Friday, December 19
Shadow
Kalli Bidiyon: A matsayina na sarkin Wakar kasar Hausa, Daga yanzu duk wanda zai saurari waka saida Umarnina>>Inji Rarara

Kalli Bidiyon: A matsayina na sarkin Wakar kasar Hausa, Daga yanzu duk wanda zai saurari waka saida Umarnina>>Inji Rarara

Duk Labarai
Tauraron Mawakin Hausa da akawa Nadin Sarkin Wakar Qasar Hausa, Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa, daga yanzu ko sauraren waka sai da izininsa. Rarara yace idan mutum ya saurara sau daya biyu sai ya dakata ya nemi izininsa. https://www.tiktok.com/@ibrahimwisdomtv/video/7584542635965123861?_t=ZS-92I3mW6yftB&_r=1
Kalli Bidiyon: Kalaman Dr. Hussain na cewa yana son shiga Aljannah ba tare da ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba Jahilci ne da Hauka>>Inji Baffa Hotoro

Kalli Bidiyon: Kalaman Dr. Hussain na cewa yana son shiga Aljannah ba tare da ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba Jahilci ne da Hauka>>Inji Baffa Hotoro

Duk Labarai
Baffa Hotoro yawa Dr. Hussain Kano wankin babban bargo kan kalaman da yayi na cewa yana son shiga Aljannah ba tare da ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba. Baffa Hotoro yace wannan magana akwai wauta, Hauka, da Jahilci a cikinta. Ya bayyana hakane a wani Bidiyon martani da yawa Dr. Hussain Kano. Yace ko Annabi Ibrahim AS sai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ceceshi, duk da kasancewar Annabi Ibrahim AS badadin Allah ne Yace dan haka kuskurene tunanin wai me laifi ne kadai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) zai ceta a ranar tashin qiyama ko kuma ace wanda suka cancanci shiga wutane kadai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) zai ceta a ranar tashin qiyama. Yace dan haka suna baiwa Dr. Hussain Kano shawarar ya daina wa'azi, ya koma yayi karatu tukuna. https://www...
Da Duminsa: Najeriya ka iya fadawa Duhu kwanannan saboda karancin gas da kamfanonin samar da wutar lantarki ke samu

Da Duminsa: Najeriya ka iya fadawa Duhu kwanannan saboda karancin gas da kamfanonin samar da wutar lantarki ke samu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanonin dake samar da wutar lantarki na Najeriya na fama da karancin gas wanda ake amfani dashi wajan samar da wutar. Dalilin haka kuwa Najeriya na iya fadawa cikin duhu a yi bukukuwan kirsimeti babu wutar lantarki. Kamfanonin rarraba wutar na Enugu da Fatakwal sun sanar da abokan hukdarsu cewa sun rage yawar wutar da suka baiwa mutane saboda wannan matsala. Wata majiya ta tabbatarwa da Jaridar Punchng da wannan labarin. Hakan na faruwa ne saboda gazawar gwamnati waja biyan bashin da kamfanonin iskar gas din ke bi wanda rahoton yace idan ba'a biya ba ka iya sa kasar ta fada Duhu.
Kalli Bidiyon: Nuhu Ribadu da Kashim Shettima ne ke hana Tinubu samar da tsaro yanda ya kamata>>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Kalli Bidiyon: Nuhu Ribadu da Kashim Shettima ne ke hana Tinubu samar da tsaro yanda ya kamata>>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Duk Labarai
Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa, Babban me baiwa shugaban kasa, Shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu da kuma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ke hana shugaban kasar samar da tsaro yanda ya kamata. Yace Ribadu kowane bafulatani na Najeriya na da lambar wayarsa. Ya nemi shugaban kasar ya canjasu. https://twitter.com/Chude/status/2000995541656986105?t=CJ4K9Ld4wGdyDgivJ9REAg&s=19
‘Yan Kano Baku da Ankali, Wancan da kuka kama ya shiga masallaci a Hotoro, kamata yayi ku mikashi wajan hukuma>>Inji Wannan mutumin

‘Yan Kano Baku da Ankali, Wancan da kuka kama ya shiga masallaci a Hotoro, kamata yayi ku mikashi wajan hukuma>>Inji Wannan mutumin

Duk Labarai
Wani mutum da ya bayyana ya soki kanawa saboda Qàshè wanda ake zargi da cire Makogoron Ladani a Hotoro. Yace da aka kamashi ba kasheshi ya kamata a yi ba, kamata yayi a mikashi hannun hukuma ta yi bincike. Yace ta hanakane za'a gano duk masu alaka dashi amma yanzu gashi an kasheshi an koma ana ta zargin wai waye ya aikosshi. Yace shi yanzu duka shi da ladanin yakewa addu'a. https://www.tiktok.com/@nationalbestblogger/video/7584503733317422392?_t=ZS-92HUYUe04B7&_r=1
Da Duminsa: Ban yi hira da Freedom Radio ba, Na yi Mubaya’a ga Sarautar Sarkin Wakar da aka baiwa Rarara>>Inji Naziru Sarkin Waka

Da Duminsa: Ban yi hira da Freedom Radio ba, Na yi Mubaya’a ga Sarautar Sarkin Wakar da aka baiwa Rarara>>Inji Naziru Sarkin Waka

Duk Labarai
Tauraron mawakin Arewa, Naziru Sarkin Waka, yace bai yi Hira da Freedom Radio ba akan sarautar Sarkin Waka da aka baiwa Rarara ba. Yace idan da gaske ya fadi cewa sarautar irin ta Alutace ai ya karawa abin daraja ne tunda masu ilimi ne ke Aluta. Yace idan amincewa da sarautar da aka baiwa Rarara zata sa a shafa musu Lafiya, yayi mubaya'a ya amince. https://vt.tiktok.com/ZSPmqvYq2