Mutum 1,296 aka kashe a Najeriya a watan Mayu – Rahoto
Mutum 1,296 aka kashe a Najeriya a watan Mayu - Rahoto.
Wasu sabbin alƙalumma kan matsalar tsaro a Najeriya sun nuna cewa mutum 1,296 aka kashe a watan Mayu a sassan ƙasar.
Rahoton na kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a shiyyar Afirka ta yamma da yankin Sahel ya ce an samu ƙaruwar yawan waɗanda suka mutu a watan Mayu idan aka kwatanta da Afrilu inda aka kashe mutum 1,092.
Rahoton ya kuma ce mutum 1,086 aka yi garkuwa da su a sassan Najeriya a watan Mayu inda aka samu ragi idan aka kwatanta da watan Afrilu da aka yi garkuwa da mutum 1,178.
Rahoton Beacon Security and Intelligence Limited ya nuna cewa an samu ragi na kashi kusan shida cikin dari na matsalolin tsaro a Najeriya cikin watan Mayun da ya gabata, idan aka kwatanta da yadda lamarin ya kasance a watan wa...





