Allah Sarki, Kamar dai yadda diyarta Zahara ta yi, Kalli Bidiyon A’isha Buhari itama tana ta kukan rashin Mijinta
A dazu ne muka ga Bidiyon diyar Tsohon shugaban kasa, Marigayi, Janar Muhammadu Buhari Watau Zahra Buhari tana ta kuka.
A yanzu kuma, Bidiyon mahaifiyarta, Hajiya A'isha Buhari ce ke kuka.
An ga A'isha Buhari na kuka ne yayin da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya je mata ta'aziyya.
https://twitter.com/channelstv/status/1944769303326097540?t=MlkSLaXhZXIFVtuY6wGqvA&s=19
A gobene dai za'a yi jana'izar gawar shugaba Buhari a mahaifarsa dake Daura.







