Monday, December 15
Shadow

Maganin yawan fitsari

Magunguna
Yawan fitsari matsala ce dake sa mutum ya rika yin fitsari fiye da kima, idan ya zamana mutum na yin fitsari fiye da sau 8 a rana, za'a iya cewa yana yawan fitsari. Wannan matsala zata iya faruwa ga kowa amma tafi yawa a tsakanin mutanen da suka zarta shekaru 70 a Duniya, da mata masu ciki, ko bayan fara shan wani magani, ko kuma wani me wata cuta ta musamman. Yawan Fitsari na iya zama alamar daukar ciki ga mace, sannan yana iya zama alamar ciwon sugar wanda ake cewa diabetes ko ciwon mafitsara, da sauransu. Masana kiwon lafiya sunce ba matsala bace idan mutum ya tashi da dare yayi fitsari, sun ce idan mutum ya kai shekaru 40 zuwa 50, to zai iya fuskantar tashi cikin dare yayi fitsari sau daya. Idan kuma mutum yana tsamanin shekaru 60 zuwa 70, zai iya rika tashi cikin dare yana yi...
Isra’ila ta lalata asibiti na ƙarshe a arewacin Gaza – WHO

Isra’ila ta lalata asibiti na ƙarshe a arewacin Gaza – WHO

Duk Labarai
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sojojin Isra'ila sun lalata babbar cibiyar lafiya ta ƙarshe da ta rage a arewacin Gaza. WHO ta ce rahotanni sun bayyana cewa an ƙona wasu muhimman sassa da aka lalata a harin da aka kai ranar Juma’a a asibitin Kamal Adwan. Hukumar ta kuma nuna matuƙar damuwa game da lafiyar majinyatan da aka tilasta musu barin asibitin. Isra'ila dai ta ce Hamas na amfani da asibitin ne a matsayin cibiyar ba da umarni - amma ba ta gabatar da wasu hujjojin da ke gaskanta hakan ba.
Kudin shigar da Najeriya ta samu a shekarar 2023 sunfi yawan kudin da Gwanati tace ta kashe amma duk da haka an ce an ciwo bashi>>Sule Lamido

Kudin shigar da Najeriya ta samu a shekarar 2023 sunfi yawan kudin da Gwanati tace ta kashe amma duk da haka an ce an ciwo bashi>>Sule Lamido

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta PDP, Sule Lamido ya zargi gwamnatin shugaban Najeriya, Bola Tinubu da ta Muhammadu Buhari da rashin gaya wa 'yan ƙasa haƙiƙa gaskiya game da gwamnatocinsu. Cikin wata hira da BBC, toshon gwamnan na jihar Jigawa ya ce gwamnatocin biyu sun fifita farfaganda a maimakon faɗa wa 'yan ƙasa gaskiyar halin da ƙasar ke ciki. Sule Lamido ya ce a shekarar da ta gabata gwamnatin Tinubu ta yi kasafin kuɗi na kusan Tiriliyan 30, kuma hukumomin tattara haraji na ƙasar sun ce sun tara naira tiriliyan 50, amma duk da haka gwamnatin Tinubu ta buƙaci cin bashin domin cike giɓi a kasafin kuɗin na shekarar da ta gabata. ''Ka yi kasafin kuɗinka da za ka kashe a duka shekarar a kan naira tiriliyan 30, sai kuma ka samu kuɗin shiga naira tiriliy...
‘Gwamnatin tarayya za ta yi cikakken bincike kan harin ƙauyukan Silame’

‘Gwamnatin tarayya za ta yi cikakken bincike kan harin ƙauyukan Silame’

Duk Labarai
Gwamnatain tarayya ta alƙawarta gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kai ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtawa a ƙaramar hukumar Sileme da ke jihar Sokoto. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X, gwamnan jihar Ahmad Aliyu, ya ce ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Bello Matawalle ne ya tabbatar da hakan a lokacin ziyarar jaje da ya kai jihar ranar Juma'a. A ranar 25 gatan Disamba ne wani hari da jiragen sojin Najeriya suka ''kai wa Lakurawa'' ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 10 a ƙauyukan. ''Gwamnatin tarayya ta tabbatar mana cewa za ta gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa lamarin domin yi wa waɗanda lamarin ya shafa adalci'', kamar yadda gwamnan ya wallafa. Tuni dai rundunar sojin ƙasar ta musanta hannu a kisan fararen hulan, inda ta ce bama-baman da ...
Kasar Nijar ta koro karin ‘yan Najeriya 392 zuwa gida

Kasar Nijar ta koro karin ‘yan Najeriya 392 zuwa gida

Duk Labarai
Kasa da mako daya bayan da kasar Nijar ta dawo da 'yan Najeriya su 310 zuwa gida Najeriya, kasar ta sake taso keyar wasu karin mutane 392 zuwa Najeriya. Hakan ya kawo jimullar 'yan Najeriya da aka dawo dasu gida daga kasar Nijar zuwa 702 a cikin sati daya. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki a lamarinne suka tarbi 'yan Najeriyar da aka koro daga Nijar a Titin Airport Road dake Kano. Hukumar ta NEMA ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na X.
Tsageran ESN Sun kashe sojojin Najeria biyu daya ya bace, sun kuma tsere da makaman sojojin

Tsageran ESN Sun kashe sojojin Najeria biyu daya ya bace, sun kuma tsere da makaman sojojin

Duk Labarai
Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojin ta 2 bayan harin da kungiyar ESN dake karkashin kungiyar IPOB ta kai mata. A sanarwar data fitar ranar Asabar, Hukumar sojojin ta bayyana cewa, lamarin ya farune a garin Osina dake karamar hukumar Ideator ta Arewa dake jihar Imo a yayin da wata tawagar sojojin ke dawowa daga wani dauki da suka kai a yankin Osina bayan kiran da aka musu cewa kungiyar ta ESN ta kai hari garin. Hakanan sanarwar tace sojojin sun fafata da ESN a yankin Nkwachi inda suka kashe mutum daya daga ciki sauran suka tsere sannan kuma an kwato bindiga daya aga hannunsu.
A karin Farko a Tarihi, Sunan Muhammad ya shiga cikin sunaye 10 na farko da aka fi sakawa Jarirai sabbin haihuwa a birnin New York City na kasar Amurka

A karin Farko a Tarihi, Sunan Muhammad ya shiga cikin sunaye 10 na farko da aka fi sakawa Jarirai sabbin haihuwa a birnin New York City na kasar Amurka

Duk Labarai
A karin farko a tarihin birnin New York na kasar Amurka, sunan Muhammad ya shiga cikin sunaye 10 na farko da aka fi sakawa jarirai sabbin haihuwa a birnin. Sunan Muhammad shine ya zo a matsayi na 9 da aka fi sakawa jarirai a birnin na new York city a shekarar 2023 da ta gabata. Ba a birnin New York City bane kadai aka fi sakawa jarirai sunan na Muhammad, hadda ma biranen kasar Ingila da Wales sunan Muhammad na kan gaba da aka fi sakawa jarirai sabbin haihuwa. Sunayen Emma da Liam ne suka fi shahara a birnin na New York City inda aka sakawa jarirai mata 382 sunan Emma sannan aka sakawa jarirai maza 743 sunan Liam. Wadannan sunaye sun dade suna a matsayi na daya na sunayen da aka fi sakawa jarirai maza da mata a birnin inda sunan Emma tun shekarar 2017 shine a matsayi na daya da ...
Bidiyon Wata Minista ya bayyana tsiràrà

Bidiyon Wata Minista ya bayyana tsiràrà

Duk Labarai
Bidiyon ministar mata da yara da tallafi ta kasar Fiji, MP Lynda Tabuya ya fita inda aka ganta tsirara haihuwar uwarta. Ministar tace wannan bidiyo ta yi shi ne ta aikawa mijinta amma bata da masaniyar yanda aka yi ya watsu a kafafen sada zumunta. Tuni dai Firaiministan kasar, Sitiveni Rabuka ya sauke ta daga mukaminta dalilin wannan badakala. Saiai tace ita bata aikata laifin komai ba dan kuwa mijinta ta aikawa bidiyon amma bata san yanda aka yi bidiyon ya watsu a kafafen sada zumunta ba. Ta gargadi masu watsa bidiyon da su yi hankali dan tasa a yi bincike dan gano wanda suka watsa shi kuma zata dauki hukuncin shari'a akansu. Mataimakin Kwamishinan 'yansandan kasar, Livai Driu ya bayyana cewa, suna kan binciken lamarin bayan korafin da Ministar ta kai musu.