Tuesday, December 16
Shadow
A yayin da Gobarar California kasar Amurka ke ci gaba da yaduwa, an hango wata mahaukaciyar Guguwa ta taho zata rura wutar ta kara shiga cikin gari dan ci gaba da kona gidaje

A yayin da Gobarar California kasar Amurka ke ci gaba da yaduwa, an hango wata mahaukaciyar Guguwa ta taho zata rura wutar ta kara shiga cikin gari dan ci gaba da kona gidaje

Duk Labarai
Wata mahaukaciyar guguwa da aka sakawa sunan Santa Ana winds dake gudun mita 45 duk awa ta doso garin Los Angeles dake ci da wuta. Ana tsammanin wannan guguwa zata rura wutar inda zata turata zuwa sassan garin dake da muhimmanci kamar gidan tarihin garin me suna J. Paul Getty Museum da kuma jami'ar University of California. Tuni dai aka fitar da sanarwa ga mutanen dake yankin da su fice daga gidajensu. Zuwa yanzu dai gobarar ta kone sama da gidaje dubu goma sha biyu da kuma yin sanadin kisan mutane 16 inda mutane 13 sun bace ba'a san inda suke ba.
Gobarar Amerika: Yawan wadanda suka mutu sun karu a yayin da mahaukaciya Gobarar ke ci gaba da yaduwa

Gobarar Amerika: Yawan wadanda suka mutu sun karu a yayin da mahaukaciya Gobarar ke ci gaba da yaduwa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa yawan wanda suka mutu a ci gaba da yaduwar mahaukaciyar gobarar garin Los Angeles na kasar Amurka na ci gaba da karuwa. Zuwa yanzu mutane 16 ne hukumomi suka tabbatar da cewa, sun mutu a gobarar. Kamfanin dillancin labaran AP yace biyar daga cikin wadanda suka mutu a unguwar Palisades ne sai 11 kuma a unguwar Eaton sannan kuma mutane 13 sun bace ba'a san inda suke ba. Zuwa yanzu gidaje dubu talatin da biyar ne suke cikin duhu babu wutar lantarki sanadiyyar gobarar. Sama da masu aikin kashe gobara dubu goma sha hudu ne ke ta aiki ba dare ba rana dan hana gobarar yaduwa. Hutudole ya kawo muku cewa, yawan wanda ke kashe gobarar sun yi kadan ta yanda saida aka fito da masu laifi daga gidan yari dan su taimaka
Gobarar California: Masu kashe gobara sun yi kadan, an fito da masu laifi daga gidan yari dan su taimaka

Gobarar California: Masu kashe gobara sun yi kadan, an fito da masu laifi daga gidan yari dan su taimaka

Duk Labarai
Masu kashe mahaukaciyar gobarar garin Los Angeles na jihar California a kasar Amurka sun yi kadan duk da yawansu ya kai dubu bakwai da dari biyar. Lamarin yayi kamari ta yanda saida aka fito da masu laifi da ake tsare dasu a gidan yari dan su taimaka. A rahoton NPR, tace masu laifi sama da 900 ne aka fito dasu daga gidan yari dan su taimaka a kashe gobarar da taki ci ta ki cinyewa. Hakanan rahotanni sun tabbatar da cewa, kasar Mexico dake makotaka da kasar ta Amurka ma ta aika da ma'aikatan kashe Gobara dan su taimaka a kashe mahaukaciyar gobarar. A baya dai, hutudole ya kawo muku cewa ana tsaka da fama da wannan gobara kuma sai ga girgizar kasa a jihar ta California. Sama da mutane 5000 ne suka shaida cewa sun ji motsin kasa San Francisco bay dake da nisan mil 350 da garin...
Gobarar Amurka: Yayin da suke tsaka da fama da mahaukaciyar gobara an kuma samun girgizar kasar a California ta kasar Amurka

Gobarar Amurka: Yayin da suke tsaka da fama da mahaukaciyar gobara an kuma samun girgizar kasar a California ta kasar Amurka

Duk Labarai
Girgizar kasa me maki 3.7 ta auku a jihar California ta kasar Amurka yayin da jihar ke kan fama da matsalar mahaukaciyar gobara data kone gidaje sama da dubu 10. Girgizar kasar ta farun da safiyar ranar Juma'a a San Francisco Bay kuma sama da mutane dubu biyar sun ce sun ji wannan girgizar kasa. Girgizar ta farune a garin dake da nisan mil 350 da garin Loas Angeles. A kalla mutane 16 ne hukumomi suka tabbatar sun mutu gobarar Los Angeles.
Talauci alamace ta yawan zunubi da rashin tsoron Allah>>Inji Pasto Komayya

Talauci alamace ta yawan zunubi da rashin tsoron Allah>>Inji Pasto Komayya

Duk Labarai
Pastor Korede Komaiya ya bayyana cewa, talauci alamace ta rashin tsoron Allah da yawan zunubi. Faston ya bayyana hakane ga mabiyansa a cikin cocinsa. Yace a rubuce yake cewa, wadanda suka bi Allah, zasu samu rayuwa ta jin dadi. Dan haka yace talauci alamace ta rashin tsoron Allah da yawan zunubi. Bidiyon da yake wannan magana ya yadu sosai a kafafen sda zumunta inda akai ta masa raddi. Yace yawanci ba'a sanin ainahin halin mutum sai idan ya samu kudi. Ya kara da cewa, yawanci talakawan da zaka ga suna kankan da kai, dama ce basu samu ba.
Obasanjo da Yakubu Gowon sun goyi bayan kungiyar su shekarau dake son kwace mulki daga hannun Tinubu  shekarar 2027

Obasanjo da Yakubu Gowon sun goyi bayan kungiyar su shekarau dake son kwace mulki daga hannun Tinubu shekarar 2027

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar su tsohon Gwamnan Kano kuma sanata Ibrahim Shekaru me suna LND dake son rikidewa zuwa ta siyasa, ta samu goyon bayan tsaffin shuwagabannin Najeriya, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo. Kungiyar dai na ci gaba da tuntubar manyan 'yan siyasa dga yankunan Kudu maso yamma da kudu maso kudu da kudu maso gabas dan cimma burinta. Shugaban kungiyar, Dr Umar Ardo ya tabbatar da komawarta ta siyasa dan samar da Jam'iyya me karfi da hadin kai da zata karade kowane yanki a kasarnan. Duka shuwagabannin biyu, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo sun yi na'am da wannan tafiya inda suka bayar da shawarar mayar da ita ta kasa baki daya.
A karin farko, Shugaba Tinubu ya sakawa dokar haramtawa sojojin Najariya yin Luwadi, Madigo da shan giya

A karin farko, Shugaba Tinubu ya sakawa dokar haramtawa sojojin Najariya yin Luwadi, Madigo da shan giya

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa dokar haramta yin luwadi, Madigo da daudu ko saka kayan mata, da yin zane a jiki wanda aka fi sani da Tattoo a gidan soja. Hakanan kuma dokar ta haramtawa sojojin huda jikinsu, irin su hudar kunne ko hanci da sauransu, sannan ba'a yadda soja ya sha giya a bakin aiki ko kuma ko da baya bakin aiki. Wannan na kunshene a cikin sabuwar dokar aikin soja da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanyawa hannu a watan Disamba na shekarar 2024. Hakanan sabuwar dokar ta haramtawa sojojin shiga kungiyar asiri ko kuma harkar siyasa.
Gwanin Ban Tausai: Ji yanda kananan ‘yan matan da aka yi gàrkùwà dasu aka sakosu suka koma yin karuwanci saboda ‘yan Bìndìgàr sun saba musu da làlàtà

Gwanin Ban Tausai: Ji yanda kananan ‘yan matan da aka yi gàrkùwà dasu aka sakosu suka koma yin karuwanci saboda ‘yan Bìndìgàr sun saba musu da làlàtà

Duk Labarai
Lawan Wakilbe, kwamishinan ilimi, da kimiyya da fasaha, da kirkire-kirkire a Jihar Borno, ya yi gargadi kan yawaitar karuwanci tsakanin tsofaffin wadanda kungiyar B0k0 Hàràm ta sace. TheCable ta rawaito cewa Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da Hamsatu Allamin, shugabar cibiyar Allamin Foundation for Peace, ta kai masa a jiya Juma’a a Maiduguri. Wakilbe ya ce an fi samun irin waɗannan matsalolin a ƙananan hukumomin Bama, Banki, da Gwoza. Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda Boko Haram din su ka saki na fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata da su saboda sun fuskanci hakan tun a lokacin da raunin da su ke hannun ƴan ta’addan. Ya yi kira ga haɗa hannu waje ɗaya domin ceto ire-iren yaran.