Saturday, December 13
Shadow
Duk da Alkawarin fara biyan matasa masu bautar kasa Naira 77,000, gwamnatin Tinubu ta saba Alkawarin

Duk da Alkawarin fara biyan matasa masu bautar kasa Naira 77,000, gwamnatin Tinubu ta saba Alkawarin

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta saba alkawarin data wa matasa masu bautar kasa, NYSC fara biyansu Alawus din Naira 77,000 a watan Fabrairu inda har yanzu ta ci gaba da biyansu Naira 33,000. Da yawan matasa masu bautar kasa da suka karbi alawus din nasu a daren ranar Juma'a sun bayyana ganin Naira 33,000 maimakon Naira 77,000 da aka musu Alkawari. Hakan ya sabawa maganar da shugaban hukumar ta NYSC, Brigadier General Yushau Ahmed yayi a watan Janairu da ya gabata inda yace maganar karin kudin tabbatacciya ce kawai ana jiran akincewa da kasafin kudin shekarar 2025 ne. Zuwa yanzu dai babu wani karin bayani kan lamarin daga gwamnati wanda hakan ya bar matasan cikin damuwa. Lura da yanda matsin tattalin arziki yayi yawa, Naira 33,000 babu inda zata kai matasan masu bautar kasa.
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NATCA tace aiki ya mata yawa tana fama da matsanancin karancin ma’aikata

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NATCA tace aiki ya mata yawa tana fama da matsanancin karancin ma’aikata

Duk Labarai
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa, NATCA ta bayyana cewa aiki yawa ma'aikatanta yawa saboda karancin ma'aikata da hukumar ke fama dashi. Hukumar tace akwai bukatar a dauki ma'aikata musamman dan saukaka aikin hukumar. Shugaban kungiyar ma'aikatan hukumar, Mr Amos Edino ne ya bayyana haka inda yace aiki yanawa ma'aikatansu yawa wanda hakan yake sa su kasa kammala aikin yanda ya kamata. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a filin jirgi na Murtala Muhammad dake Legas. Yace a ka'ida, ma'aikatansu aikin awanni 2 kawai ya kamata su rika yi suna tashi kamin wani yazo ya karbeka, yace amma yanzu ma'aikatansu har aikin awanni 4 suna yi. Yace makarantar horas da matuka jirgin sama dake Zaria, NCAT dake da alhakin horas da irin wadannan ma'aikata itama tana fama da kar...
Duk namijin da ya ganni sai ya harba, saboda na hadu>>Inji ‘Yar Fim, Lydia Usang

Duk namijin da ya ganni sai ya harba, saboda na hadu>>Inji ‘Yar Fim, Lydia Usang

Duk Labarai
'Yar Fim din kudancin Najeriya, Lydia Usang ta bayyana cewa duk namijin da ya ganta sai sha'awarsa ta tashi saboda tsabar kyan da jikinta ke dashi. Ta bayyana hakane a hirar da jaridar Vanguard ta yi da ita inda tace maganar gaskiya Allah ya mata kyau, babi namijin da zai kalleta bai sake kallo ba. Saidai tace har yanzu bata da tsayayye abinda ta mayar da hankali akai shine aikinta na yin fim.
Sanata Akpabio ya zargi Sanata Natasha Akpoti da saka kaya masu shara-shara dake nuna surar jikinta da kuma yin kwaliyar data wuce kima

Sanata Akpabio ya zargi Sanata Natasha Akpoti da saka kaya masu shara-shara dake nuna surar jikinta da kuma yin kwaliyar data wuce kima

Duk Labarai
A ci gaba da dambarwar data kunno kai tsakanin kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti inda ta zargeshi da neman yin lalata da ita, Sanata Akpabio yace Akpoti na saka kaya shara-shara. Akpabio ya bayyana hakane ta bakin babban hadiminsa, Mfon Patrick wanda ya rubuta a shafin Facebook cewa, Sanata Natasha Akpoti ta sha aikin sanata shine yin kwalliya a koda yaushe da kuma saka kaya masu shara-shara dake nuna tsiraici. saidai lauyan Sanata Natasha Akpoti, Victor Giwa ya shigar da kara kotu akan lamarin inda yake karar hadimin na Akpabio Patrick da shi Akpabio din da kansa inda yace wadannan kalamai sun zubarwa da wadda yake wakilta mutunci a idon jama'a.
Da Duminsa: ‘Yan Bìndìgà sun sako janar Maharazu Tsiga

Da Duminsa: ‘Yan Bìndìgà sun sako janar Maharazu Tsiga

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan Bindiga da suka yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar bautar kasa, Janar Maharazu Tsiga sun sakoshi. An sakoshi ne bayan shafe kwanaki 22 a hannun masu garkuwa da mutanen, Rahoton yace wata majiya tace an sakoshi kuma yana wani asibiti da ba'a bayyana sunansa ba yana jinya. A ranar 6th February 2025 ne 'yan Bindigar suka dira a gidansa suka yi garkuwa dashi tare da jikkata mutane 2 sannan daya daga cikin 'yan Bindigar ya mutu bayan da wani dan Bindigar ya harbeshi bisa kuskure. A baya dai hutudole ya jiyo cewa 'yan Bindigar sun nemi kudin fansa Naira Miliyan 250 kamin sakin tsohon sojan. Saidai zuwa yanzu hukumomin tsaro a jihar basu ce uffan ba kan lamarin.
Banki yayi kiskuren aikawa Wani Kwastoma Tiriliyan 1 a account dinsa

Banki yayi kiskuren aikawa Wani Kwastoma Tiriliyan 1 a account dinsa

Duk Labarai
Bankin Citibank dake kasar Amurka yayi kuskuren aikawa wani kwastomansa Dala Tiriliyan 1 a asusun jiyarsa maimakon Dala $280. Saidai an gyara kuskuren da gaggawa bayan gano hakan. Kuskuren ya farune a ranar 1 ga watan Afrilu na shekarar data gabata, kamar yanda jaridar Financial Times ta ruwaito. Saidai kwana daya da yin kuskuren, Tuni aka gyarashi. Bankin ya sanar da cewa ba'a yi asarar ko sisi daga cikin kudin ba.
Ku yiwa Najeriya addu’a, Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta gayawa musulmai da suka fara Azumin watan Ramadana

Ku yiwa Najeriya addu’a, Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta gayawa musulmai da suka fara Azumin watan Ramadana

Duk Labarai
Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta nemi 'yan Najeriya musulmai da su yi amfani da watan Ramadana wajan nuna son kasa da yiwa kasar addu'a. Remi ta fitar da wannan sanarwa ne ranar Juma'a a babban birnin tarayya, Abuja a yayin da Musulmai ke shirye-shieryen fara azumin watan Ramadana. Ta yi fatan watan na Ramadana zai kawo zaman lafiya, jin dadi da cikar burin rayuwa ga iyalan musulman kasarnan.
Mijina ba Dan iska bane, Sharri kika masa, Matar Sanata Akpabio ta maka Sanata Natasha Akpoti a kotu inda tace sai ta biya diyyar Naira Biliyan 250 na bata sunan data taiwa mijinta

Mijina ba Dan iska bane, Sharri kika masa, Matar Sanata Akpabio ta maka Sanata Natasha Akpoti a kotu inda tace sai ta biya diyyar Naira Biliyan 250 na bata sunan data taiwa mijinta

Duk Labarai
Matar kakakin majalisar Dattijai, Unoma Akpabio ta maka Sanata Natasha Akpoti a kotu bisa zargin bata suna da take hakkin bil'adama. Ta kai Sanata Natasha Akpoti babbar kotun tarayyane dake Abuja. Hakan ya biyo bayan zargin da sanata Natasha Akpoti tawa Akpabio na cewa ta fara samun matsala a majalisar ne tun bayan da ta ki yadda ta yi lalata da da sanata Akpabio. Matar sanata Akpabio ta bayyana cewa, zargin da Sanata Natasha Akpoti tawa mijinta yasa ita da 'ya'yanta sun shiga firgici da kuma tsoron za'a iya kai musu harin da zai iya sawa su rasa rayuwarsu. Dan haka matar Akpabio ta nemi kotun da ta ayyana maganar da Sanata Natasha Akpoti ta yi a matsayin take hakkin mutuncin mijinta. Sannan ta nemi kotun data tursasa Sanata Natasha Akpoti ta biya diyyar Naira Biliyan 250 a...
Reno Omokri ya caccaki ‘yan Kudu masu zagin jihar Bauchi saboda ta bada hutun watan Ramadana, yace jihohin da ake kulle makarantu duk ranar Litinin ya kamata a caccaka ba jihar Bauchi ba

Reno Omokri ya caccaki ‘yan Kudu masu zagin jihar Bauchi saboda ta bada hutun watan Ramadana, yace jihohin da ake kulle makarantu duk ranar Litinin ya kamata a caccaka ba jihar Bauchi ba

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya caccaki 'yan uwansa 'yan kudu da suke zagin jihar Bauchi saboda ta bayar da hutun Azumin watan Ramadana ga makarantu. Omokri ya bayyana cewa fiye da sau 10 yana ziyarar jihar Bauchi. Yace yana son jihar Bauchi kuma mutanenta wayayyu ne wanda sun san abinda suke so a rayuwa. Sannan yace mutanen Bauchi sun zabi gwamnansu kuma suna goyon bayansa a kan duk wani abu da yayi. Yace kuma a Dimokradiyya ake kuma mutanen Bauchi suna goyon bayan abinda gwamnatinsu ta yi na bayar da hutun watan Ramadana, dan haka bai kamata wani ya zauna a Legas, ko Fatakwal ko Anambra ya rika jin haushin wannan mataki ba. Yace jihar Bauchi ba cima zaune bace a Najeriya, jihace wadda take bayar da gudummawa sosai wajan ci gaban Najeriya musamman ta bangaren a...