Da Duminsa: Sati daya bayan rahotannin yunkurin jhuyin mulki Shugaba Tinubu ya kori manyan sojoji, Ya sauke Janar Christopher Musa daga shugaban sojoji, ya baiwa Gen. Olufemi Oluyede shugaban sojojin Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya tuɓe hafsan hafsoshin Najeriya, Janaral Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron ƙasar, a wani sauyi a tsarin jagorancin sojjin ƙasar domin inganta da ƙarfafa sha'anin tsaro a Najeriya.
A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar mai sa hannun ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaban a harkar watsa labarai, Sunday Dare, Tinubu ya yi musu fatan alkairi tare da bayyana sunayen sabbin hafsoshin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke ɗin.
Jadawalin sabbin hafsoshin:
Janar Olufemi Oluyede - Hafsan hafsoshi
Manjo Janar W Sha'aibu - Hafsan sojojin ƙasa
Air Vice Marshall S.K Aneke - Hafsan sojin sama
Rear Admiral I. Abbas - Hafsan sojin ruwa
Manjo Janar E.A.P Undiendeye - Shugaba sashen tattara bayan sirri na soji.
Waɗanda suka tsira:
Mal...








