Ƴaƴana sun je karɓo kuɗin kai su asibiti aka kama su cikin masu zanga-zanga a Kano’
Ɗaya daga cikin iyayen yaran nan da gwamnatin Najeriya ta tuhuma da cin amanar ƙasa sakamakon zanga-zanga kan tsadar rayuwa ta ce ta yi farin ciki da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya ce a sake su.
Fatima Muhammad ta ce 'ya'yanta biyu ne cikin yaran da aka kama lokacin da ta aike su karɓo kuɗin za a yi amfani da su wajen kai ɗaya daga cikinsu asibiti saboda ba shi da lafiya.
"Wallahi farin cikin da muka ji ba zai musaltu ba," in ji Fatima.
Shugabanni da kungiyoyi sun yi tir da kama yaran a wurin zanga-zangar da aka gudanar domin nuna fushi game da tsadar rayuwa daga 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.
Da yake jawabi a fadar shugaban ƙasa, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce shugaban ƙasa ya ce a sake su duk inda suke a faɗin Najeriya, kuma a sadar da su ga iyayensu.
...








