Sunday, April 26
Shadow
Gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 100 dan ciyar da yara ‘yan Makaranta a shekarar 2025

Gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 100 dan ciyar da yara ‘yan Makaranta a shekarar 2025

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya a cikin kasafin kudin shekarar 2025 ta ware Naira Biliyan 100 dan ciyar da yara 'yan Makarantar Firamare. Tsarin ciyarwar an fito dashi ne dan kawar da matsalar rashin samun abinci me gina jiki da yaran ke fama da ita da kuma karfafa ilimi da karfafa gwiwar manoma. A kokarin inganta tsarin, Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, zata yi kokarin ganin an magance matsalolin shirin kama daga rashin biyan masu aikin da manoma da rashin baiwa daliban abinci me kyau.
Jamb ta samu kudin shiga Biliyan 22.9 inda ta baiwa gwanatin tarayya Naira Biliyan 6

Jamb ta samu kudin shiga Biliyan 22.9 inda ta baiwa gwanatin tarayya Naira Biliyan 6

Duk Labarai
Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta Jamb ta sanar da cewa ta baiwa gwamnatin tarayya kudi shiga da suka kai Naira Biliyan 6 a shekarar 2024. Kakakin JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Litinin inda yace sun samu jimullar kudin shiga da suka kai Naira N22,996,653,265.25 a shekarar 2024 din. Yace sun baiwa Gwamnatin tarayya Naira N6,034,605,510.69 daga cikin kudin. Sanarwar tace kudin da suka baiwa gwamnatin tarayya rara ce da suka samu bayan kammala aikin shirya jarabawar ta shekarar 2024 da cire duk wasu kudade da suka kamata. Ya kara da cewa a cikin shekaru 7 da suka gabata, sun baiwa Gwamnatin tarayya jimullar kudaden shiga da suka kai naira Biliyan 50.
Baku da Godiyar Allah>>Shugaban kasar Faransa ya caccaki shuwagabannin kasashen Africa

Baku da Godiyar Allah>>Shugaban kasar Faransa ya caccaki shuwagabannin kasashen Africa

Duk Labarai
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya caccaki shuwagabannin kasashen Africa inda yace basu da godiyar Allah. Ya bayyana hakane yayin da yake tattauna ci gaban da aka samu a yankunan Africa. Yace tun shekarar 2013 suka girke sojojinsu inda suke taimakawa wajan yaki da ta'addanci da kuma magance matsalar juyin mulki da aka rika samu a wasu kasashen African. Yace ba dan taimakon da suka bayar ba da wasu kasashen African yanzu ba kasashe bane sun dade da arwatsewa. Yace amma shuwagabannin African basa ganin irin kokarin da kasar Faransar take musu, sojojinsu na sadaukar da rayuwarsu, amma ba'a godewa. Idan dai za'a iya tunawa, kasar Nijar ta kori sojojin faransa daga cikinta.
Shugaba Tinubu ya amince a rika baiwa manyan sojojin da suka ajiye aiki Naira Miliyan 34 duk shekara da canja musu motoci duk bayan shekara 4

Shugaba Tinubu ya amince a rika baiwa manyan sojojin da suka ajiye aiki Naira Miliyan 34 duk shekara da canja musu motoci duk bayan shekara 4

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa sabuwar dokar canja fasalin biyan manyan sojoji da suka ajiye aiki hakkokinsu. A sabuwar dokar, Soja da ya aije aiki yana da mukamin CDS, za'a rika bashi Dala dubu $20 duk shekara na kula da lafiyarsa a kasar waje, sannan za'a bashi mota jif wadda harsashi baya hudata, kuma hukumar soji ce zata rika kula da motar sannan bayan duk shekara hudu za'a rika canja mai motar. Sannan za'a bashi mota Peugeot 504 ko wata kwatankwacinta sannan kuma za'a bashi ma'aikata 5, da suka hada da masu dafa abinci 2, me ban ruwan fulawa, da wasu karin masu hidima biyu. Zakuma a bashi me gadi mutum daya da Mataimaki na musamman guda daya, sai direbobi 3, sannan kuma duk sanda yake bukatar karin jami'an tsaro, za'a bashi. Sannan kuma zai ci gaba da rike bin...
Kwankwaso ba zai yi nasara a zaben 2027 a Kano ba>>Inji Ganduje

Kwankwaso ba zai yi nasara a zaben 2027 a Kano ba>>Inji Ganduje

Duk Labarai
Shugaban Jam'iyyar APC ta kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, Mutanen Kano ba zasu sake goyawa Kwankwaso baya ba. Yace ko da a 2023 ma rikicin cikin gida na Jam'iyyar APC ne yasa Kwankwaso yayi nasara a zaben, yace amma wanda suka zabi Jam'iyyarsa ta NNPP a yanzu suna nadama. Ya bayyana hakane a wajan taron karrama jiga-jigan Jam'iyyar da aka yi inda shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya wakilceshi. Ganduje yace yakan yi mamaki idan yaji Kwankwaso na cewa yana da goyon bayan mutanen jihar, yace gashinan Gwamna Abba Kabir Yusuf ma duk a rude yake bai san abinda ke tafiya a gwamnatinsa ba. Ganduje yayi kira ga 'yan Jam'iyyar ta APC da su hada kansu inda yace ta hanyar hakane musamman zasu samu nasarar kwace Jiyar daga hannun NNPP.
An kubutar da yara 4 da aka sace daga jihar Bauchi aka kaisu Jihar Anambra aka sayar

An kubutar da yara 4 da aka sace daga jihar Bauchi aka kaisu Jihar Anambra aka sayar

Duk Labarai
Hukumar 'yansanda a jihar Anambra ta sanar da kubutar da wasu yara 4 da aka sato daga jihar Bauchi aka kaisu Anambra aka sayar dasu ga wasu iyalai. Kwamishinan 'yansandan jihar, Obono Itam ne ya bayyana haka inda yace sun kama mutane 4 da ake zargi da hannu a lamarin. Ya hayyana hakane ranar Litinin, 6 ga watan Janairu inda yake bayani game da yanda hukumar tasa ta gudanar da ayyukanta a shekarar 2024. Yace daya daga cikin yaran an ganeshi kuma dukansu za'a mayar dasu ga iyayensu. Ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun amsa laifukansu.
‘Ƙungiyar su Shekarau za ta koma jam’iyyar siyasa’

‘Ƙungiyar su Shekarau za ta koma jam’iyyar siyasa’

Duk Labarai
Ƙungiyar League of Northern Democrats (LND) wadda wasu ƴan siyasa daga arewacin Najeriya suka kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ta fara yunƙurin zama jam'iyyar siyasa domin fuskantar zaɓen shekarar 2027. Ƙungiyar ta zargi jam'iyya mai mulki ta APC da babbar jam'iyyar adawa ta PDP da gazawa wajen ciyar da Naeriya gaba, sannan ta buƙaci ƙungiyoyin kudancin ƙasar da su shigo su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ceton ƙasar. A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta ruwaito daga ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar, Dr Umar Arɗo, ya ce ƙungiyar ta LND za ta kawo sauyi tare da sake dawo da martabar ƙasar. Ya ce rashin ingancin gwamnati ne ya jefa ƙasar cikin ƙangin talauci da rashin tsaro da rashin tabbas. Sai dai tuni jam'iyyar APC ta mayar da ma...
Dattawan Arewa sun koka da kwamitin da aka kafa domin duba ƙudurin haraji

Dattawan Arewa sun koka da kwamitin da aka kafa domin duba ƙudurin haraji

Duk Labarai
Ƙungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta koka kan rashin shigar da ƙwararu a kwamitin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci ofishin ministan shari’a da na majalisar ƙasar su kafa domin sake duba ƙudurorin cikin tsanaki. Ƙungiyar ta ce bai kamata gwamanti ta nemi a kawo sauye-sauye cikin gaggawa kan batun dokar harajin ba, inda ta ce aiwatar da dokar ba tare da tuntuɓa yadda ya kamata ba zai yi wa jihohin yankin illa. Farfesa Abubakar Jika Jiddere ɗaya ne daga cikin shugabanin ƙungiyar ya ce kawo yanzu sun kamala yi wa dokar harajin duba na tsanaki kuma sun haɗa rahotonsu, wanda haka yasa suke ganin dole a sake nazari kan ƙudurin.