Friday, December 19
Shadow
Kalli Bidiyon: Naga cikin masu min raddi hadda matan banza, Rokon Annabi Ceto Kafurcine>>Inji Dr. Hussain Kano

Kalli Bidiyon: Naga cikin masu min raddi hadda matan banza, Rokon Annabi Ceto Kafurcine>>Inji Dr. Hussain Kano

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Dr. Hussain Kano ya bayyana cewa, Rokon Annabi(Subhanallahi Alaihi Wasallam) ceto kafurcine. Inda yace saidai mutum ya roki Allah ya sakashi a cikin ceton Annabi. Yace a cikin wanda ke masa raddi ya ga hadda Karuwai. https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7584506809746984204?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7584506809746984204&source=h5_m&timestamp=1765918165&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7568740291232040721&share_link_id=027a73ed-f3e6-...
Buhari ya rika rokon Shugaba Tinubu kada ya binciki ministocinsa, saboda suna amfanar dashi>>Inji A’isha Buhari

Buhari ya rika rokon Shugaba Tinubu kada ya binciki ministocinsa, saboda suna amfanar dashi>>Inji A’isha Buhari

Duk Labarai
Matar tsohon shugaban kasa, Marigayi, Muhammadu Buhari Hajiya A'isha Buhari ta bayyana cewa, Shugaba Buhari ya rika rokon Shugaba Tinubu kada ya binciki ministocinsa. Ta bayyana cewa, dalili shine saboda yana karuwa da su. Ta bayyana hakane a cikin littafin da aka rubuta na bayar da tarihin rayuwar tsohon shugaban. Rahoton yace wannan na daga cikin dalilan da suka sa Buhari ya kasa rika canja ministocinsa duk da korafin da akai ta yi akansu.
Kalli Bidiyon: Shugaba Tinubu zai nada Ali Nuhu Minista>>Inji Saheer Abdul

Kalli Bidiyon: Shugaba Tinubu zai nada Ali Nuhu Minista>>Inji Saheer Abdul

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Saheer Abdul ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai nada Ali Nuhu Minista. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta. Saidai da alama ya fadi wannan maganane cikin Raha inda a karshe yake cewa, amma sai Ali Nuhun yayi sadaka da garin Danwake. https://www.tiktok.com/@mr_saheeer/video/7584476452922428693?_t=ZS-92H6rAYRjXN&_r=1
Kalli Bidiyon: A gabana Fulani da Hausawa Musulmai kusan 100 suka koma Kirista >>Inji Wannan matashiyar

Kalli Bidiyon: A gabana Fulani da Hausawa Musulmai kusan 100 suka koma Kirista >>Inji Wannan matashiyar

Duk Labarai
Wannan matashiyar me suna Suwaiba ta bayyana cewa wani abu da ya faru a wajan da take aiki ya tayar mata da hankali. Tace a gabanta, Hausawa da Fulani Musulmai su 100 suka koma Kirista. Tace da take jan hankalinsu har suma suka rika ce mata tazo yesu ya ceceta. Ta bayyana lamarin da karshen Duniya. https://www.tiktok.com/@user2542206614891/video/7581825566404545813?_t=ZS-92H5D7Lx1mL&_r=1
Da Duminsa: Aliko Dangote ya maka shugaban Hukumar kula da man fetur ta MNDPRA, ga hukumar ICPC inda yace yayi amfani da dala Miliyan $7 wajan biyawa ‘ya’yansa kudin makaranta a kasar Switzerland

Da Duminsa: Aliko Dangote ya maka shugaban Hukumar kula da man fetur ta MNDPRA, ga hukumar ICPC inda yace yayi amfani da dala Miliyan $7 wajan biyawa ‘ya’yansa kudin makaranta a kasar Switzerland

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya maka shugaban Hukumar MNDPRA, Engnr. Farouk Ahmed ga hukumar ICPC inda yace yana zarginsa da satar kudin talakawa. Dangote yace Ahmad yayi amfani da dala Miliyan $7 wajan biyawa 'ya'yansa kudin makaranta a kasar Switzerland. Dangote yace gaba daya rayuwar Ahmad yayi ta ne a matsayin ma'aikacin gwamnati kuma idan aka tattara kudin albashinsa da alawus ko kusa ba zasu kai dala Miliyan $7 ba. Yace dan haka yana amfanine da hukumar da yake shugabanta wajan karkatar da kudaden Talakawa kawai. Dan Haka Dangote yace yana neman hukumar ta ICPC ta bincikesa. Dangote ya bayyana hakane ta hanyar lauyansa, Ogwu Onoja (SAN) ranar 16 ga watan Disamba.
Kalli Bidiyon: Mazan Kano basu yi ba, Kaf Kano banga namijin da zan iya aure ba>>Inji ‘YarGuda

Kalli Bidiyon: Mazan Kano basu yi ba, Kaf Kano banga namijin da zan iya aure ba>>Inji ‘YarGuda

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok dake tare Maiwushirya, 'Yarguda ta bayyana cewa mazam Kano masu mata ba. Tace Kaf Kano bata ga namijin da zata iya aure ba. Ta bayyana hakane a wani Bidiyo da suka yi tare da Maiwushirya. https://www.tiktok.com/@maiwushiryabackup/video/7583797120914754837?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7583797120914754837&source=h5_m&timestamp=1765902265&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7568740291232040721&share_link_id=b12fb9f7-156e-4899-8874-024dcec263db&share...
Labari Me Dadi: Najeriya ta yo Odar idin wanann jirgin guda 24 daga kasar Italiya

Labari Me Dadi: Najeriya ta yo Odar idin wanann jirgin guda 24 daga kasar Italiya

Duk Labarai
Najeriya ta yo odar jirgin yaki me suna M-346 guda 24 daga kasar Italiya. A watan Nuwamba na shekarar 2023 ne hukumar sojin sama NAF ta nemi sayen jiragen daga kamfanin kerasu me suna Messrs Leonardo dake kasar Italia. Kudin sayen jiragen sun kai €1.2 billion kuma an bayyanasu da cewa shine babban kudi da aka taba kashewa wajan sayen makamai a yankin Afrika ta yamma. Kamfanin ya amince zai ci gaba da baiwa Najeriya aikin kulawa da jirgin na tsawon shekaru 25. Jirage 6 na farko tuni aka fara kerasu inda ake tsammanin guda 3 za'a kawo su a 2025 inda sauran za'a kawo su a shekarar 2026.
Da Duminsa: Akwai yiyuwar Najeriya zata iya kaiwa ga gasar cin kofin Duniya na 2026 duk da Dr. Congo ta cireta

Da Duminsa: Akwai yiyuwar Najeriya zata iya kaiwa ga gasar cin kofin Duniya na 2026 duk da Dr. Congo ta cireta

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, har yanzu akwai yiyuwar Najeriya ta samu damar buga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026 wanda za'a yi a kasashen Amurka, Canada, da Mexico. Hakan na zuwane bayan da hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta shigar da korafi a gaban hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA inda take cewa wasu daga cikin 'yan wasan kasar Dr. Congo basu cancanci yi wa kasar wasa ba. Korafin na cewa akalla 6 zuwa 9 na 'yan wasan Dr. Congo sun koma 'yan kasar ta Dr. Congo ne daga wasu kasashe daban-daban kuma ma har FIFA ta tantancesu ta amince da hakan. Saidai NFF sun gano cewa, daga cikinsu akwai wadanda basu bar kasashen su na baya ba, watau ma'ana suna rike da fasfon kasashe biyu, wanda kundin tsarin mulkin kasar Dr. Congo ya haramta rike fasfon kasashe Biyu. Yanzu dai...