Fadar Vatican ta sanar da mutuwar shugaban majami'ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya.
A shekarar 2023 ne cocin ta zaɓi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin.
Tun bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya tafi kasar Faransa a ranar 2 ga watan Afrilu, fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa zai yi sati biyu ne.
Saidai yayin da ake tsammanin zai dawo ranar 16 ga watan Afrilu, shugaban kasar bai dawo ba inda musamman 'yan Adawa suka fara tambayar ba'asi.
Fadar shugaban kasar ta sake fitar da sanarwa inda tace shugaban kasar yana nan lafiya kuma yana gudanar da aiki daga can kasar Faransar da yake.
Saidai hakan a cewar masana ya sabawa aiki inda bai kamata ace daga kasar Wajene shugaban kasar zai rika gudanar da gwamnati ba.
Abubuwan da dama sun faru musamman bangaren matsalar tsaro inda aka yi kashe-kashe amma shugaban kasar bayanan inda daga can kasar Faransa ne ya baiwa jami'an tsaro umarnin cewa su magance matsalar da kakka...
A yau, Litinin, Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar Filato dan jajantawa iyalan wadanda aka kashe a hare-haren da suka faru a jihar.
Mutane sama da 100 ne aka kashe a jihar biyo bayan wasu munanan hare-haren da aka kai a cikin makonnin nan.
Ministan jinkai da rage Talauci, Dr. Nentawe Yilwatda ne ya tabbatar da zuwan mataimakin shugaban kasar a yayin da ya kai ziyara Bassa ranar Asabar dan ganewa idansa yanda lamarin ya faru.
Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kansa ne ya baiwa Kashim Shettima umarnin kai wannan ziyara.
A yayin ziyarar tasa ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai gana da masu ruwa da tsaki na yankin dan samo hanyar magance wannan matsalar.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman kiristoci, Bishop Matthew Hassan Kukah da Pastor Tunde Bakare suka soki Gwamnatinsa.
A sakonsu na bikin Easter, Manyan malaman kiristocin sun nemi shugaban kasar ya dauki matakai akan matsin tattalin arziki da matsalar tsaro da ake fama da ita.
Saidai da yake mayar da martani ta bakin kakakinsa, Daniel Bwala, shugaba Tinubu yace a wasu bangare da Fasto Tunde Bakare ya sokeshi sun sha banban amma kuma yana da 'yanci a matsayinsa na dan kasa ya bayyana ra'ayinsa.
Yace amma shugaban kasar ya mayar da hankali wajan ganin ya cika alkawuran da ya daukarwa 'yan Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa, Bankunan Najeriya sun samu kudin shiga daga kudaden ruwa da suke karba a hannun wadanda suka baiwa bashi da suka kai Naira Tiriliyan 14.26.
Hakan ya bayyana ne bayan kammala kididdigar da aka yi ta kudaden shigan bankunan a shekarar 2024.
Bankunan da suka samu wadannan kudaden shigar sune, Fidelity, UBA, GT Bank, First Bank, Wema Bank, Stanbic IBTC, FCMB, Access, da Zenith Bank.
Rahoton yace a shekarar 2023 bankunan sun samu kudin ruwa da suka kai Naira Tiriliyan 6.49 wanda idan aka hada da kudaden ruwan da suka samu a shekarar 2024 na Tiriliyan 14.26, hakan na nufin sun samu karin kaso 119.55 cikin dari kenan na kudin ruwan.
Saidai a gefe guda, yayin da bankunan ke murnar samun kudin ruwa daga hannun wadanda suka baiwa bashin, su kuma wadanda suka k...
Rahotanni daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa ƴanbindiga sun saka harajin miliyoyin naira ga wasu al'umomi da ke yankin Ɗan Kurmi a ƙaramar hukumar mulki ta Maru.
Ƴanbindigar sun ayyana Laraba a matsayin ranar wa'adin biyan kuɗin amma tuni suka fara aiwatar da dokar tsare mutane a garin Zargado har sai an biya kudin a matsayin diyya.
Al'ummar yankin da abin ya shafa sun sheda wa BBC cewa sun samu kansu a wannan tasku ne bayan da wasu mazauna yankin suka kona daji da kuma hare-haren da sojoji suka kai wa 'yanbindigan shi ne barayin dajin suka dora musu wannan haraji na naira miliyan 60.
Honarabul Iliyasu Salisu Dankurmi ya tabbatar wa da BBC wannan lamari :
''Sojoji sun shigo aiki wannan yanki sun koma to kuma yanzu 'yanbindiga sun zo sun aza mana haraji, suka ce sai ...
Rahotanni daga jihar Kano na cewa an samu fashewar tukunyar gas a wani wajan sayar da gas din dake Dorawar 'yan Kifi, Rijiyar Zaki.
A bayanan da hutudole ya samu shine ba'a samu asarar rayuka ko jikkata ba saidai asarar Dukiya.
A bidiyon da suka rika yawo a kafafen sada zumunta, an ga da jin yanda tukwanen gas din duka rika fashewa kamar bam na tashi.
https://www.tiktok.com/@kingkadoo1/video/7495415482929974583?_t=ZM-8vhcbEDH8TN&_r=1
https://www.tiktok.com/@kingkadoo1/video/7495418146510179639?_t=ZM-8vhcgdjSPDT&_r=1
https://www.tiktok.com/@kingkadoo1/video/7495422464655101189?_t=ZM-8vhcl2xDLao&_r=1
https://www.tiktok.com/@a.k.a.i.s.u/video/7495433889079463174?_t=ZM-8vhcsqiCr3O&_r=1
Saidai daga baya 'yan kwana-kwana sun kai wajan sun kashe gobara...
Babban me sharhi akan Al'amuran tsaro, Bulama Bukarti ya mayarwa da Tsohon Ministan tsaro, T.Y Danjuma martani kan kiran da yayi mutane su tashi tsaye su kare kansu game da matsalar tsaro.
T.Y Danjuma yace gwamnati ba zata iya ba ita kadai inda yace kamata yayi mutane su tashi su kare kansu.
Saidai a hirar da aka yi dashi a Channels TV, Bulama Bukarti ya bayyana cewa wannan ba mafita bace.
Yace idan aka yi hakan, makamai zasu karu a hannun farar hula wanda hakan zai kawo ci gaba da kisan mutane ba tare da hukunci ba.
2027: Nan da watanni 6 yankin Arewacin Najeriya zai bayyana matsayar sa kan zaben shugaban kasa - Hakeem Baba-Ahmed.
Hakeem Baba-Ahmed, tsohon mai bai wa Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa, ya yi gargadin cewa Arewacin Najeriya na iya daukar matsaya mai tsauri dangane da makomar siyasar yankin idan aka ci gaba da watsi da koke-koken yankin.
A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Baba-Ahmed ya bukaci ‘yan Arewa da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya tare da lura da "makaryata" da ke aiki don raunana yankin.
“Arewacin Najeriya za ta tsaya ta kare kanta, wallahi,” in ji shi.
“Ya kamata Arewa ta yi hattara sosai, ta guji ‘yan siyasa na cin amana da kuma duk wani abu da zai kawo rabuwar kai.”
Ya jaddada bukatar h...
Rahotanni daga Maiduguri na cewa wani abin fashewa me kama da bam ya fashe a gidan yarin dake garin da daren Ranar Lahadi.
Lamarin ya farune da misalin karfe 9 na darennan inda hakan yayi sanadiyyar tashin wuta a dakin da ake tsare da Charles Okah.
Wasu shaidu sun ce an cilla wani abu me kama da bam a dakin da ake tsare da Charles Okah din inda aka ga hayaki na tashi.
Wannan lamari ya biyo bayan budaddiyar wasikar da Charles Okah ya aikewa ministan harkokin cikin gida, Olubunmi-Ojo ne inda yake korafi kan yawaitar cin hanci a gidajen yarin Maidugurin.
Rahoton na Sahara reporters yace Okah ya rika tari inda aka ji yana fadin an cilla masa bom a dakinsa.
Saidai babu wanda ya kai masa dauki dan kuwa a cewar rahoton ma'aikatan gidan yarin dake aikin dare basa nan.
Hakanan wan...