Tuesday, December 16
Shadow
Za’a kara farashin kiran waya daga sayen data>>Gwamnatin Tarayya

Za’a kara farashin kiran waya daga sayen data>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kwanannan za'a kara kudin kiran waya daga sayen data. Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Bosun Tijani ne ya bayyana haka. Ya bayyana hakane a wajan wani taron masu ruwa da tsaki ranar Laraba a Abuja. Yace kamfanonin sadarwa na neman a basu damar kara farashin kudin kira dana sayen data da kaso 100 bisa 100 amma ba za'a yadda da hakan ba. Yace za'a yi karin inda za'a kare kowane bangare tsakanin kwastomomi da Kamfanin. Yace ana jiran hukumar NCC ne dan ta fitar da tsarin yadda karin zai kasance.
Yansandan Najeriya sun kama saurayin da ya haɗa baki da budurwarsa don ‘damfarar’ iyayenta

Yansandan Najeriya sun kama saurayin da ya haɗa baki da budurwarsa don ‘damfarar’ iyayenta

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Delta da ke kudancin ƙasar ta kama saurayi da budurwarsa bisa zargin haɗa baki domin damfarar iyayen yarinyar. Da yake gabatar da matasan da aka ɓoye fuskokinsu a wani ofishin 'yansanda, kakakin rundunar SP Bright Edafe ya ce matasan sun tsara cewa saurayin ya kira mahaifan budurwar ya ce ya sace ta kuma nemi kuɗin fansa. Ya ƙara da cewa sun yi nasarar kama matasan ne bayan mahaifiyar budurwar ta kai musu rahoton sace 'yar tata. A cewarsa: "A ranar 30 ga watan Disamba Princess mai shekara 21 ta je gidan saurayinta Prince kuma ta ba shi shawarar cewa su haɗa baki don neman kuɗi a wajen iyayenta. "Prince ya kira iyayen nata kuma ya ce musu ya yi garkuwa da ita, har ma ya nemi kuɗin fansa naira miliyan biyu." Matashiyar wadda ta yi maga...
Ƴanbindiga sun kashe aƙalla mutum 20 a Zamfara

Ƴanbindiga sun kashe aƙalla mutum 20 a Zamfara

Duk Labarai
Rahotanni na cewa ana ci gaba da samun ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga A jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan sauƙin da aka samu a ƴan watannin nan. Wasu mahara sun shiga garuruwa da dama na ƙaramar hukumar Maru, inda suka kashe aƙalla mutum 20 tare da yin garkuwa da gommai. Waɗanda BBC ta zanta da su sun ce ƴan bindigar sun shiga garuruwan ne da motoci inda suka kwashi kayan abinci da sauransu. Wannan dai na zuwa ne bayan nasarorin da sojojin Najeriya suka samu na hallaka wasu daga cikin shugabannin ƴan bindigar a jihar ta Zamfara.
Mutanen da suke juya gwamnatin Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Dalung

Mutanen da suke juya gwamnatin Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Dalung

Duk Labarai
Tsohon ministan matasa da wasanni a Najeriya a zamanin shugaba Buhari, Solomon Dalung, ya ce mutanen da ke juya gwamnati ta bayan fage waɗanda ake kira 'cabal' na mulkin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu sun fi na zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari haɗari. Dalung ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na tashar Channels a ranar Talata, inda ya ce a zamanin mulkin Buhari, wasu mutane sun riƙa juya akalar gwamnatin. Sai dai ya ce waɗanda suka juya mulkin Buhari ba su da ilimi da wayewa sosai, amma waɗanda suke juya gwamnatin Tinubu sun fi ilimi da sanin mulki kuma sun fi tarin buri. Dalung ya ce, "lallai akwai masu juya gwamnati ta bayan fage a zamanin Buhari. Amma mutanen wancan lokacin ba su da ƙwarewa sosai a kan mulki da siyasa, don haka tasirin ya taƙaitu. Amma...
EFCC ta tsare jami’anta 10 bisa zargin satar kayan aiki

EFCC ta tsare jami’anta 10 bisa zargin satar kayan aiki

Duk Labarai
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta tsare jami'anta 10 game da zargin hannunsu a ɓacewar wasu kayayyakin aiki. An kama jami'an ne a makon da ya gabata, kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafukan zumunta ta bayyana yau Laraba. "Jami'an da aka kama makon da ya gabata bisa umarnin Shugaba Ola Olukoyede, na amsa tambayoyi game da ɓatan wasu kayayyakin aiki," in ji kakakin EFCC Dele Oyewale. Wannan sanarwa na zuwa ne bayan hukumar ta sanar da korar jami'an nata 27 a shekarar da ta gabata saboda "zambatar mutane" da sauran laifuka.
Bankin China ya bai wa Najeriya rancen kuɗin gina titin jirgi kasa daga Kano zuwa Kaduna

Bankin China ya bai wa Najeriya rancen kuɗin gina titin jirgi kasa daga Kano zuwa Kaduna

Duk Labarai
Bankin raya ƙasa na China ya bai wa Najeriya rancen dala miliyan 254.76 domin gina titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna. Sanarwar da bankin ya fitar na zuwa ne gabanin ziyarar ministan harkokin wajen China a Najeriya cikin mako mai zuwa. Minista Wang Yi zai isa Najeriya domin ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, da sauran manyan jami'an gwamnatin tarayya tun daga ranar Laraba. Aikin layin dogon mai tsawon kilomita 203, ana sa ran zai laƙume dala miliyan 973 amma ya dakata saboda ƙarancin kuɗi. "Idan aka kammala shi, layin dogon zai haɗe Kano, mai muhimmanci a arewacin Najeriya, da kuma Abuja babban birnin ƙasar, inda zai ba wa mutane damar yin tafiya mai sauƙi," a cewar sanarwar da bankin ya wallafa a shafinsa na intanet. Tun da farko gwamnatin Najeriya ta ce Exim Bank na...
Daga almajiranci na zama shugaban NNPC – Kyari

Daga almajiranci na zama shugaban NNPC – Kyari

Duk Labarai
Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, Mele Kyari ya ce yana godiya ga Allah da ɗaga darajarsa daga wanda ya taɓa karatu a makarantar tsangaya ta amajirai har ya kai ga zama shugaban NNPCL a Najeriya. Mele Kyari ya bayyana haka ne a shafinsa na X, a saƙonsa na godiya ga Allah bisa cika shekara 60 a duniya. A cewarsa, "cikin ikon Allah, a yau nake cika shekara 60 a duniya, duk da na riga na kai tun a baya idan aka yi la'akari da watan musulunci. Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar zama shugaban kamfanin makamashi mafi girma a Afirka." Kyari ya ce yana godiya ga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ma Najeriya bisa wannan damar da ya samu. "Idan na waiwayi baya, nakan tuna gwagwarmayar da na sha. Nasarori da ƙalubale waɗanda Allah ne kaɗ...
ICPC ta maka tsohon kwamishinan El-Rufai a kotu

ICPC ta maka tsohon kwamishinan El-Rufai a kotu

Duk Labarai
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa ta Najeriya ICPC ta maka kwamishina a tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna, Bashir Saidu a kotu bisa zargin almundahanar kuɗi. Jami'in shari'a na hukumar ICPC, Osuobeni Akponimisingha ne ya gabatar da ƙarar a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Talata, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito. Takardar ƙarar mai lamba FHC /KD/IC/ 2025, ta nuna cewa an maka Bashir Sa'idu a kotun ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka danganci almundahana da rashawa. A wani rahoto da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar a bara, ta zargi tsohuwar gwamnatin da almundahanar sama da naira biliyan 423 na jihar.
Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

Duk Labarai
Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai kan sojojinta a jihar Borno. A wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ya ce an kashe sojoji guda shida, sannan wani kwamandan ƴan sa-kai ya jikkata. Sai dai Buba ya ƙara da cewa a gumurzun, sojojin sun samu nasarar kashe ƴan Boko Haram 34, sannan sun ƙwato wasu makamai. Wannan ne karo na biyu a cikin wata biyu da mayaƙan Boko Haram suka kashe sojoji a Najeriya. A watan Nuwamban 2024, an kashe gomman sojoji a wasu hare-hare da mayaƙan suka kai kan sojoji a ƙauyen Kareto da ke ƙaramar hukumar Mobbar da ke jihar Borno.
An kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus na naira 77,000 — NYSC

An kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus na naira 77,000 — NYSC

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ce an kusa fara biyan masu yi wa ƙasar hidima alawus na naira 77,000 da aka amince za a riƙa biyansu na wata-wata. Darakta-janar na NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ya bayyana haka a ranar Talata a wata sanarwa da kakakin NYSC, Caroline Embu ta fitar kamar yadda tashar Channels ta ruwaito. Ahmed ya ce zai mayar da hankali kan jin daɗin masu yi wa ƙasa hidima, inda ya ƙara da cewa tuni shirye-shirye sun kammala domin fara biyan sabon alawus ɗin. An dai ƙara alawus ɗin ne tun bayan da gwamnatin Najeriya ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata a ƙasar.