Yadda ake dafa taliya da makaroni
Ana dafa Taliya da makaroni a cisu da miya, ko a yi Jollof dinsu ko a ci da mai da ya ji da dai sauransu, ya danganta da bukatar da ake da ita.
Yanda ake dafa Taliya da makaroni fari shine:
A samu tukunya me kyau a zuba ruwa kofi 4 ko 5 a barshi ya tafasa.
Bayan ya tafasa sai a zuba Taliya da makaronin a lokaci guda.
A barsu su dahu zuwa minti 15 ko 20.
Sai a sauke a tace ko kuma idan ruwan ya tsotse sai a sauke kawai a ci da abinda ake so.
Idan kuma Jollof za'a yi.
Sai a tanadi kayan Miya na leda ko danye a markadashi.
A tanadi Magi.
A tanadi man ja ko man gyada ya danganta wanda ake so.
A tanadi Kifi ko nama, ko kashin miya, ya danganta wanda aka fi so.
A tanadi Albasa.
A dora Tukunya a wuta a zuba man ja ko man kyada. A zuba kifi ko naman da aka tana...



