Saturday, December 20
Shadow
Da Duminsa: Fadar Shugaban kasa ta musanta cewa, Ministan kudi ya gabatar da Naira Dubu Dari da biyar(105,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Da Duminsa: Fadar Shugaban kasa ta musanta cewa, Ministan kudi ya gabatar da Naira Dubu Dari da biyar(105,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Siyasa
Rahotannin da muke samu na cewa, fadar shugaban kasa ta musanta wasu bayanai dake cewa ministan kudi ya gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Naira Dubu dari da biyar(105,000) a matsayin mafi karancin Albashi. Babban me baiwa shugaban kasa Shawara kan harkar yada labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta. Ga sakonsa kamar haka: "The Honorable Minister of Finance and coordinating minister of the economy, Wale Edun has not proposed N105,000 minimum wage. The contrary story being disseminated is false.”
Ji matakin da Kasar Iran tace zata dauka akan kasar Israela bayan da Israelan ta sake kai harin da ya kashe sojan Iran din

Ji matakin da Kasar Iran tace zata dauka akan kasar Israela bayan da Israelan ta sake kai harin da ya kashe sojan Iran din

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
A jiyane dai muka samu rahoton cewa, kasar Israela ta kai wani mummunan hari a garin Aleppo dake kasar Syria wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa ciki hadda me baiwa kasar Iran shawara akan harkar soji. A martanin kasar Iran kan harin, Kwamandan dakarun IRGC na kasar Salami ya bayyana cewa, Israela ta saurari harin ramuwar gayya. A baya dai, irin wannan harin ne Israela ta kai kan ginin ofishin jakadancin Iran wanda ya kashe wasu janarorin soja na Iran. Hakan yayi sanadiyyar harin ramuwar gayya akan Israela da Iran ta yi wanda ya baiwa Duniya mamaki kuma ya tayar da hankalin kasar Israela. A wannan karin dai ba'a san wane irin harin ramuwar gayyane Iran zata kai akan Israela ba.
Na bauta wa Kaduna da gaskiya kuma ina alfahari da hakan – El-Rufai

Na bauta wa Kaduna da gaskiya kuma ina alfahari da hakan – El-Rufai

Kaduna, Siyasa
Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kan nazari game da kuɗaɗen da aka kashe a gwamnatin da ta gabata a jihar ya miƙa sakamakon bincikensa a yau. Cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar har da na buƙatar hukumomi su binciki tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i. Lokacin da ya gabatar da rahoton a ranar Laraba, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa'i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo bashin domin su ba ko kuma ba a bi ƙa'ida wajen cin bashin ba. Da yake karɓar rahoton, shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman ya ce kuɗi naira biliyan 423 ne suka zurare a lokacin gwamnatin El-Rufa'i tare da jefa jihar cikin ƙangin bashi. Sai dai tsohon gwamnan ya ce binciken da...
A yaune Ministan kudi zai gabatar wa da shugaba Tinubu sabon daftarin mafi karancin Albashi

A yaune Ministan kudi zai gabatar wa da shugaba Tinubu sabon daftarin mafi karancin Albashi

Siyasa
Ministan kudi, Wale Edun a yau ne ake sa ran zai gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sabon daftarin mafi karancin Albashi. Ko da ita kanta kungiyar kwadago, NLC ta dage zaman ta da gwamnatin tarayya sai yau din Alhamis da ake tsammanin sake ganin nawane gwamnatin tarayyar zata kara akan Naira dubu 60 da a baya NLC din ta ki amincewa da ita a matsayin mafi karancin Albashi. Saidai a rahotanni na baya, kungiyar TUC tace ba zata amince da Kari dan kadan ba akan Naira dubu 60 din. Sannan kuma tace ba ta dage akan sai an biyata Naira Dubu 400 ba, kawai dai abinda take nema shine a biya albashi da zai wadaci ma'aikaci.
Lokacin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na gwamnan Kaduna an cire Naira Biliyan 423 daga asusun bankin jihar ba tare da yin wani aiki da kudin ba>>Majalisar Jihar

Lokacin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na gwamnan Kaduna an cire Naira Biliyan 423 daga asusun bankin jihar ba tare da yin wani aiki da kudin ba>>Majalisar Jihar

Kaduna, Siyasa
Majalisar Jihar Kaduna ta bayyana cewa a lokacin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yana mulkin jihar, an cire Naira Biliyan 423 ba tare an yi wani aiki da kudin ba daga asusun gwamnatin jihar. Hakanan kuma an cire wata Biliyan 30 daga ofishin Kwamishinan kudi da babban akanta na jihar. Jimulla, an cire Tiriliyan 1.4 daga asusun gwamnatin jihar Kaduna. Hakan ya bayyana ne daga bakin dan majalisar jihar ta kaduna, Henry Mara wanda shine me magana da yawun Majalisar a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Domin Kawo Saukin Hauhawar farashin kayan masarufi, Gwamnati zata cire harajin VAT akan kayan abinci da ake shigowa dasu Najeriya

Domin Kawo Saukin Hauhawar farashin kayan masarufi, Gwamnati zata cire harajin VAT akan kayan abinci da ake shigowa dasu Najeriya

Siyasa
Domin kawowa al'umma saukin rayuwa, Gwammatin tarayya ta sanar da shirin cire harajin VAT daga shigo da kaya da hukumar Kwastam ke karba akan kayan abinci na tsawon watanni 6. Gwammati zata dauki wannan mataki ne dan magance matsalar hauhawar farashin kayan abinci. Yanzu haka an aikawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da rahoto kan wannan lamari dan ya duba ya saka masa hannu. Kayan da za'a cirewa harajin sun hada da kayan abinci, magunguna, abincin kaji, Fulawa da sauransu. Da yawan 'yan Najeriya dai na kukan tsadar rayuwa, abin jira a gani shine idan wannan mataki zai haifar da da me ido.
Bama tunanin hadewa da kowace jam’iyya>>PDP

Bama tunanin hadewa da kowace jam’iyya>>PDP

Siyasa
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, bata tunanin hadewa dan yin maja da kowace jam'iyya. Hakan na zuwane yayin da ake tsammanin Atiku da Peter Obi zasu hade dan hada karfi su kayar da jam'iyyar APC. Hakanan a bangaren Labour party, shima kakakin kungiyar yakin neman zaben Peter Obi, Yunusa Tanko ya bayyana cewa Peter Obi baya tunanin hadewa da kowa dan samun karfi. Jam'iyyar PDP tace bata neman hadewa da kowa amma tana maraba da tsaffin membobinta wanda suke son dawowa cikinta. Kakakin PDP, Debo Ologbunagba ne ya bayyana hakan inda yace a rijistar da suke yi yanzu haka, mutane da yawa a matakin mazabu sai shiga PDP suke wanda hakan alamace ta cewa har yanzu PDP jam'iyyar Al'ummace.