An bayyana sunayen sojojin da Kungiyar IPOB ta kashe
Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana sunayen sojoji 5 da ake zargin 'yan Kungiyar IPOB sun kashe.
An kashe sojojinne a ranar Laraba a Obikabia dake jihar Abia.
sunayen sojojin sune:
• Sergeant Charles Ugochukwu (94NA/38/1467)• Sergeant Bala Abraham (03NA/53/1028)• Corporal Gideon Egwe(10NA/65/7085)• Corporal Ikpeama Ikechukwu (13NA/70/5483)• Corporal Augustine Emmanuel (13NA/70/6663)
Hukumar sojojin Najeriya dai ta sha Alwashin daukar mataki me tsauri dan rama kisan sojojin nata.








