Saturday, December 13
Shadow
Kalli Bidiyo da Hotuna: Kungiyar B0k0 Hàràm ta kaiwa Sansanin Sojojin Najariya hari ta kashe sojoji 7

Kalli Bidiyo da Hotuna: Kungiyar B0k0 Hàràm ta kaiwa Sansanin Sojojin Najariya hari ta kashe sojoji 7

Duk Labarai
Kungiyar ISWAP data balle daga jikin B0K0 Hàràm ta kaiwa sansanin sojojin Najariya hari a garin Damboa dake jihar Borno. Maharan sun kona gidaje da motocin sojojin da kashe akalla sojoji 7. Rahoton Sahara Reporters yace maharan sun shafe awanni 2 suna cin karensu ba babbaka a sansanin sojojin. Rahoton yace harin ya farune ranar 4 ga watan Janairu, watau Asabar data gabata. Wani soja yace zuwa yanzu sun gano gawarwakin Sojoji 7, kuma ya kara da cewa an kai musu harinne da misalin karfe 4 na safe. Kalli Bidiyon anan
Sojoji sun mamaye garin Shinkafi saboda barazanar Bello Turji

Sojoji sun mamaye garin Shinkafi saboda barazanar Bello Turji

Duk Labarai
Kwanaki kadan bayan da gawurtaccen dan ta'adda, Bello Turji ya kaiwa wasu unguwannin garin shikafi hari, sojoji sun mamaye garin dan samar da tsaro. Yaran Bello Turji sun kai hari a kasuwar garin inda suka Kashe mutane 2 da yin garkuwa da wasu da dama. Turji dama yayi Alkawarin kaiwa garin Shinkafi hari idan ba'a saki wasu 'yan uwansa da aka kama ba. Turji ya kuma tare motoci biyu ya yi garkuwa da mutanen ciki ya koma mota daya.
Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: Gobara a gidan babban Sakataren (Perm. Sec.) na ma’aikatar Matasa da wasanni ta jahar Sokoto Muhammad Bello Yusuf tayi sanadiyyar rasuwar matarsa da ‘ya’ya 3 da mai aiki ɗaya

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: Gobara a gidan babban Sakataren (Perm. Sec.) na ma’aikatar Matasa da wasanni ta jahar Sokoto Muhammad Bello Yusuf tayi sanadiyyar rasuwar matarsa da ‘ya’ya 3 da mai aiki ɗaya

Duk Labarai
Gobara a gidan babban Sakataren (Perm. Sec.) na ma'aikatar Matasa da wasanni ta jahar Sokoto Muhammad Bello Yusuf tayi sanadiyyar rasuwar matarsa da 'ya'ya 3 da mai aiki ɗaya. Muna rokon Allah Ya gafarta musu, Ya kyautata tamu idan tazo. Amin ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR:AN KAMMALA SALLAR JANA'IZAR ƊIYAR SSG NA JAHAR SOKOTO Alhaji BELLO SIFAWA kuma Matar PERMANENT SECRETARY na MINISTRY of Youths and Sport Alhaji MUHAMMAD YUSUF BELLO, TARE da 'YA'YANTA UKKU da MAI AIKINSU WANDA DUKKANSU SUKA RASU a CIKIN IFTILA'I NA GOBARA. UBANGIJI ALLAH YA ya JIKANSU DA RAHAMA KUMA ya GAFARTA MASU BAKI DAYA. ALLAH YA BADA HAƘURI
Kotu ta bayar da belin matar datawa dan shugaban kasa, Seyi Tinubu Barazana akan Naira Miliyan 10

Kotu ta bayar da belin matar datawa dan shugaban kasa, Seyi Tinubu Barazana akan Naira Miliyan 10

Duk Labarai
Kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin matar datawa dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da shugaban 'yansandan Najeriya barazanar kisa akan Naira Miliyan 10. Alkalin kotun, Justice Emeka Nwite ya bayyana cewa kuma matar da aka gurfanar Olamide Thomas sai ta gabatar da wanda zai tsaya mata. Kuma dole ya kasance yana zaune a inda kotun ke da hurumi.
Aikin Ofis yayi karanci a kasar China, Matasa masu digiri na biyu dana uku watau Masters da PhD sun koma tuka motocin haya da aiki da gidajen abinci da sauran sana’o’in hannu dan dogaro da kai

Aikin Ofis yayi karanci a kasar China, Matasa masu digiri na biyu dana uku watau Masters da PhD sun koma tuka motocin haya da aiki da gidajen abinci da sauran sana’o’in hannu dan dogaro da kai

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar China na cewa, aikin Ofis yayi karanci a kasar inda matasa da yawa da suka kammala digiri na biyu dana uku watau Masters da PhD sun rungumi kananan sana'o'i irin su tukin motocin haya da aiki a gidajen abinci da saurans. Rahoton BBC yace wasu masu PhD sun koma aikin goge-goge a ma'aikatu inda wasu ke aikin kai sakonni gidaje. Wani matashi dan shekaru 25 da majiyar tamu ta yi hira dashi me suna Sun Zhan ya bayyana cewa ya kammala Digirin Masters a fannin Kididdigar kudi, watau Finance inda yayi fatan yin aiki da babban kamfani dake hadahadar kudi ko banki, yace amma ya nemi irin aikin da yake so bai samu ba. Yace yanzu yana aiki ne a wani gidan abinci dake birnin Nanjing inda yake mikawa mutane irin abincin da suke so idn sun shiga gidan abincin. Rahoton yac...
‘Yan Najeriya na son mu, ko bamu yi hadaka da kowace Jam’iyya ba zamu iya cin zaben 2027>>Inji Labour Party

‘Yan Najeriya na son mu, ko bamu yi hadaka da kowace Jam’iyya ba zamu iya cin zaben 2027>>Inji Labour Party

Duk Labarai
Jam'iyyar Labour party ta bayyana cewa ta na da karbuwa a wajan talakawa ta yanda ko da bata hade da kowace Jam'iyya ba zata iya yin nasara a zaben shekarar 2027. Jam'iyyar tace irin nasarar data samu a shekarar 2023 alamace dake nuna cewa zata iya yin nasara a zaben me zuwa ba tare da hadaka da kowa ba. Sakataren yada labarai na Jam'iyyar, Obiora Ifoh ne ya bayyana haka a ganawarsa da jaridar Punchng. Yace babu wata yarjejeniyar hadaka tsakanin Jam'iyyarsu da NNPP ta Kwankwaso ko PDP ta Atiku. Ya kara da cewa babu wanda ya gayyacesu dan yin wata maganar hadaka. A baya dai, shima Kwankwaso ya musanta cewa sun yi hadaka da Atiku dan tunkarar zaben shekarar 2027.
A wannan satin za’a fara daukar man fetur daga matatar Mai ta Fatakwal

A wannan satin za’a fara daukar man fetur daga matatar Mai ta Fatakwal

Duk Labarai
Idan dai ba wani canji aka samu ba, A cikin wannan satin ne ake sa ran 'yan kasuwa zasu fara daukar man fetur daga matatar mai ta Fatakwal. Me yada labarai na kungiyar 'yan kasuwar man fetur din ta PETROAN Joseph Obele ne ya bayyana haka a wata ganawa da yayi da jaridar Punchng. Ya bayyana cewa, tun bayan da Matatar man ta dawo aiki a watan Nuwamba, gidajen mai na NNPCL ne kawai take baiwa man amma suma suna sayen manne daga gurin NNPCL wanda ake shigo dashi daga kasar waje. Ya koka da cewa amma ana sayar musu mai da tsada a fatakwal fiye da yanda NNPC din ke sayar da man a Legas inda yayi kiran a rika sayar musu a farashi daya.
Bidiyo da hotuna masu daukar hankali, Sabuwar cuta ta sake bullowa daga kasar China, hankalin Duniya ya tashi, Najeriya ma ta fara killace mutanen dake zuwa daga kasar China a filin Jirgi

Bidiyo da hotuna masu daukar hankali, Sabuwar cuta ta sake bullowa daga kasar China, hankalin Duniya ya tashi, Najeriya ma ta fara killace mutanen dake zuwa daga kasar China a filin Jirgi

Duk Labarai
Wata sabuwar cuta ta sake bulla a kasar China me suna HMPV Virus. Cutar kamar dai Corona Virus itama na da alaka da sarkewar numfashi amma tafi kama kananan yara 'yan kimanin shekaru 14. A kasar Chinan, an dawo da irin dokar da aka yi lokacin da cutar CoronaVirus tazo, watau saka Face Mask da yin nesa-nesa da juna da sauransu. Saidai wani abin jin dadi shine wannan sabuwar cutar bata kai Coronavirus illa ba. A ranar Lahadi, Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar fara daukar matakin killacewa da kuma binciken lafiya ga dukkan mutanen da suka shigo Najeriya daga kasar China. Wannan cuta dai na zuwane shekaru 5 bayan bullar cutar Coronavirus. A kasar China, Asibitoci aun cika da mutanen da suka kamu da wannan sabuwar cuta inda ake ta yada hotuna da bidiyo a kafafen sada zu...
Kwamishina a jihar Kano ya ajiye muƙamin sa

Kwamishina a jihar Kano ya ajiye muƙamin sa

Duk Labarai
Kwamishinan Ma'aikatar Sanya Idanu a ayyukan gwamnati, Mohammed Diggol ya ajiye aiki. Labarin hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa a Ranar Lahadi a wata sanarwa da ya fitar a Kano. Tun da dare, Diggol shi ne Kwamishinan Ma'aikatar Sufuri kafin daga bayan gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya canja masa ma'aikata. Sai dai kuma kwanaki kadan da bashi sabuwar ma'aikatar Sa'id Diggol ya sanar da ajiye aiki a matsayin Kwamishina a gwamnatin Abba. Dawakin-Tofa ya ce Gwamna Abba ya karbi takardar ajiye muƙamin, inda ya kuma godewa Diggol tare da yi masa fatan alheri s rayuwarsa.