Hotuna da Bidiyo: Kalli Kananan yara da aka barsu da yunwa bayan kamasu saboda sun yiwa gwamnatin Tinubu zanga-zanga, wasu daga cikinsu sun fadi ana tsaka da musu shari’a saboda yunwa, An bayar da belinsu akan Naira Miliyan 10 kowanne yaro daya
Rahotanni daga Babban birnin tarayya Abuja na cewa kananan yara guda 32 ne aka gabatar a gaban babbar kotun tarayyar dake Abuja bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
An kamasu ne saboda sun yi zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a watan Augusta da ya gabata inda tun wancan lokaci suke a tsare.
Jimullar mutane 76 ne ake tsare dasu bisa wannan zargi inda guda 32 kananan yarane.
Saidai a yayin da aka gabatar dasu a kotun an ga mafi yawancinsu suna cikin halin yunwa da rashin lafiya da tashin hankali.
Guda 5 daga cikin yaran sun yanke jiki suka fadi kasa ana tsaka da musu shari'a inda anan lauya ya nemi gwamnati da ta janye zargin da take musu na dan lokaci dan a kaisu Asibiti.
Alkalin Kotun ya amince da wannan bukata inda gwamn...








