba zata ba tare da jami’an tsaronsa ba a jihar Katsina

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kaiwa sojojin Najeriya na rundunar Operation FANSAR YAMMA dake yaki da 'yan Bindiga a jihar Katsina ziyarar ba zata dan ya ga yanda ake gudanar da aiki. Shugaban ya je ne ba tare da jami'an tsaronsa ba kamar yanda aka saba. Ya karfafa sojojin musamman yanda suka sadaukar da rayuwarsu dan samarwa mutanen Najeriya tsaro. Yace zasu yi kokarin biyan sojojin dukkanin hakkokinsu da kuma inganta rayuwarsu data iyalinsu.
Irin Yadda Allah Ya Daukaki Kuŕ’ani Da ManźonŠà, Allah Ya Daukaka Sarki Aminu Ado Bayero Ya Kuma Daga Martabarsa, Inji Sheik Lawal Triumph

Irin Yadda Allah Ya Daukaki Kuŕ’ani Da ManźonŠà, Allah Ya Daukaka Sarki Aminu Ado Bayero Ya Kuma Daga Martabarsa, Inji Sheik Lawal Triumph

Duk Labarai
Irin Yadda Allah Ya Daukaki Kuŕ'ani Da ManźonŠà, Allah Ya Daukaka Sarki Aminu Ado Bayero Ya Kuma Daga Martabarsa, Inji Sheik Lawal Triumph. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shehin Malamin ya gabatar da wannan addu'ar ne a wajen bikin saukar karatun Alƙur’ani da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya halarta a jiya Alhamis, Kofar Gidan Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babbba Ɗan'agundi, Dake Unguwar Gini Musa Da Ofishin 'Yan Śanda na Kwalli a cikin birni Kano.
Kalli Bidiyo: Wata mata ta fito tace ita Annabiya ce kuma Akwai Karama akanta, Duk wanda ya shafa zai yi kudi, mutane na ta tururuwar zuwa shafa Kanta

Kalli Bidiyo: Wata mata ta fito tace ita Annabiya ce kuma Akwai Karama akanta, Duk wanda ya shafa zai yi kudi, mutane na ta tururuwar zuwa shafa Kanta

Duk Labarai
Wannan wata mata ce data bayyana inda ta yi ikirarin Annabta. Matar tace tana da wata karama a kanta da duk wanda ya shafa yake samun waraka musamman daga kangin Talauci. Mutane maza da mata na ta tururuwa zuwa gidanta dan taba kanta kamar yanda Bidiyon ya nunar. https://www.youtube.com/watch?v=0jH98leT6fs Sai Muce Subhanallah.
Jam’iyyar LP ba za ta shiga kowace ƙawance ba a 2027

Jam’iyyar LP ba za ta shiga kowace ƙawance ba a 2027

Duk Labarai
Jam'iyyar adawa ta LP a Najeriya ta nesanta kanta daga shiga kowace irin ƙawance dmin tunkarar zaɓen 2027. Kwamitin zartarwar jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ne ta tababtar da haka lokacin wani taro da ta gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar. A baya-bayan nan dai jam'iyyun hamayya a Najeriya na ta ƙoƙarin ƙulla wata haɗaka domin tunkarar jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027. To sai dai jam'iyyar ta LP ta ce ba za ta shiga kowace irin haɗaka. “Taronmu a jajjada cewa jam'iyyarmu ba ta ciki, kuma ba za ta shiga kowane irin haɗaka ba domin tunkarar zaɓen 2027, a maimakon haka jam'iyyar LP za ta mayar da hankali wajen sake gina kanta ta hanyar ɓullo da sabbin sadaru da ƙarfafa kanta domin samun nasara a zaɓen 2027'', in ji Abure.
Saudiyya ta saka tarar riyal 20,000 ga masu yin aikin Hajji ba bisa ƙa’ida ba

Saudiyya ta saka tarar riyal 20,000 ga masu yin aikin Hajji ba bisa ƙa’ida ba

Duk Labarai
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta tabbatar da cewa duk mutumin da aka kama yana taimaka wa mutane wajen yin aikin Hajji ba bisa ƙa'ida ba zai fuskanci tarar riyal 100,000. Tarar za ta shafi duk wanda da ke ɓoye maniyyatan da ba su da cikakkun takardu a gidajensu, ko nema musu biza, ko kuma yin jigilarsu. Lokutan da dokokin suka shafa su ne daga 1 ga watan Zulƙi'ida (wanda ya yi daidai da 29 ga watan Afrilu) har zuwa 14 ga watan Zulhijja (10 ga watan Yuni). Duk mutumin da aka kama yana ƙoƙarin gudanar da aikin Hajjin ba tare da takardun izini ba zai fuskanci tarar riyal 20,000. Sannan kuma za a mayar da shi ƙasarsa tare da hana shi shiga Saudiyya tsawon shekara 10. Irin wannan tarar za a yi wa duk wanda aka kama da kowace irin biza ta ziyara wadda ta gama aiki yan...
Duka kwalejojin ilimi a Najeriya za su fara ba da shaidar digiri

Duka kwalejojin ilimi a Najeriya za su fara ba da shaidar digiri

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara aiwatar da sabon tsarin Dual Mandate Policy a dukkan kwalejojin ilimi na ƙasar wanda ke ƙunshe cikin sabuwar dokar kwalejojin ilimi ta 2023. A cewar wata sanarwa daga ma'aikatar ilimi, dokar ta bai wa dukkan kwalejojin damar bayar da shaidar karatu ta digiri da kuma NCE a lokaci guda a fannin koyarwa. Ministan Ilimi Tunji Alausa ya siffanta tsarin a matsayin "babba kuma na cigaba". "Wannan tsari na Dual Mandate Policy ba gyara ba ne kawai, gagarumin sauyi ne da ke bai wa kwalejojin damar bayar da shaidar NCE da kuma digiri," in ji ministan kamar yadda sanarwar ta ruwaito. "Tsarin zai ƙarfafa kwalejojin, ya ƙara yawan damar samun ilimi, kuma ya kyautata ingancin azuzuwan koyarwa a faɗin Najeriya."