Saturday, March 7
Shadow
Gwamnatin tarayya ta baiwa masu boye da dalar Amurka a gidajensu watanni 9 su fito da ita

Gwamnatin tarayya ta baiwa masu boye da dalar Amurka a gidajensu watanni 9 su fito da ita

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana baiwa masu boye da dalar Amurka a gidaje su fito da ita su kai banki wata tara. Gwamnatin tace idandai kudaden na halas ne ba na sata ba ko zamba cikin aminci ba,babu wani hukunci da za'a wa mutum idan ya fito dasu. Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka inda ya zargi cewa masu boye dalar na taimakawa wajan kara karancinta da tsadarta a Najeriya.
NAFDAC ta yi gargadin daina Amfani da wani turaren Nivea Roll-On saboda illarsa

NAFDAC ta yi gargadin daina Amfani da wani turaren Nivea Roll-On saboda illarsa

Duk Labarai
Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta yo gargadin daina amfani da wani kalar Turaren Nivea Roll-on saboda illar da yake dauke da ita. Kalar turaren da ta ja kunne kan amfani dashi shine Nivea Black & White Invisible Roll-on deodorant saboda yana dauke da wani sinadari da aka haramta amfani dashi a cikin turaruka. Tuni kungiyar Kasashen Turai ta EU ta fitar da sanarwa akan daina amfani da wannan turare inda tace duk ma wadanda suka sayeshi su mayar dashi ga kamfanin. Shi wannan sinadari dai na taba lafiyar haihuwar masu amfani dashi inda yawan amfani dashi na iya kai ga mutum ya kasa haihuwa sannan yana taba lafiyar yaron da ba'a haifa ba idan mace me ciki na amfani dashi sannan kuma yana sanya kaikai a jikin mutum. Shi wannan sinadari dai sunansa 2-(4-tert...
Ji bayanan Bala me rungumar mata, duk da ya tsufa bai tubaba

Ji bayanan Bala me rungumar mata, duk da ya tsufa bai tubaba

Duk Labarai
Shahararren mutuminnan na jihar Bauchi me suna Bala wanda yayi suna a kafafen sada zumunta saboda bayyanar hotunansa yana rungumar mata a jihar Bauchi an yi hira dashi. A hirar ya bayyana cewa, abubuwan da suka faru wanda ake ta yayata hotunansu a yanzu wasunsu sun kai shekaru 20 da faruwa saidai yace na baya-bayannan shekaru 6 ne da faruwarsa. Yace shi baya rayuwa irin ta addini, rayuwa yake irin ta 'yanci da jin dadi. Saidai yace yana son ya auri mace me aiki wadda ko da bayan ya mutu zata kula da 'ya'yansu. Kalli Bidiyon anan

Maganin karin duwawu na shafawa

Kara Kiba
Idan kina Bukatar Hips Sannan kuma Mazaunan ki suyi Sutu sutu, Domin Hakan yana Kayatar da Maza. ⇚ Madarar Shanu ⇚ Zuma ⇚ Dan kalin Turawa ⇚ Coconba ⇚ Kayan Marmari. ki samu dankalin turawa ki dafashi ya dahu sosai, idan yasha iski Hadashi da Cocoban dinki sai ki Marka deshi, ki dinga Sha da madarar shanu da Zuma kadan, Zaki Sha na tsawon wata 1. Sannan ki dinga yawan Shan Mayan Marmari.

Maganin hips cikin kwana uku

Kara Kiba
Mata da yawa suna bukatar suga hips dinsu ya ciko tun basuyi aureba saboda yanda yake daukar hankalin da namiji to ballantana amarya Wanda ita tafi cancanta data samu hips domin daukar hankalin oga. kuma yana kara saka namiji yaji ya gamsu da matarsa Kafin kiyi amfani da maganin karin hips Abinda ya kamata kifara sani shine yaya yanayin jikinki yake? Ya dace ki kara hips? Abinda nake nufi shine akwai mace Wanda taketa kiba ita wannan batada matsakar wannan koda yake ana samu wacce kibarta tafi yawa ta sama. Akwai kuma mace wacce take batada kiba amma tanada breast(nono) sosai to irin wadannan zaka samesu basuda wadataccenhips irinsu sune ya kamata surinka kokarin amfanida maganin karin hips amma mace wacce batada nono sosai tun tana budurwa ana samunta da hips itama wannan babu ru...

Maganin kiba da duwawu

Kara Kiba
Karin girman duwawu abune da mata da yawa ke son samu amma ba kowace macece ke samun magani sahihi ba. A wannan bayani zamu bayyana muku sahihan hanyoyi na kara girman duwawu da zaki ga mazaunanki sun yi bulbul. Magani na farko shine ana samun hada Hulba da Man zaitun a rika sha sau 4 a rana, hakan yakan sa mace jikinta yayi bulbul ciki hadda duwawunta. Ana samun Man Hulba da Castro Oil a hada a rika shafawa akan duwawun, insha Allah zaki ga jikinki ya kara girma sosai. Hakanan ana son a rika cin wake, Dankalin Turawa, Fasuliyya da dai sauransu.

Karin kiba da hulba

Kara Kiba
*MAGANIN ƘARIN ƘIBA WANDA BASHI DA ILLAH BAYANI YADDA ZAA KARA KIBA GA MAI BUKATAR WANNAN.•(1)- Domin Karin kiba Za'a samo Zabib,da hulba, Za'a wanke Zabib din sannan azuba shi acikin ruwa Kofi biyu, sai shi yayi awa (16)Sannan Amur tsike shi atace bayan yahade sai kuma azuba hulba cokali (2) idan ruwan yayi kasa Sai akara wani daga nan sai asanya a freeze arufe amma banda marfin Wanda zai rufe kwanon ko robar gamgam. Idan yakara kamar awa (6)Sai atace za'arika shan karamin kofin shayin larabawa ,ko buzaye.•Sai dai yakan sanya kara cin abinci,to ana bukatar arika cin abinci mai kya Wanda yake gina jiki.•(2)-hanya ta biyu:•(1)- Ya yan hulba(2)- alkama(3)- waken suya(4)- gyada(5)- garin dabino(6)- garin farar shinkafa(7)- madara(8)- zumasaiki maida su gari suyi laushi saiki rika diba coka...
Da Duminsa: Kungiyar Gwamnonin Najeriya tace bata yadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kara harajin VAT ba

Da Duminsa: Kungiyar Gwamnonin Najeriya tace bata yadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kara harajin VAT ba

Duk Labarai
Majalisar zartaswa wadda ta hada da kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF ta bayyana cewa tana baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar ya dakata da maganar kara harajin VAT. Kungiyar gwamnonin ta bakin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde tace tana baiwa shugaban kasar shawarar ya dakata a wayarwa mutane da kai su fahimci abinda kudirin kara dokar VAT din ke nufi. Sannan ya kamata a tuntubi masu ruwa da tsaki a kan harkokin al'umma dan jin shawarar su kan lamarin. Ko da a baya dai, Kungiyar Gwamnonin Arewa da sarakunan yankin sun bayyana cewa basa tare da shugaban kasar kan karin harajin VAT.
Muna nan akan bakarmu na baiwa shugaba Tinubu shawarar ya ci gaba da kara kudin man fetur>>IMF

Muna nan akan bakarmu na baiwa shugaba Tinubu shawarar ya ci gaba da kara kudin man fetur>>IMF

Duk Labarai
Hukumar bayar da lamuni ta Duniya tace bata canja ba, har yanzu tana nan akan bakanta cewa shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur dana dala. Hukumar tace ta hakane 'yan Najeriya zasu samu saukin rayuwa daga matsin tattalin arzikin da suke fama dashi. Karin farashin man fetur dai yasa kayan masarufi sun tashi sama sosai inda talakawa ke cin abinci da kyar. Lamarin ya jawowa gwamnati tofin Allah tsine tsakanin Talakawa. Hakanan an sha zargin hukumar ta IMF da bankin Duniya da bayar da shawarwarin dake jefa kasashe da yawa cikin wahalar rayuwa.
Kalli Bidiyon matasan Kaduna suna murnar Nepa ta dawo

Kalli Bidiyon matasan Kaduna suna murnar Nepa ta dawo

Duk Labarai
Bayan dawowar wutar lantarki a jihar Kaduna, Matasa sun hau titi inda suka rika wakar cewa Nepa ta dawo. Bidiyon hakan ya watsu sosai a kafafen sada zumunta: https://www.youtube.com/watch?v=caZd7slnLhs Wasu sun bayyana abin da Nishadi inda wasu kuma suka bayyana takaici da cewa 'yan Kaduna sun bayar da kunya da wannan murna. https://twitter.com/Abdool85/status/1851757048075051304?t=oy8qaPAfPahhKBfpfc46Tg&s=19 Kusan sati biyu aka kwashe ana fama da rashin wuta a yankin Arewa kamin a samu ta dawo.