Friday, December 5
Shadow
Kalli Bidiyo: Sojan Najeriya yayi gargadin cewa ida aka sake aka kori Sojan Ruwa, AM. Yerima daga aiki, za’a ga abhinda Zhasuyi a kasarna

Kalli Bidiyo: Sojan Najeriya yayi gargadin cewa ida aka sake aka kori Sojan Ruwa, AM. Yerima daga aiki, za’a ga abhinda Zhasuyi a kasarna

Duk Labarai
Sojan Najeriya ya bayyana cewa masu kiran a kori Sojan ruwa, AM. Yerima daga aiki, su jira su ga abinda zai faru idan hakan ta faru. Yace ba zai yiyu Janar ya bayar da umarni ba wani Dan siyasa yace kada abi wannan umarnin ba. https://twitter.com/General_Somto/status/1989027173659730321?t=ocG686SlrNHmBopm3mhWdQ&s=19 Hakan na zuwane bayan dambarwar data faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da Sojan Ruwa, AM. Yerima bayan da sojan ya hana Wike Shiga wani fili a Abuja.
Babban Malamin Kirista, Reverend Ezekiel Dachomo na san Suka har daga wajan Kiristoci saboda kiran Addinin Musulunci addinin Qarya

Babban Malamin Kirista, Reverend Ezekiel Dachomo na san Suka har daga wajan Kiristoci saboda kiran Addinin Musulunci addinin Qarya

Duk Labarai
Malamin Kirista, Reverend Ezekiel Dachomo ya mayarwa da Sheikh Dr. Ahmad Gumi da martanin cewa da gaske an binne Kiristoci da yawa wanda ake zargin 'yan Bindiga da kashewa. Hakan na zuwane bayan da Rahotanni suka bayyana cewa, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya zargi Kiristoci da binne akwatunan gawa a karya da babu gawar a ciki dan su nuna cewa, an kashe musu mutane. Faston ya kai ziyara wani kabari da aka binne mutane 27 kamar yanda yace inda anan ne yace zasu sa matasa su hako gawarwakin dan a nuna shaida. A cikin jawabinsa ne yake cewa Addinin Musulunci addinin Qarya, Subhanallah. Saidai wasu hadda Kiristoci sun bayyana cewa abinda ya fada bai kamata ba, bai kamata bacin ran abinda Sheikh Gumi ya masa ba yasa ya bayyana gaba dayan Addinin Musulunci da addinin Qarya ba. https://tw...
Shugaba Tinubu ba zai zarce ba a 2027>>Inji Hadimar Buhari, Lauretta Onochie

Shugaba Tinubu ba zai zarce ba a 2027>>Inji Hadimar Buhari, Lauretta Onochie

Duk Labarai
Hadimar tsohon shugaban kasa, Marigayi, Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta bayyana cewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai zarce a shekarar 2027 ba. Tace tana daga cikin wadanda suka zabi Tinubu amma ta yi nadamar zabenshi. Lauretta Onochie dai ta dade tana sukar Gwaamnatin Shugaba Tinubu dan haka wadannan kalamai nata ba zasu zowa mutane da mamaki ba
Allah Sarki:Ji Yanda tsohon Dansanda ya baiwa Sojan Ruwa, AM. Yerima wani sashe na kudin Fansho dinsa inda yace Abinda yawa Wike abin jinjinawane

Allah Sarki:Ji Yanda tsohon Dansanda ya baiwa Sojan Ruwa, AM. Yerima wani sashe na kudin Fansho dinsa inda yace Abinda yawa Wike abin jinjinawane

Duk Labarai
Tsohon dansandan Najeriya, Sunny Anyanwu ya gabatar da Naira dubu 5 daga cikin dubu 49 da yake karba a matsayin kudin fansho ga sojan ruwa AM. Yerima. Dansandan yace a aika masa da lambar asusun banki na Soja Yerima dan ya aika masa da kudin. yace abinda sojan ruwan yawa Wike abin a yaba ne inda yace yana fatan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai baiwa sojan lambar yabo.
Da Duminsa: Mutum daya ya rigamu gidan gaskiya, wasu suka jikkata a Turmutsitsun daya faru a gidan karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle dake jihar Zamfara

Da Duminsa: Mutum daya ya rigamu gidan gaskiya, wasu suka jikkata a Turmutsitsun daya faru a gidan karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle dake jihar Zamfara

Duk Labarai
Turmutsutsu a gidan karamin ministan tsaro dake Gusau jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi sanadiyyar rasa rai daya wasu mutane 6 suka jikkata da yammacin ranar Alhamis. Rahotanni sun ce lamarin ya farune da misalin karfe 7:30 na ranar Alhamis yayin da mutane suka taru a gidan nasa dan tarbarshi. Zagazola Makama yace wanda ya rasun sunansa, Khalifa Uzairu kuma dan kimanin shekaru 23 ne. Sannan akwai mutane 6 Ayuba Sani, Muhammadu Adams, Aliyu Aminu, Shaaban Hamisu, da Inusa Musa Shehu da su kuma suka jikkata suna karbar magani. An kai jami'an tsaro wajan sannan an fara binciken yanda lamarin ya faru.
Kalli Bidiyon abin ban mamaki: Wata tsohuwar malamar Jinya(NURSE) tace sukan canjawa mata jarirai bayan sun haihu, wani lokacin ma sukan dauke Jariri su ajiye ma me jego Mattaccen Jariri, su sayar da natan

Wata tsohuwar malamar Jinya, Nurse ta dauki hankula saboda irin bayanan data fitar kan irin yanda ta gudanar da aikinta. Tace wasu lokutan sukan canjawa me Jego Jariri ko kuma su dauke jariri me rai su ajiye matacce. Tace suna sayar da Namijin Jariri akan Naira Miliyan 4.5 ko Miliyan 3. Hakanan sukan sayar da macen Jaririya akan Naira Miliyan 2.5. https://twitter.com/instablog9ja/status/1989329219139051955?t=LzUAB8PG1hcsm4opoIK0ug&s=19