Sunday, April 5
Shadow
Allah ya gayamin idan na bar cocin RCCG dana na farko zai mùtù>>Inji Fasto Enoch Adeboye

Allah ya gayamin idan na bar cocin RCCG dana na farko zai mùtù>>Inji Fasto Enoch Adeboye

Duk Labarai
Babban Faston cocin RCCG, fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa, Allah ya taba gargadinsa cewa idan ya bar cocin RCCG din dansa na farko zai mutu. Faston ya bayyana hakane a wajan wani taron addu'a da aka yi a cocinsa ta RCCG din dake Ogun ranar 7 ga watan Yuni. Faston ya bayyana damuwa sosai kan yanda wasu kiristoci ke tsalle daga wannan coci zuwa wancan coci. Inda yace shi kam Allah ne ya hanashi canja coci dan ya gargadeshi idan ya canja, dansa na fari zai mutum.
Kalli Bidiyo: In baka da Miliyan 50 ba zan iya auren ka ba>>Inji Wannan matashiyar

Kalli Bidiyo: In baka da Miliyan 50 ba zan iya auren ka ba>>Inji Wannan matashiyar

Duk Labarai
Wata matashiya ta dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan da tace idan mutum bashi da Miliyan 50 ba zata iya aurensa ba. Ta bayyana hakane a wani shirin da ake hira da ita. Tace miliyan 50 din da take magana ba wai na wani abu bane, na shagalin bikine take magana akai. https://www.tiktok.com/@juicy_lifstyle/video/7512539700184337670?_t=ZM-8x1x4TwvWGW&_r=1 Da yawa dai sun bayyana mamaki da wannan ikirari nata.
Karanta Jadawalin Fitattun ‘Yan Siyasa Goma Da Suka Fi Kowanne Dan Siyasa Kudi A Nijeriya

Karanta Jadawalin Fitattun ‘Yan Siyasa Goma Da Suka Fi Kowanne Dan Siyasa Kudi A Nijeriya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Fitattun 'Yan Siyasa Goma Da Suka Fi Kowanne Dan Siyasa Kudi A Nijeriya Bola Ahmed Tinubu Ibrahim Badamasi Babangida Orji Uzor Kalu Andy Uba Abubakar Bukola Saraki David Mark Ifeanyi Ubah Olusegun Obasanjo Atiku Abubakar Rochas Okorocha Me za ku ce? MAJIYA: Politics Nigeria
Ku bi duk inda masu yiwa Najeriya barazanar tsaro suke ku gama dasu>>Shugaban Sojojin Najeriya ya baiwa sojojin Umarni

Ku bi duk inda masu yiwa Najeriya barazanar tsaro suke ku gama dasu>>Shugaban Sojojin Najeriya ya baiwa sojojin Umarni

Duk Labarai
Shugaban sojojin Najeriya, COAS, Lt.-Gen. Olufemi Oluyede ya baiwa sojojin Umarnin su bi duk inda masu yiwa Najeriya barazanar tsaro suke su gama dasu. Ya bayar da wannan umarnin ne a yayin bikin sallah tare da sojojin a Giwa dake jihar Kaduna. Maj.-Gen. Erema Akerejola, ne ya wakilci shugaban sojojin a wajan bikin sallar. Yace biyayya da karfin hali da sojojin Najeriya ke nunawa ya taimaka matuka wajan nasarorin sa suke samu a fagen daga. Ya kuma jinjinawa sojojin da suka rasa rayukansu a fagen daga inda yace yana baiwa iyalansu tabbacin jajircewar da suka nuna ba zata tafi a banza ba.
Kasar Ìran ta yiwa kasar Israyla mummunan kutse inda ta kwashi bayananta game da makamin kare danginta

Kasar Ìran ta yiwa kasar Israyla mummunan kutse inda ta kwashi bayananta game da makamin kare danginta

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Iran na cewa, kasar ta yiwa kasar Israyla kutse inda ta kwashi bayananta game da makamashin kare danginta. Rahoton yace kasar Iran ta dauki hayar wasu 'yan kasar Israelan aiki ne inda ta rika biyansu makudan kudade wanda suka rika bata bayanan sirri game da kasar ta Israela. Iran ta sanar da cewa ta dade tana wannan shirin kuma ba yau ta yi nasara ba amma dai ta tsaya ne kamin ta tabbatar da takardun bayanan sirrin kasar Israelan sun zo hannunta kamin ta sanar da nasarar ta. Kasar Israyla dai bata ce uffan ba kan lamarin. Saidai wasu rahotanni sun ce an kama wasu mutane da ake zargin sun hada kai da kasar Iran a cikin kasar ta Israela. A shekarun baya dai, kasar Israela itama tawa kasar Iran irin wannan kutse.
SANARWA GA MATAFIYA: Yanzu Haka Hanyar Abuja Zuwa Kano-Kaduna Ta Cunkushe, Inda Masu Ababen Hawa Suka Yi Curko-Curko Dauke Da Matafiya Musamman Masu Zuwa Hidimar Sallah

SANARWA GA MATAFIYA: Yanzu Haka Hanyar Abuja Zuwa Kano-Kaduna Ta Cunkushe, Inda Masu Ababen Hawa Suka Yi Curko-Curko Dauke Da Matafiya Musamman Masu Zuwa Hidimar Sallah

Duk Labarai
SANARWA GA MATAFIYA: Yanzu Haka Hanyar Abuja Zuwa Kano-Kaduna Ta Cunkushe, Inda Masu Ababen Hawa Suka Yi Curko-Curko Dauke Da Matafiya Musamman Masu Zuwa Hidimar Sallah. Idan da wata hanya da matafiya masu bin hanyar za su bi, gwamma su sauya don gudun fadawa cikin cunkuson. Wasu rahotonnni da Rariya ta samu, sun bayyana cewa cunkoson motocib ba ya rasa na nasaba da gyaran hanya da ake yi. Jama'a don Allah a yada (sharing) domin amfanar matafiyan dake shirin bin hanyar.
YANZU-YANZU: Jama’a Sun Ruga Cikin Gidajensu Da Gudu, Bayan Sun Ji Karar Harbe-Haŕbè A Garin Buni Gari Dake Jihar Yobe, Iñda Suķè Zàrgin masu ikirarin  Jìhàdì Nè Suka Shigo Garin

YANZU-YANZU: Jama’a Sun Ruga Cikin Gidajensu Da Gudu, Bayan Sun Ji Karar Harbe-Haŕbè A Garin Buni Gari Dake Jihar Yobe, Iñda Suķè Zàrgin masu ikirarin Jìhàdì Nè Suka Shigo Garin

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Jama'a Sun Ruga Cikin Gidajensu Da Gudu, Bayan Sun Ji Karar Harbe-Haŕbè A Garin Buni Gari Dake Jihar Yobe, Iñda Suķè Zàrgin masu ikirarin Jìhàdì Nè Suka Shigo Garin
Na yi na’am da hana hawan Sallah a Kano da hukumar ‘yansanda suka yi kuma ina zan bi wannan doka>>Inji Sarki Aminu Ado Bayero

Na yi na’am da hana hawan Sallah a Kano da hukumar ‘yansanda suka yi kuma ina zan bi wannan doka>>Inji Sarki Aminu Ado Bayero

Duk Labarai
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yace yayi murna da hana hawan Sallah da hukumar 'yansandan jihar suka yi. A ranar Talata ne hukumar 'yansandan jihar suka fitar da sanarwar cewa, sun dakatar da hawan Sallah a Kano. Hakan na zuwane jim kadan bayan da sarki Muhammad Sanusi II ya aikawa hakimai da su je hawan Sallah. Saidai a sanarwar da Sarki Aminu Ado ya fitar yace yana maraba da dakatar da hawan sallar kuma zai bi wannan doka. Sarki Aminu ya sanar da hakanne ta bakin kakakinsa, Awaisu Abbas Sanusi inda yace ya dauki wannan mataki ne bayan tuntuba da yayi da masu ruwa da tsaki
Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya ta kara yawan ziga-zirgar jirgin saboda tafiye-tafiyen Sallah

Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya ta kara yawan ziga-zirgar jirgin saboda tafiye-tafiyen Sallah

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, (NRC) ta kara yawan zirgazirgan jirgin kasar dake Jigila daga Legas zuwa Ibadan. Hakan na zuwa ne yayin da mutane ke ta tafiye-tafiye dan shagulgulan Sallah. Me magana da yawun hukumar, Callistus Unyimadu ne ya bayyana haka inda yace jirgin dake Jigila tsakanin Warri-Itakpe shima zai yi aiki na musamman a ranar Alhamis. Sannan yace jirgin Kaduna zuwa Abuja an kara mai yawan tarago.
Ma’aikatan wutar Lantarki zasu tsunduma yajin aiki

Ma’aikatan wutar Lantarki zasu tsunduma yajin aiki

Duk Labarai
Rahotanni na cewa, ma'aikatan wutar lantarki na Abuja zasu tafi yajin aiki. Ana sa ran lamarin zai saka mutanen jihohin Naija, Kogi, da Nasarawa cikin duhu. Ma'aikatan kamfamin me suna (AEDC) sun bayyana cewa, zasu tsunduma yajin aikinne saboda kasa cika alkawuran da kamfanin ya dauka bayan da suka yi yajin aiki a watan Nuwamba na shekarar 2024. A cikin sakon da suka aikawa hukumar kamfanin na AEDC sun Sanar da cewa wannan shine karo na karshe da zasu yi gargadi kuma a koda yaushe zasu iya tsunduma yajin aiki