Sunday, February 15
Shadow
Da Duminsa: Majalisar Jihar Rivers ta fara shirin tsige gwamna Fubara

Da Duminsa: Majalisar Jihar Rivers ta fara shirin tsige gwamna Fubara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Rivers sun bayyana cewa, Majalisar Jihar ta fara shirin tsige gwamnan jihar, Simi Fubara. An ga kakakin majalisar a wani Bidiyo daya watsu sosai a kafafen sada zumunta yana cewa 'yan majalisar 26 sun sakawa takardar neman tsige Fubara hannu. https://twitter.com/i/status/2009198809163665530 Majalisar tace tana zargin Gwamna Fubara da karya dokar kundin tsarin Mulki. Kuma sun ce zasu aika masa da takarda kan hakan. Hakanan majalisar ta kuma ce ta fara shirin tsige mataimakin Gwamnan na jihar Rivers, Ngozi Nma Odu. Majalisar ta kuma ce ta dakatar da shirin Gwamna Fubara na kai mata kasafin kudin shekarar 2026.
Kai Duniya: Ji abinda wata matashiya daga Arewa ta yi bayan data yi cikin Shyègyè ta haihu da ya dauki Hankula

Kai Duniya: Ji abinda wata matashiya daga Arewa ta yi bayan data yi cikin Shyègyè ta haihu da ya dauki Hankula

Duk Labarai
Wata matashiya daga Arewa da ta yi cikin shege ta haihu ta kuma mayar da dan inda ya fito ta dauki hankula. Ta aikawa Malam tambaya ne inda tace ta tuba kuma tana neman yanda Allah zai yafe mata. Abin dai ya baiwa mutane mamaki amma Malam yace idan da gaske ta tuba Allah zai yafe mata idan ta maye abinda ta aikata da kyakkyawa. https://www.tiktok.com/@mhaliru92/video/7592682873547787541?_t=ZS-92tcnLlGekz&_r=1
Wata Sabuwa: Bayan da aka bukaci ya je ICPC ya bayar da hujja kan zargin da yakewq shugaban Hukumar NMDPRA, Dangote yace ya janye zargi da yake

Wata Sabuwa: Bayan da aka bukaci ya je ICPC ya bayar da hujja kan zargin da yakewq shugaban Hukumar NMDPRA, Dangote yace ya janye zargi da yake

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Dangote ya janye zargin da yakewa shugaban Hukumar NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmad a gaban Hukumar ICPC. Dangoten ya janye zargin da yake wa Ahmad ne inda yace ya kashe dala Miliyan $7 wajan biyawa 'ya'yansa kudin makaranta a kasar Switzerland. Wata Majiya tace Dangoten ya janye zarginne bayan da aka bukaci ya je da kansa ba aiken Lauya ba ya gabatar da hujjoji a gaban ICPC kan wannan zargin da yake. Hakanan Wata Hujja da aka samu game da janye wannan korafi da Dangoten yayi shine EFCC ta fara bincike kan lamarin. Saidai ICPC tace duk da wannan Janyewar da Dangote yayi ba zata yi watsi da binciken da takewa Ahmad ba, tace ta ma aika da bukatar bincike makarantar da ake zargin Ahmad din ya kai 'ya'yansa. Ahmad dai tun tuni ya sauka daga kan mukaminsa ...
Kalli Bidiyon: Tsohon Shugaban Buhari ya yi ta neman Masu gaskiya irinsa da zai baiwa Mukami amma ya kasa samun ko da mutum daya>>Inji Hadimin Shugaban kasar, Malam Bashir Ahmad

Kalli Bidiyon: Tsohon Shugaban Buhari ya yi ta neman Masu gaskiya irinsa da zai baiwa Mukami amma ya kasa samun ko da mutum daya>>Inji Hadimin Shugaban kasar, Malam Bashir Ahmad

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nemi wadanda zai baiwa mukaman Siyasa masu gaskiya da kishin Najeriya irinsa amma ya kasa samu. Hadiminsa, Malam Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a wata hira da Ali Jita yayi dashi. Yace Buhari ya gaya musu cewa a tsawon lokacin da ya dauka yana kokarin neman Mulki, ya manta bai nemi mutane nagartattu ba da zai yi aiki dasu. Yace sai bayan da ya ci zabe, ya je gida ya kwanta amma Bacci ya ki zuwa, yace sai ya tuna wata ma'aikata da ke da matsala, sai yayi tunanin wanene zai dakko me irin ra'ayinsa ya baiwa wannan ma'aikata amma sai ya kasa samun ko da mutum daya. Yace a wannan lokacinne yasan cewa bai samarwa kansa abokan aiki ba. https://www.tiktok.com/@realalijita/video/7592575748817440008?_t=ZS-92tY3O7k8DA&_r=1
A shekarar 1983 manyan sojoji sun sameni suka ce zasu yiwa Tsohon Shugaban kasa, Shehu Shagari Juyin mulki dan in zama shugaban kasa amma nace bana so>>Inji Obasanjo

A shekarar 1983 manyan sojoji sun sameni suka ce zasu yiwa Tsohon Shugaban kasa, Shehu Shagari Juyin mulki dan in zama shugaban kasa amma nace bana so>>Inji Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, a shekarar 1983, manyan sojoji sun sameshi suka ce zasu yiwa shugaban kasa a wancan lokacin, Shehu Shagari Juyin Mulki dan shi Obasanjon ya zama shugaban kasa. Saidai Obasanjon yace musu baya so. Yace dalilinsa shine su suka Kafa Dimokradiyya diyya a Najeriya dan haka ba zai zama cikin wanda zasu rusata ba. Hakanan shima tsohon shugaban kasar Soji, Janar Ibrahim Badamasi ya tabbatar da wannan labari na Obasanjo.