Monday, December 15
Shadow
Da Mahaifiyata ta mutu, An bani Kyautar Naira Miliyan dari biyar amma naki karba dan tsare mutunci na>>Inji Shugaban EFCC

Da Mahaifiyata ta mutu, An bani Kyautar Naira Miliyan dari biyar amma naki karba dan tsare mutunci na>>Inji Shugaban EFCC

Duk Labarai
Shugaban hukumar EFCC dake yaki da rashawa da cin hanci a Najeriya, Olanipekun Olukoyede yace a shekarar 2019 mahaifiyarsa ta rasu. Yace ana kwana daya za'a binneta ya je gida dan halartar jana'izarta. Yace akwai gidansa da ya gina tun kamin ya fara aiki da EFCC kuma a wancan lokacin yana mukamin sakatarene a hukumar, yace yana zuwa gida sai ya tarar da shanu an kawo masa. Yace sannan kuma ya tarar da me gadinsa ya bashi wani akwati cike da Check na banki. Yace da ya shiga gida sai matarsa ta daga hannu sama tace sun godewa Allah, amma anan ya taka mata birki, yace nan suka zauna suka duba duka kudaden da aka aika masa wanda sun kai Naira Miliyan 500. Yace wadanda suka aika masa da wadanna kudade manyan ma'aikata ne da ministoci a ma'aikatun da suke bincike. Yace a sheka...
Kalli Hotunan yanda akawa wasu ‘yan luwadi da aka kama bulala 80 kowannensu a kasar Indonesia

Kalli Hotunan yanda akawa wasu ‘yan luwadi da aka kama bulala 80 kowannensu a kasar Indonesia

Duk Labarai
Kasar Indonesia ta zane wasu mutane maza 2 da aka kama suna aikata Luwadi. an zane su ne a gaban gwamman Mutane dan ya zama izina ga meyi ya daina. An yi wannan bulala ne a yankin Aceh na kasar a ranar Alhamis. Shi wannan yanki na Aceh ya kasance yana aiki ne da shari'ar Musulunci. Tun a watan Nuwamba da ya gabata ne mutane suka kamasu turmi da tabarya wanda daga nan ne suka kaisu kotun shari'ar Musulunci.
Za a ƙara alawus ɗin abinci na sojojin Najeriya zuwa naira 3,000

Za a ƙara alawus ɗin abinci na sojojin Najeriya zuwa naira 3,000

Duk Labarai
Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar janar Olufemi Oluyede ya bayyana rashin jin daɗinsa kan kuɗin alawus na kullum da ake RCA da ake ba sojojin Najeriya, wanda yanzu ake ba su naira 1,500. Da yake yi wa sojojin sashe na 81 jawabi a Legas, Oluyede ya ce za a ƙara alawus ɗin zuwa naira 3,000 daga wata mai zuwa. Baya ga ƙarin na RCA, babban hafsan ya ce rundunar sojin ƙasan Najeriya za ta fara ba sojoji lamunin kuɗi a kan kuɗin ruwa na kashi 3, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Ya ba sojoji shawarar su nemi bashin kuɗin, domin a cewarsa biyan ba zai zama musu matsala saboda babu ruwa mai girma a ciki. A game da tsarin gidaje, janar ɗin ya ce za su faɗaɗa shirirnsu na lamunin gidaje a Abuja da Ibadan da Jos da Fatakwal da Owerri da Akwa Ibom. Ya ce a tsarin,...
Sarkin Musulmin Najeriya ya buƙaci a fara duba watan Azumi daga gobe Juma’a

Sarkin Musulmin Najeriya ya buƙaci a fara duba watan Azumi daga gobe Juma’a

Duk Labarai
Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Muhamad Sa'ad Abubakar III na sanar da fara duba watan Ramadan daga gobe Juma'a 28 ga watan Sha'aban, wanda ya yi dai dai da 29 ga watan Janairun 2025. Cikin wata sanarwa da shugban kwamitin harkokin addini na fadar mai Alfarmar, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar ranar Alhamis ya ce idan aka ga watan a sanar da fadar mai alfarmar ta hanyar wasu lambobin waya da ya bayar. Sanarwar ta ƙara da cewa idan ba a ga watan a ranar Juma'a ba, to ranar Lahadi za ta kasance 1 ga watan Ramadan na wannan shekara. A ranar Laraba ne dai hukumomin Saudiyya suka da fara duba watan Ramadan ɗin daga gobe Juma'ar.
Kalli Bidiyon yanda Buhari ya koma gidansa na Kaduna da zama bayan kwashe kusan shekaru 2 a Daura

Kalli Bidiyon yanda Buhari ya koma gidansa na Kaduna da zama bayan kwashe kusan shekaru 2 a Daura

Duk Labarai
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gidansa na birnin Kaduna daga Daura na jihar Katsina, a cewar tsohon mai taimaka masa na musamman Bashir Ahmad. Buhari ya koma mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina tun bayan saukarsa daga mulki a watan Mayun 2023. Tsohon shugaban ya samu rakiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da Gwamnan Borno Babagana Zulum, da Gwamnan Kaduna Uba Sani. Akwai kuma sauran 'yansiyasa da tsofaffin jami'an gwamnati da suka tarɓi shugaban a gidan nasa. Kalli Bidiyon anan
Ana zargin Mawakin Najeriya, Burna Boy ya yaudari wannan budurwar me suna Sophia Egbueje yayi lalata da ita da sunan cewa zai sai mata motar Lamborghini amma bai cika mata alkawari ba

Ana zargin Mawakin Najeriya, Burna Boy ya yaudari wannan budurwar me suna Sophia Egbueje yayi lalata da ita da sunan cewa zai sai mata motar Lamborghini amma bai cika mata alkawari ba

Duk Labarai
Maganganu na ta yawo cewa, shahararren mawakin Najeriya, Burna Boy ya yaudari wata babbar yarinya da take wuta a birnin Legas me suna Sophia Egbueje inda yayi lalata ita da sunan zai sai mata motar Lamborghini amma bai cika mata alkawari ba. Yanda aka san labarin shine Sophia ta baiwa kawarta labarin abinda ya farune inda kuma hirar tasu ta watsu a kafafen sadarwa. A cikin muryar da aka nada, an ji Sophia na bayar da labarin cewa, sun gama rawa da Burna Boya a gidan rawa inda ya kaita gidansa ya kasheta da kalamai ita kuma ta yadda yayi lalata da ita da sunan zai sai mata motar. Tace daga baya ma kwata-kwata ya daina kiranta. Tuni dai akai ta mayar da martani kan lamarin inda da yawa suka rika mata dariya da kiranta marar wayau.

Ji Dalilai huɗu da suka sa Dangote ya rage farashin man fetur

Duk Labarai
"Duk shikashika da za su jawo rage farashin man fetur an cika su a yanzu," kamar yadda Farfesa Ahmed Adamu - masanin tattalin arzikin man fetur a jami'ar Nile University da ke Abuja - ya shaida wa BBC. Gasa Tun bayan sauye-sauyen da aka samu a kasuwar hada-hadar man fetur ta Najeriya, aka fara samun gasa tsakanin masu shigo da man da kuma matatar Dangote. Wannan gasa na ɗaya daga cikin dalilan da suka jawo raguwar farashin, ko kuma sanadiyyar hana farashin ya ƙaru. "Da ma amfanin gasa kenan. Shi Dangote yana ganin yanzu yana yin takara ne da wasu matatun man fetur ɗin na duniya, kuma babban burinsa shi ne ya riga kowa sayarwa," in ji Farfesa Ahmed. "Da zai yiwu ma, zai so ya haddasa yadda za a yi wasu 'yankasuwar ma su ji ba za su iya ci gaba da harkar ba, ta yadda duk masu ...
In Kaine Ya zaka yi: Kalli Bidiyon ya da mahaifi ya gayawa mijin diyarsa cewa ba dole bane sai matarsa ta masa girki ba

In Kaine Ya zaka yi: Kalli Bidiyon ya da mahaifi ya gayawa mijin diyarsa cewa ba dole bane sai matarsa ta masa girki ba

Duk Labarai
Bidiyon wani biki da ya wakana ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga mahaifi yana gayawa mijin diyarsa cewa ba lallai bane sai matarsa ta masa girki ba. https://www.youtube.com/watch?v=-987RYe_ff4 Wasu dai na ganin cewa wannan magana bai kamata ta fito daga bakin mahaifin ba musamman lura da cewa, al'adace mace tawa mijinta girki shi kuma ya fita neman Abinci.