Karanta Munanan Abubuwan da suka faru a Najeriya lokacin da Tinubu ke ƙasashen Turai
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya koma Abuja daga nahiyar Turai bayan ziyarar aiki da ya kai biranen Paris da Landan.
Shugaba Tinubu ya isa filin jirgi na Nnamdi Azikwe da yammacin ranar Litinin, inda wasu manyan jami'an gwamnati suka tarbe shi.
A cewar fadar shugaban kasa, dalilan da suka sanya shugaban ya gudanar da wannan ziyarar sun haɗa da yin nazari kan wasu muhimman cigaban da gwamnatinsa ta samu.
''Zai yi amfani da wannan ziyarar domin yin nazari kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke gudanarwa da kuma tsara yadda za a ɓullo da wasu sabbin shirye-shirye gabanin cikarsa shekara biyu kan karagar mulki," a cewar fadar shugaban ƙasa.
A wani ɓangare kuma yayin da ake murnar samun ƙaruwa a asusun gwamnatin Najeriya na ƙasashen waje a babban bankin ƙasar, abubuwa da dama sun ...








