Friday, December 19
Shadow
Da Duminsa: Najeriya ka iya fadawa Duhu kwanannan saboda karancin gas da kamfanonin samar da wutar lantarki ke samu

Da Duminsa: Najeriya ka iya fadawa Duhu kwanannan saboda karancin gas da kamfanonin samar da wutar lantarki ke samu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanonin dake samar da wutar lantarki na Najeriya na fama da karancin gas wanda ake amfani dashi wajan samar da wutar. Dalilin haka kuwa Najeriya na iya fadawa cikin duhu a yi bukukuwan kirsimeti babu wutar lantarki. Kamfanonin rarraba wutar na Enugu da Fatakwal sun sanar da abokan hukdarsu cewa sun rage yawar wutar da suka baiwa mutane saboda wannan matsala. Wata majiya ta tabbatarwa da Jaridar Punchng da wannan labarin. Hakan na faruwa ne saboda gazawar gwamnati waja biyan bashin da kamfanonin iskar gas din ke bi wanda rahoton yace idan ba'a biya ba ka iya sa kasar ta fada Duhu.
Kalli Bidiyon: Nuhu Ribadu da Kashim Shettima ne ke hana Tinubu samar da tsaro yanda ya kamata>>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Kalli Bidiyon: Nuhu Ribadu da Kashim Shettima ne ke hana Tinubu samar da tsaro yanda ya kamata>>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Duk Labarai
Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa, Babban me baiwa shugaban kasa, Shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu da kuma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ke hana shugaban kasar samar da tsaro yanda ya kamata. Yace Ribadu kowane bafulatani na Najeriya na da lambar wayarsa. Ya nemi shugaban kasar ya canjasu. https://twitter.com/Chude/status/2000995541656986105?t=CJ4K9Ld4wGdyDgivJ9REAg&s=19
‘Yan Kano Baku da Ankali, Wancan da kuka kama ya shiga masallaci a Hotoro, kamata yayi ku mikashi wajan hukuma>>Inji Wannan mutumin

‘Yan Kano Baku da Ankali, Wancan da kuka kama ya shiga masallaci a Hotoro, kamata yayi ku mikashi wajan hukuma>>Inji Wannan mutumin

Duk Labarai
Wani mutum da ya bayyana ya soki kanawa saboda Qàshè wanda ake zargi da cire Makogoron Ladani a Hotoro. Yace da aka kamashi ba kasheshi ya kamata a yi ba, kamata yayi a mikashi hannun hukuma ta yi bincike. Yace ta hanakane za'a gano duk masu alaka dashi amma yanzu gashi an kasheshi an koma ana ta zargin wai waye ya aikosshi. Yace shi yanzu duka shi da ladanin yakewa addu'a. https://www.tiktok.com/@nationalbestblogger/video/7584503733317422392?_t=ZS-92HUYUe04B7&_r=1
Da Duminsa: Ban yi hira da Freedom Radio ba, Na yi Mubaya’a ga Sarautar Sarkin Wakar da aka baiwa Rarara>>Inji Naziru Sarkin Waka

Da Duminsa: Ban yi hira da Freedom Radio ba, Na yi Mubaya’a ga Sarautar Sarkin Wakar da aka baiwa Rarara>>Inji Naziru Sarkin Waka

Duk Labarai
Tauraron mawakin Arewa, Naziru Sarkin Waka, yace bai yi Hira da Freedom Radio ba akan sarautar Sarkin Waka da aka baiwa Rarara ba. Yace idan da gaske ya fadi cewa sarautar irin ta Alutace ai ya karawa abin daraja ne tunda masu ilimi ne ke Aluta. Yace idan amincewa da sarautar da aka baiwa Rarara zata sa a shafa musu Lafiya, yayi mubaya'a ya amince. https://vt.tiktok.com/ZSPmqvYq2
Da Duminsa: Shugaban Hukumar NMDPRA da Dangote ya kai kara ICPC bisa zargin ya kashe dala Miliyan $7 wajan biyawa ‘ya’yansa kudin makaranta yayi martani

Da Duminsa: Shugaban Hukumar NMDPRA da Dangote ya kai kara ICPC bisa zargin ya kashe dala Miliyan $7 wajan biyawa ‘ya’yansa kudin makaranta yayi martani

Duk Labarai
Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed ya yi martani kan zargin da Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya masa na cewa ya kashe dala Miliyan $7 wajan biyawa 'ya'yansa kudin makaranta. Yace 3 daga cikin 'ya'yansa sun samu scholarship inda aka biya musu kaso me yawa na kudin karatunsu. Sannan yace akwai kudaden da mahaifinsa wanda dan kasuwane ya tara dan ilmin 'ya'ya da jikoki sannan 'yan uwa na taimakawa hakanan shima yana taimakawa 'ya'yan nasa. Yace ta hakane ya samu ilmantar da 'ya'yan nasa amma ba sata yayi ba.
Da Duminsa: A hukumance, Shugaban Amurka, Donald Trump ya haramtawa ‘yan Najeriya da wasu karin kasashe 14 shiga kasar Amurka

Da Duminsa: A hukumance, Shugaban Amurka, Donald Trump ya haramtawa ‘yan Najeriya da wasu karin kasashe 14 shiga kasar Amurka

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya saka karin kasashe 15 da ya hanasu shiga kasar Amirkar. Kasashen sune: AngolaAntigua and BarbudaBeninCote d’IvoireDominicaGabonThe GambiaMalawiMauritaniaNigeriaSenegalTanzaniaTongaZambiaZimbabwe Yace ya dauki wannan mataki ne dan inganta tsaron kasar Amirkar. Saidai Haramta shigar bata dindin bace ta wucin gadi ce.
Kalli Bidiyon yanda Tsohon Minista, Hadi Sirik ya sha da kyar a hannun matasa a Garin Dutsi jihar Katsina

Kalli Bidiyon yanda Tsohon Minista, Hadi Sirik ya sha da kyar a hannun matasa a Garin Dutsi jihar Katsina

Duk Labarai
Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa a garin Dutsi dake jihar Katsina. An ga yanda matasa suka taru a wajan da Hadi Sirikan yaje inda ake basu Hakuri. Rahotanni dai sun ce ya sha ruwan duwatsu. https://twitter.com/SaharaReporters/status/2001028453978775801?t=Kc_uDHE26i02tVAnTX3jYw&s=19
Kalli Bidiyon: Naga cikin masu min raddi hadda matan banza, Rokon Annabi Ceto Kafurcine>>Inji Dr. Hussain Kano

Kalli Bidiyon: Naga cikin masu min raddi hadda matan banza, Rokon Annabi Ceto Kafurcine>>Inji Dr. Hussain Kano

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Dr. Hussain Kano ya bayyana cewa, Rokon Annabi(Subhanallahi Alaihi Wasallam) ceto kafurcine. Inda yace saidai mutum ya roki Allah ya sakashi a cikin ceton Annabi. Yace a cikin wanda ke masa raddi ya ga hadda Karuwai. https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7584506809746984204?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7584506809746984204&source=h5_m&timestamp=1765918165&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7568740291232040721&share_link_id=027a73ed-f3e6-...
Buhari ya rika rokon Shugaba Tinubu kada ya binciki ministocinsa, saboda suna amfanar dashi>>Inji A’isha Buhari

Buhari ya rika rokon Shugaba Tinubu kada ya binciki ministocinsa, saboda suna amfanar dashi>>Inji A’isha Buhari

Duk Labarai
Matar tsohon shugaban kasa, Marigayi, Muhammadu Buhari Hajiya A'isha Buhari ta bayyana cewa, Shugaba Buhari ya rika rokon Shugaba Tinubu kada ya binciki ministocinsa. Ta bayyana cewa, dalili shine saboda yana karuwa da su. Ta bayyana hakane a cikin littafin da aka rubuta na bayar da tarihin rayuwar tsohon shugaban. Rahoton yace wannan na daga cikin dalilan da suka sa Buhari ya kasa rika canja ministocinsa duk da korafin da akai ta yi akansu.