Saturday, December 6
Shadow
Sanata Godswill Akpabio ya gargadi Minista da cewa ya rufawa kansa Asiri kada yayi magana akan Trump

Sanata Godswill Akpabio ya gargadi Minista da cewa ya rufawa kansa Asiri kada yayi magana akan Trump

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai Sanata Godswill Akpabio ya gargadi Kingsley Udeh (SAN) da cewa, kada ya sake ya amsa tambaya akan shugaban kasar Amirkaz Donald Trump. Ya bayyana masa hakane ranar Alhamis yayin tantance shi dan bashi ministan kimiyya da Fasaha. Bayan da Kingsley Udeh (SAN) ya gabatar da kansa a gaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya bayar da damar a masa tambayoyi amma ya gargadeshi da cewa, kada ya amsa tambaya akan shugaban kasar Amirka, Donald Trump. A karshe dai majalisar ta amince da nadin Kingsley a matsayin Ministan. Shidai Godswill Akpabio a baya yace bai isa ya baiwa Trump amsa ba sai abinda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace. trump dai na barazanar kawo Khari Najeriya.
‘Yan Najeriya sai kun yi Hakuri gaskiya nasan ba zaku ji dadin matakin da zan dauka ba amma ya zama dole>>Inji Shugaban kasar Amurka, Donald Trump

‘Yan Najeriya sai kun yi Hakuri gaskiya nasan ba zaku ji dadin matakin da zan dauka ba amma ya zama dole>>Inji Shugaban kasar Amurka, Donald Trump

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gayawa 'yan Najeriya cewa, su yi Hakuri domin matakin da zai dauka ba zasu ji dadinsa ba. Saidai yace ya zama dole su kawo Khari Najeriya saboda abinda akewa Kiristoci na Khisan Khiyashi. Yace ba Najeriya kadai ba hadda ma sauran kasashen Duniya dik inda suka ji ana Muzgunawa Kiristoci ba zasu bari ba. Trump ya bayyana hakane a sabon sakon da ya saki da yammacin jiya.
Kalli Bidiyo: Matashi Tsulange da a baya aka kamashi saboda yin Bidiyo a cikin makara da kusa da whuta yana cewa ya matsu yace zai ci gaba da yin Bidiyonsa

Kalli Bidiyo: Matashi Tsulange da a baya aka kamashi saboda yin Bidiyo a cikin makara da kusa da whuta yana cewa ya matsu yace zai ci gaba da yin Bidiyonsa

Duk Labarai
Matashi dan Kano me amfani da sunan Tsulange wanda a baya ya rika Bidiyo a kusa da cikin makara da kusa da wuta yana cewa ya matsu ya dawo. A Bidiyon daya saki, matashin yace, an hanashi yin Bidiyonsa bayan ya sayo makara Naira dubu 30 sannan ya siyo likkafani Naira dubu 10. Yace zai ci gaba da yin Bidiyonsa amma zai daina cewa ya matsu. A baya dai an kama matashinnaka masa Nasiha bayan da ya rika cewa ya matsu a kusa da wuta da cikin Makara. https://www.tiktok.com/@tsulange89/video/7569325959648644370?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7569325959648644370&source=h5_m&timestamp=1762423621&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aF...
Kalli Bidiyon: Yanda wani matashi ya zo tada Janareta yaki tashi amma yana kiran sunan Shehu sai Injin ya tashi

Kalli Bidiyon: Yanda wani matashi ya zo tada Janareta yaki tashi amma yana kiran sunan Shehu sai Injin ya tashi

Duk Labarai
Wannan wani matashine da ya dauki hankula sosai bayan da ya je tayar da Janareta amma Janaretan ya ki tashi. Saidai yana kiran sunan Shehu sai Injin ya tashi. Ya maimaita abin dan ya nuna ba sa'a ko dace bane inda abin ya baiwa mutane mamaki sosai. https://www.tiktok.com/@zeebeautiful3/video/7569165659955940628?_t=ZS-91AaEwWAW6T&_r=1
Sanatan Amurka ya gabatar da kudirin dokar Hukunta wasu ‘yan Najeriya da jihohin Arewa 12 dake amfani da dokar shari’ar Musulunci

Sanatan Amurka ya gabatar da kudirin dokar Hukunta wasu ‘yan Najeriya da jihohin Arewa 12 dake amfani da dokar shari’ar Musulunci

Duk Labarai
Sanatan Amurka, Ted Cruz wanda shine ya kai kudirin dokar da ta saka Najeriya cikin jerin kasashen da Amurkar ke sakawa ido bisa zargin anawa Kiristoci khisan Kyiyashi a yanzu kuma ya sake kai wani Kudirin dokar majalisar kasar. Ted Cruz ya godewa shugaban kasa, Donald Trump kan matakin da ya dauka akan Najeriya inda yace a baya lokacin mulkin Trump na farko, ya saka Najeriya cikin kasashen da Amurka zata rika sakawa ido amma tsohon shugaban kasar, Biden ya cireta. Saidai yace ya ji dadi da a yanzu Trump ya dawo da Najeriya cikin kasashen da Amurka zata rika sakawa ido. Yace a yanzu ya sake gabatar da wata sabuwar kudirin doka da zata hukunta wasu 'yan Najeriya da ake zargi da hannu wajan Muzgunawa Kiristoci sannan ya ce zakuma a dauki hukunci kan jihohi 12 na Arewa dake amfani da...
Abubuwa na ci gaba da kankama: Sojojin Amurka sun mikawa shugaba Trump kalar khare-kharen da suke son kawowa Najeriya

Abubuwa na ci gaba da kankama: Sojojin Amurka sun mikawa shugaba Trump kalar khare-kharen da suke son kawowa Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar Amurka sun mikawa shugaban kasar kalar Hare-haren da suke son kawowa Naira. Sun mika masa tsare-tsaren hare-haren guda biyu, na farko yanayi ne me tsanani, sai matsaka kaici sai kuma me sauki. Yanayi me tsanani shine kawo jirgin ruwan yaki na Amurka kusa da Najeriya inda za'a rika aiko da jiragen yaki suna luguden wuta musamman a Arewacin Najeriya. Yanayi matsakaici shine Amurkar ta rika aiko da jirage marasa matuka da zasu rika kaiwa 'yan Bindiga hari. Yanayi me sauki kuma shine goyon bayan sojojin Najeriya da bayanan sirri da kuma aiki tare wajan kaiwa 'yan Bindigar hari. Zuwa yanzu dai ba'a san wanne shugaban kasar Amurkar zai dauka ba.
Trump zai zo ne ya sake Bhautar damu kawai amma babu wata maganar Mhuzghunawa Kiristoci>>Inji Fasto Elijah Ayodele

Trump zai zo ne ya sake Bhautar damu kawai amma babu wata maganar Mhuzghunawa Kiristoci>>Inji Fasto Elijah Ayodele

Duk Labarai
Shahararren Fasto Elijah Ayodele ya bayyana cewa ba maganar kisan kiyashi da aka ce anawa Kiristoci ne zai kawo Trump Najeriya ba, Satar ma'adanai ne zai kawoshi da kuma lalata kasar. Faston ya bayyana hakane a cocinsa yayin da yake wa'azi. Yace kuma ba Najeriya kadai Trump zai lalata ba idan ya kawo harin, hadda sauran kasashen Afrika za'a sake bautar damune. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1986097914918126033?t=8zpdqnO5vDOMIGJYcx1qFA&s=19
Zamu sayar da matatun man fetur na kasarnan>>Gwamnatin Tarayya

Zamu sayar da matatun man fetur na kasarnan>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyar sayar da matatun man fetur mallakin Gwamnati, watau na Kaduna, Fatakwal, da Warri. Gwamnatin tace zata yi hakanne dan inganta aikin matatun da kuma jawo masu zuba jari Najeriya. Babban me baiwa shugaban kasar shawara akan makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a wajan wani taro a Kasar UAE. Matatun man fetur din na Najeriya sun lakume makudan kudade wanda aka ware dan gyarasu amma har yanzu basu aiki yanda ya kamata.